Fadaƙarwa Ce Ta Jawo Hankalina Na Koma Harkar Waƙa — Alan Waƙa (3)

0
10631

GTK: Shin waƙoƙin da kake rerawa, kai kake tsara su da kanka ko kana da wani wanda yake rubuta maka ko ya tsara maka?

ALAN WAƘA: Ni nake zama in tsara su ko in rubuta su, ni nake zama in yi tunani ko nake zama in yi bincike a kan duk wani abin da nake so in yi waƙa, sai dai akan sami wasu waƙoƙin wanda wani kan samar da tunani, ni kuma in zauna in tsara waƙar, in rubuta, sai rerawa, misali waƙar bikin cika shekara 50 muryar BBC ce ke buƙatar waƙar cika shekara 50 a kan ci gaba aka yi ko ci baya, su ne suka samar da wannan tunani suka faɗa mini, shi ne na zauna na tsara waƙar na rubuta.

Haka kuma basarake na iya cewa ka yi waƙa a kan Maiduguri ko Zariya, inda zan je in yi bincike na a kan garin, in zauna in rubuta waƙar in tsara waƙar, in kuma rera da kaina, amma su suka samar da tunanin, in ko ba haka nan ba ne, to, ni nake zama in rubuta ko in tsara, ko in samar da tunanin waƙa da kaina, amma ba wani ke rubuta mini ba.

GTK: A matsayin ka na mawaƙi, shin kana zuwa gidajen biki yin waƙa ne ko kakan tsara waƙa ne kawai na sayarwa na ra’ayin kan ka kawai?

ALAN WAƘA: Eh, ina yin waƙa don mutane, don da ma waƙa ana yinta ne don ra’ayin jama’a, idan ma siyasa ka yi wa ko yabon Annabi (SAW), haka kuma in mutane suka ce za su yi aure tun da auren Sunnar Annabi (SAW) ne, kana so a taya ka murna, kuma halas ne ma a yi biki a taya murna, saboda haka idan ka yi don faɗakarwa ga ango da amarya, don nuna haƙƙoƙin miji ga mata, kana ga haƙƙoƙin mata ga miji don faɗakarwa ko yin tuni.

Haka kuma ina yin waƙoƙi na sarauta, na siyasa, na biki da na faɗakarwa, amma waƙoƙin da nake fitarwa na albam ɗina, su waɗannan waƙoƙi ne da nake yi don mutane ko don kaina, amma ni bana zuwa taron aure na biki sai dai mutum na iya sanya ni in waƙe shi da matar shi don su je su sanya a wajen biki, amma ba ni sai na zo da kaina ba, domin wani shi ma wani aiki ne babba, kuma jin kunyar wasu mutane na iya sanya ka ɗaukar alƙawarin da ba za ka iya cikawa ba, amma dole ka ɗauka a wajen.

GTK: Kasancewar ka a cikin harkar sana’ar waƙa, waɗanne irin nasarori ka samu a cikin sana’ar waƙa?

ALAN WAƘA: Kamar yadda na faɗa a baya a cikin nasarorin babu nasarar da na samu irin saurare na da ake yi, yau idan na yi waƙa Allah kaɗai Ya san iya adadin manya – manyan mutanen da suke saurare na, saboda haka wannan shi ne babban nasarar da na samu, kuma wannan nasarar ta janyo duk wani abin da na ɗauka nasara ne, misali samun abin da za ka ci ko ka ɗauki ɗawainiyar kan ka, ka ga wannan nasara ne, to ka ga ina samun yadda zan yi har in gabatar da ita ga al’umma, bayan ci da sha da nake yi a ciki da ɗaukar ɗawainiyar kai na, amma babban nasarar shi ne saurare na da ake yi.

GTK: Wasu jama’a a gari na zargin cewa ka daina waƙa, mene ne gaskiyar lamarin?

ALAN WAƘA: Wannan shaci-faɗi ne kawai, wasu sun yi ƙarya suka zauna suka shirya suka ce wai na yi mafarki da Annabi (SAW) ya gaisa da kowa amma ni ya tsallake ni , da na tambayi dalili ya ce saboda ina yin waƙa , wannan gaskiya mutane ne suka zauna suka shirya tatsuniya don ni ma haka nake ji kamar yadda sauran jama’a ke ji.

Kuma ina sa ran Insha Allahu idan Allah Ya kai mu shekara mai zuwa a watan farko kamar yadda na ce zan riƙa yi a kowace shekara, zan fitar da albam ɗina  mai suna ‘kawalwainiya’, da albam ɗin ‘duniya makaranta’ da albam ɗin ‘Dillaliya’ da izinin Allah.

GTK: Kasancewarka mawaƙin Hausa kuma jama’a da dama na ganin kamar kana tare da ‘yan fim ɗin Hausa, shin ko kana da sha’awar shiga fina-finan Hausa ko fara yin fim ɗin Hausa?

ALAN WAƘA: A’a bani da sha’awar shiga fina-finan Hausa, sai dai ina da sha’awar kallon fina-finan Hausa, kuma waƙa don ta isar min shi ya sa nake waƙa, amma ina da sha’awar a ce an wayi gari a ce ana yin waƙoƙi na faɗakarwa a cikin fina-finan Hausa ko da na bayan fage ne, don ko ni ina iya bayar da gudunmawa, ba lallai sai an yi waƙa an yi min ba amma ya zamana tana ɗauke da babban saƙo a ciki, don babu ƙyama a tsakanina da ‘yan fim ɗin Hausa wanda hakan ne ya sa za ka ga a cikin wasu fina-finan ake jin wasu waƙoƙina amma na fi son yin waƙoƙina kawai ba in shiga yin fim ba.

GTK: Waɗanne irin matsaloli kake fuskanta a kan wannan sana’ar ta waƙa?

ALAN WAƘA: Eh, to akwai matsaloli da ba za a rasa ba, saboda duk mutumin da ya yi shuhura, dole ne zai riƙa fuskantar abubuwa na ƙalubale na maganganu munana ko kyawawa, wasu kuma su dinga yin munaƙisa ba a rasa waɗannan, amma duka muna ɗaukar su a matsayin nasara ne tun da mun san da ma hakan sai ya faru, don su ne kamar matakai na nasara.

GTK: Wace shawara za ka ba sauran mawaƙa ‘yan uwanka a kan sana’ar waƙa, musamman masu yin waƙa wanda ya bambanta da irin taka?

ALAN WAƘA: Shawarar da zan ba dukkan mawaƙa, shi ne ya zamana yana da hujja, ko yana da ilimi a kai, don ba shakka wannan matakai guda biyu su ne za su kai mutum ga tudun-mun-tsira a cikin harkar waƙa musamman a waƙar Hausa, ka san iyakar ka kuma ka san iyakar abin da za ka iya faɗa, sannan ka san haƙƙin kanka kuma ka san ‘yancin faɗi da bakin ka, sannan komai za ka yi ka yi shi da ilimi, don duk abin da ka yi in har yana da kyau ka sani, ko ma ba ya da kyau duk ka sani tun da da ilimi ka yi shi, kuma ba lallai ba ne duk abin da ka yi ka ce sai ka burge mutane ko ka ce ka na burge mutane.

GTK: Wasu jama’a na zargin cewa a sakamakon daina waƙa da ka yi ya sanya ka bar ofishinku da aka san ka, shin ko mene ne gaskiyar maganar?

ALAN WAƘA: Ka san cewa dukkan ɗan Adam yana son ci gaba a rayuwa, ofishin da nake a da a baya ‘Hikima Multimedia’ mu muka assasa shi, amma na ubangidanmu ne, to mun zauna tsawon shekaru 5 a wannan kamfani, daga bisani Allah Ya hore mini na buɗe nawa na kaina wanda a yanzu yana nan a hanyar ‘Gudu Abdullahi farm centre’, yana kallon makarantar kuɗi ta ‘Assalam gidan Garba Goro’ inda na  buɗe ‘Taskar Ala Global Limited’.

Sannan kuma ina da wani ofishin a garin Kaduna a nan sabon ‘Magadishu layout city’ a hawa na 3 a cikin wani fulaza kusa da ‘yan doya, don na ga wannan a matsayin nasara kuma duk wanda yake ƙaunata hakan shi ma zai gan shi a matsayin nasara.

Don a da ina ƙarƙashin wani ina ci daga gare shi, amma ga shi Allah Ya sa na buɗe nawa a yanzu, duk da yake ina gode wa Allah na zaman rayuwa da na yi a can wajen, da duk abin da aka samu na ci gaba mai amfani har ya kai ga ga shi na buɗe nawa, to wannan shi ne ainihin lamarin.

GTK: A ƙarshe me za ka ce wa mutane masoyanka, masu sauraronka a kodayaushe kuma sha’awar irin waƙoƙin da kake yi na ilimantarwa?

ALAN WAƘA: A kullum ina son in jan hankalin mutane da ke sauraronmu cewa su dinga yi mana adalci, kuma su dinga ji da saurare na nazari, kuma su dinga yi mana zato na alkairi kuma muna yi wa Allah godiya don martabarmu, shi ne masu sauraron mu, darajarmu masu sayen ayyukanmu, saboda haka ba ma yi sai don su, amma ba masu nazarin mu ba, don masu nazarinmu suna yi ne don warware tufkar da muka yi.

Amma mu ba su muke kallo ba, mu muna kallon masu sauraron mu ne, saboda haka ba mu da daraja ko guda ɗaya sai da masu saurarenmu, don da su muke alfahari, da su muke ji, saboda haka idan muka yi wani ɓatanci su za mu ɓata, idan muka yi wani abu na alkairi su muka fi ba gudunmawa fiye da kowa, saboda haka ina yi masu fatar alheri, kuma ina fatar su ma za su riƙa yi mana zato na alkairi kuma su riƙa bibiyar mu da ma’aunin hankali da nazari.

GTK: To, Malam Aminu Ala mun gode, wassalam.

ALAN WAƘA: Wassalamu Alaikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.

Mun Kammala

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here