JABIRU A HASSAN, Daga Kano
AN kafa ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na makarantar Arabiyya ta ‘yan mata ta Ɗambatta sakamakon ƙoƙarin sabuwar shugabar makarantar, Hajiya Lauratu Ado Ɗiso na ganin makarantar ta sami ƙungiyar tsofaffin ɗalibai kamar yadda kowace makaranta take da ita.
Ƙungiyar wadda aka sanya wa suna ƊANGOSA, wato ‘Ɗambatta Girls Old Students Association’ ta sami karɓuwa ƙwarai da gaske daga tsofaffin ɗalibai na wannan makaranta da suka barta shekara da shekaru, tare da yi wa wannan sabuwar ƙungiya fatar kasancewa abar misali cikin sauran ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai irinta.
Bayan an kammala taron farko na ƙungiyar, shugabar kwamitin riƙo wadda aka naɗa Hajiya Ruƙayya Muhammad Yaƙub ta bayyana wa wakilinmu cewa, sun yi matuƙar farin ciki da zuwan Hajiya Lauratu Ado Ɗiso wannan makaranta domin ita ce ta sanya su a hanyar kafa ƙungiyar ƊANGOSA domin su taimaka wa ƙoƙarin gwamnatin Jahar Kano na bunƙasa ilimi.
Sannan ta sanar da cewa, suna da labarin irin ƙoƙarin da shugabar makarantar, Hajiya Lauratu Ado Ɗiso take yi a duk makarantar da ta riƙe, wanda ga shi yanzu Allah ya kaita makarantar da suka bari shekaru masu yawa za ta taimaki ci gaban ilimi kamar yadda ta saba.
Hajiya Ruƙayya Yaƙub ta ƙara da cewa, da yardar Allah kuma da taimakon Hajiya Lauratu Ado Ɗiso, ƙungiyarsu za ta kasance mai taimaka wa makarantar sakandaren ‘yan mata ta Ɗambatta bakin gwargwadon ikonsu ta yadda za a sami yanayi mai kyau na koyo da koyarwa don inganta ilimin mata a Jahar Kano.
Haka kuma ta yi alƙawarin cewa, za ta ci gaba da haɗa kan ɗaukacin tsofaffin ɗalibai waɗanda suke raye ko da kuwa suna nesa ne domin su shiga cikin ƙungiyar ta yadda za su haɗa hannaye wajen taimaka wa ƙoƙarin gwamnati na bunƙasa ilimin mata da kyautata tarbiyyarsu.
Daga ƙarshe, Hajiya Ruƙayya Muhammad Yaƙub ta yi amfani da wannan dama wajen ƙara jinjina wa Hajiya Lauratu Ado Ɗiso wadda ita ce ta assasa ƙungiyar har ga shi ta fara tafiya bisa manufar taimaka wa makarantar da suka bari tun lokaci mai tsawo, sannan ta yi kira ga dukkan tsofaffin ɗaliban makarantar Arabiyya ta ’yan mata ta Ɗambatta da su shiga cikin ƙungiyar domin su bada tasu gudunmawar.
Ita dai sabuwar shugabar makarantar wato Hajiya Lauratu Ado Ɗiso ta yi fice ƙwarai wajen yin amfani da basirar da Allah ya bata domin taimaka wa ci gaban ilimi a duk inda ta sami kanta. Bincike ya nuna cewa, ita ce ta assasa saukar karatun Alƙur’ani mai tsarki lokacin da take makarantar sakandaren ‘yan mata ta Gezawa wanda ga shi abin ya bunƙasa a dukkan makarantun ‘yan mata da ke Jahar Kano.
Sannan ta yi aiki sosai wajen samar da ƙarin ɗakunan kwanan ɗalibai a makarantar ‘yan mata ta ‘yar Gaya da wasu muhimman abubuwa kuma a yau wannan makaranta tana daga cikin makarantu masu kyau a jahar, kana zuwanta kwalejin ‘yan mata ta Dala wato GGC Dala, Hajiya Lauratu Ado Ɗiso ta ruɓanya ƙoƙarinta wajen samar da ayyuka masu tarin yawa ta hanyar ƙungiyar tsofaffin ɗalibai da kuma ta PTA.
Don haka, komawarta makarantar sakandaren Arabiyya ta Ɗambatta, za ta yi aiki sosai wajen ganin wannan makaranta tana samun ci gaba domin ƙara taimaka wa gwamnati na bunƙasa ilimin mata da tarbiyyarsu.
Sabuwar ƙungiyar ta ƊANGOSA tana da shugabanni kamar haka Hajiya Ruƙayya Muhammad Yaƙub a matsayin shugaba sai Hajiya Hansa’u Usaini mataimakiyar shugaba sai Hajiya Bilkisu Garba sakatariya sai Hajiya Safiyya Hashim jami’ar hulɗa da jama’a, sai Hajiya Binta Isyaku mamba da kuma Hajiya Rabi’atu Aliyu ita ma mamba, sannan za su sake taronsu na biyu ranar 24 ga Nuwamba, 2012.