BURINMU mu ga an ci gaba da karantar da addinin Musulunci a makarantar Islamiyya ta Nurul-huda ya sanya aka kafa kwamitin makarantar Islamiyya, Alhaji Aliyu Shitu shugaban kwamitin ne ya tabbatar wa Gaskiya Ta Fi Kwabo haka a tattaunarwa da suka yi da wakilinmu a Kalaba, AHMAD ABDUL, ga yadda hirar ta kasance:
GTK: Sai ka gabatar wa makarantan jaridar nan kanka gare su?
Alhaji Aliyu Shitu: Sunana Aliyu Shitu, shugaban kwamitin makarantar Islamiyya ta Nurul-Huda da ke layin Bagobiri Kalaba, Jahar Kuros Riba.
GTK: Bisa labarin da ya riski wannan jarida, an ce kun kafa kwamitin da zai farfaɗo tare da yin gyara a harkokin yaɗa addinin Musulunci ta ci gaba da karantar da yara addinin Musulunci a nan unguwar Hausawa, me ya jawo hankalinku har kuka kafa wannan kwamiti?
Alhaji Aliyu Shitu: Eh! Alal haƙiƙa na daɗe ina ta yin tunanin yadda za a magance matsalar taɓarɓarewar karatun yaranmu na Islamiyya a wannan makaranta tare da tunanin wace hanya za a bi a gyara lamarin, haka dai ina kallon tsarin makarantar na koma baya abin yana mini ciwo shi ne sai na nemi shugabanninmu su fito mana da wani tsari da za a gyara matsalar tare da yin gyaran masallaci ya dawo irin na zamani, shi ne aka kafa kwamitin masallaci, ni kuma na fi matsawa kan na makarantar Islamiyya. Da na matsa ƙaimi kan son a yi gyara sai shugabannin masallaci suka umarce ni da in nemi wasu mutane da za a kafa kwamiti mai zaman kansa wanda zai riƙa kula da makarantar Islamiyya.
Daga nan ne Allah ya ba ni sa’a na fita ina nema har na dace na sami waɗanda ra’ayinsu ya zo ɗaya da nawa na son kyautata wa addinin Allah kuma da ma malamin makarantar Malam Hamisu Ɗan Mudi Mai Adashi shi ma ya damu da a gyara makarantar sai muka haɗa da shi da muka fitar da kwamitin kuma aka fitar wa kowa matsayi su kuma suka taru suka ɗora mini nauyin shugabancin kwamitin, ka ji yadda abin ya samo asali har zuwa halin yanzu.
GTK: To, daga nan fa sai aka yi yaya?
Alhaji Aliyu Shitu: Daga nan mun sami wasu bayin Allah irin su Yusuf Malam Auwalu duka dai aka raba masu muƙamai tun da su ma duk masu son ganin addinin Musulunci ya ƙara ci gaba da yaɗuwa, ne ya sa aka ba su muƙaman da sauran wasu jama’a da za su yi mini ahuwa, lokaci ba zai bari in kawo jerin sunayensu ba. Haƙiƙa lokacin da muka fara aniyar gyara mun fara samun ƙorafi daga wasu jama’a ka san da ma gyara ba ya yiwuwa sai an yi wa wasu ɓarna tun da mun zo da kyakkyawar niyya ce shi ne yanzu kuma cikin yardar Allah muke samun nasara, sannan muka ci gaba da nuna masu cewa, ba dole sai mun haɗa ɗaliban makarantar wuri ɗaya nan take ba, muka ce tsarin da muke so shi ne ko da ɗalibai uku muka samu za mu ci gaba da su, mu burinmu mu ga komai ya tafi daidai da zamani ta fuskar karantarwa.
To, cikin ikon Allah mutane da suka fahimci manufarmu suka amince, yanzu zancen nan da ake mana ta samun gudunmawa a wurin mutane, zancen nan ma da ake, mun samar wa makarantar fom na zamani wanda ake sayarwa an ɓullo da wani tsari na yadda kowane karatu za a riƙa fitar masa da zangon ɗalibai suna yin jarrabawa hatta karatun zamani ma duk mun tsara yadda za a riƙa karantarwa don cimma buri, mun ɗauko sabon malami daga Jahar Kano zai zo ya riƙa karantar da yara su haɗu tare da wanda yake yi yanzu suna karantarwa.
GTK: Bayan haka ko akwai wani tsari da kuka ƙara ɓullo da shi don gyara?
Alhaji Aliyu Shitu: An ɓullo da tsarin yadda ɗalibai za su yi zaman makarantar, sannan kuma mun fara yin gyara a kujerun makaranta da ainihin yin wasu sababbi ma da ɗalibai za su riƙa zama a kai ko da an sami ƙarin wasu sababbin ɗalibai ba za su fuskanci matsalar wurin zama ba. Yanzu muna kan hanyar sake wa wasu azuzuwan fasali har ofishin malamai da na shugaban makaranta duk za mu fitar da aji daban-daban, kowane aji na ɗaya da na biyu da makamantan inda azuzuwan suka tsaya suka dace duk da yardar Allah niyyarmu ke nan duk bayan mun kai kukanmu wurin kwamitin masallaci suka ba mu inda za mu yi aikinmu, ba wata matsala kuma tsakanin kwamitina da na masallaci akwai jituwa mai kyau da fahimtar juna Alhamdulillahi. Yanzu haka an sami ɗalibai yawan su ya kai 50, akwai ma manya sun buɗe nasu karatun suna yi duk a makarantar saboda ci gaba da aka samu.
GTK: Kun shawo kan matsalar iyayen yara da ba su son a ladabtar da ‘ya’yansu da kuma masu ƙin turo su makaranta?
Alhaji Aliyu Shitu: Shi ya sanya tun da farko da muka fara taro muka bi wata hanya a siyasance muka fara da neman iyayen yara su zo makarantar muna kiransu taro. Matsalar da ma muka fara fuskanta da su ita ce, su ji suke kamar kuɗi za a karɓa hannunsu amma sai da suka ji ga manufarmu, da ya sanya suka ji daɗin yunƙurin muka nuna masu shawarwarinsu kaɗai muke buƙata duk lokacin da buƙatar hakan ta taso daga gare su, ga abin da kaɗai muke so komai da ƙarfin Allah da yardarSa da ƙarfin aljihunmu za mu yi.
Mun faɗa wa iyayen yara buƙatarmu duk lokacin karatu su turo mana yaransu, mun kuma nuna masu cewa, dole fa su yi haƙuri idan yaro ya yi ba daidai ba a ladabtar da shi kada su yi fushi kan haka, don sai ka ga uban yaro yana sa-in-sa da malami kan an hori ɗansa, gudun haka muka kafa doka tsakanin iyayen yara da malami, shi ma kuma da ɗalibai maganin ƙaramar magana.
Idan ma har aka sami wani uba ya zo ya ɗauki doka a hannu kwamiti ya ba malami dama ya tura yaro gida har sai uban yaro ya zo ya nemi ahuwa ko da an tura yaro gida tsawon sati ɗaya sai yaron ya cika sharaɗin domin abin ya yi masa ciwo ya gyara halayensa ko da uban yaron ma ya zo ya roƙi ahuwar sai a nuna masa gyara ake son yi bada wata manufa ba.
GTK: Idan na fahimce ka kun kafa kwamitin ladabtarwa tsakanin iyaye da malaman makaranta da ɗalibai ke nan?
Alhaji Aliyu Shitu:Eh! Ƙwarai, mun sanya dokoki, shi ma malami idan ya ɗauki mataki kan yaro ba bisa ƙa’ida ba shi ma ga irin matakin da za a ɗauka kansa kowa an ba shi iya hurumin da zai tsaya, ba mu yarda da wuce ƙa’ida ba.
GTK: Ka fara ganin alamun kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulunta kuwa?
Alhaji Aliyu Shitu: Eh! Alal haƙiƙa akwai alamu ta fara biyan kuɗin sabulunta ma ba ɗaya ko biyu ba. Kamar yadda na faɗa da farko da aljihunmu za mu yi komai, da shi muke yi daga aikace-aikacen da muka sanya ne har Allah ya sa mun kammala kashi 55 cikin 100 na aikin da muka sanya gaba.
GTK: Shawararka ga iyayen yara da kuma ‘yan kwamitin makaranta?
Alhaji Aliyu Shitu: Shawarata ga ɓangaren iyayen yara su yi ƙoƙari su ba kwamiti da malamai haɗin kai a duk lokacin da aka buƙacesu, su zo taro kada su yi zato ko don kuɗi ne ake kiransu su zo taro. Ga ‘yan kwamiti kuwa, shawara ita ce, duk wanda ya sanya kansa na taimakawa ya cire tunanin abin da zai bayar gudunmawa a ransa duk lokacin da muka zo mu ƙuduri niyyar aikin alherin da muka ɗauka tun farko ci gaba ne za mu yi.