Ƙungiyar MECAHDA Ta Nemi A Kammala Gyaran Asibitin Misau

0
9988

Umar Saye, Daga Bauci

ƘUNGIYAR bunƙasa ci gaban masarautar Misau wato MECAHDA ta roƙi gwamnatin Jahar Bauci ta hanzarta kammala aikin kwaskwarimar babban asibitin Misau don ɗaukaka matsayin asibitin da inganta lafiyar jama’ar yankin kamar yadda gwamnatin ta alƙawarta.

Shugaban ƙungiyar, Malam Ahmad Mohammed, ne ya yi kiran a lokacin da suka kai ziyara asibitin garin don bayar da agajin kayan jinya ga marasa lafiya da kuma kayan mata masu juna biyu. Don haka ya bayyana rashin jin daɗi game da tsawon lokacin da aikin kwaskwarimar ya ɗauka har zuwa matsayin an ƙwace aikin a hannun ɗan kwangilar.

Ahmad Mohammed Misau ya roƙi gwamnatin da ta sanya aikin a hannun ƙwararren ɗan kwangila domin a samu kammala aikin a ingantaccen matsayi. Don haka ƙungiyar ta ziyarci Mai Martaba Sarkin Misau, Alhaji Muhammad Manga na uku inda cikin jawabinsa ya yaba musu game da ƙwazon neman ciyar da yankin gaba, don haka shi ma ya bayar da nasa taimakon don isar da shi ga asibitin ta hannunsu, kuma ya roƙi jama’a su yi koyi da irin wannan aiki da suke gudanarwa.Kasuwanci

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here