Daga Nura Ibrahim Khalil
0803371 8219 nuriddeen2003@yahoo.com
Wannan alaƙa wadda ke nufin kariyar nau’i, kuma take tunkuɗawa zuwa jima’i don nufin jin daɗi; ta dukkan ɓangarorinta biyu na halayya da ‘yan Adamtaka tana tsayawa ne a bisa asasin ƙauna, jin ƙai da samar da natsuwa.
Da wannan Alƙur\’ani ya ɗauki mace a matsayin tushen natsuwa ta hanyar tabbacin hankali da na zamantakewa ga namiji da rayuwar zamantakewa baki ɗayanta; wannan kuwa saboda ƙosar da rai daga son wani jinsi da jaraba ta jiki daga gare shi, suna haifar da kawar da damuwar rai da na zuciya, da cika irin faragar da rai ɗin ke da shi, da sarrafa ƙarfin buƙatar jima’i da halayya don tabbatar da daidaici ga jinsosin biyu da ke tsaye a kan asasin cika ta hanyar gamammiyar dokar auratayya ta halitta.
Daga nan nauyin da ya rataya a wuyan mace wajen gina rayuwar al\’umma miƙaƙƙiya kuma mai lafiya ta jiki da zamantakewa ke iyakantuwa; saboda ita ce maɓuɓɓugar natsuwa, ƙauna, tausayi da jin ƙai cikin rayuwar zamantakewa.
2-Sanayya: Abu na biyu da ke sa mutum haɗa rayuwar zamantakewa, shi ne ƙa’idar nan ta sanayya tsakanin mutane, abin da ke tsaye a bisa asasin nan na jin son zaman tare wanda masana falsafa ke nunawa da cewa: ‘Mutum mai zaman tare ne bisa ɗabi’a”. Jarabce-jarabce na halayya da zamantakewa sun tabbatar da cewa mutum ba ya jin tabbas da kwanciyar hankali, kuma mutuntakarsa ba ta cika sai da zamantakewa da rayuwa tare da wasu. Domin shi yana da matsananciyar buƙata ta rai kuma mai zurfi zuwa ga wasu, saboda haka ne ma Allah Ya faɗi cewa: “.-don ku san juna”; kalmar sanin juna na nuni ne ga ɓoyayyen abin da ke tura mutum zuwa zamantakewa da haɗa al\’ummar ɗan Adam.
3-Musayar amfanoni: Sababi na uku daga sabubban gina al\’umma shi ne musayar amfanoni na abin duniya daban-daban. Haƙiƙa Allah Ya so ɗaiɗaikun mutane su sami cika da irin ƙarfi da ƙwarewarsu ta tunani, jiki da hankali, kuma wannan cika na tabbata ne ta hanyar musayar amfanoni tsakanin ɗaiɗaiku. Kowane mutum -shi kaɗai- yana da buƙatu da wasu abubuwa da yake nema masu yawa, kuma ba ya iya samar wa kansa da su duka; don haka yana buƙatar wasu, su ma suna da buƙata da shi, wannan saɓani cikin ƙwarewa wanda daga gare shi ne ake samun saɓani cikin nau’o’in abubuwan da ake samarwa da hidimomin da mutum ke iya yi ga wasu, da musayar waɗannan abubuwa da amfanoni da hidimomi don biyan buƙatu, shi ne wanda Alƙur\’ani mai girma ya yi maganarsa da cewa:
“…kuma muka ɗaukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riƙi wani mai yi mishi hidima…” Surar Zukhrufi, 43:32.
A bisa wannan asasi ne ayyukan zamantakewa ke faruwa, kuma (haka) ya fassara tubalin faruwar ayyuka a cikin al\’umma don rayuwa ta sami cika kamar yadda gaɓuɓɓan jiki ke cika wajen cika ayyukansu.
Haka nan Alƙur’ani ke yi mana bayanin abubuwan da ke haifar da al\’umma, mutuntaka da abin duniya. Kuma cikin dukkan waɗannan tubaloli da asasai, gudunmawar mace na bayyana ƙarara tun daga tushe, Sawa’un ta ɓangaren abin duniya ne ko ta halayya ko aiki cikin rayuwar zamantakewa, ita babbar sashi ce ta al\’umma. Haƙiƙa alƙaluman mutanen duniya baki ɗaya na nuna cewa adadin mata a duniyar ɗan Adam ya wuce adadin maza.
Ta wannan hange na cikar aiki da Alƙur\’ani ya bayyana a baya, za a iya ginin gudunmawar mace kamar yadda ake ginin gudunmawar namiji daidai-wa-daida cikin tsaikon manufofi da halayyar Musulunci, mace ba asasi ta biyu ba ce, ba kuma ƙarin halitta ba ce, duk kuwa da cewa jarabce-jarabcen ɗan Adam sun tabbatar da cewa gudunmawar namiji wajen gina ilimi da tattalin arziƙi ya fi gudunmawar mace mai zurfi da yawa kuwa, amma nata gudunmawar wajen haɗa shika-shikan ruhi don gina iyali ya fi gudunmawar namiji girma nesa ba kusa ba kuwa. Wannan shi ne abin da Alƙur\’ani ya nuna dacewarsa:
“..Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami natsuwa da ita”. Surar A’arafi, 7:189. Ke nan namiji shi ne yake natsuwa zuwa ga mata, ya sami tabbaci da rayuwa tare da ita, ita ce cibiyar haɗuwa kuma tsaikon aminci, ƙauna da soyayya. Alƙur\’ani na magana a kan ‘natsuwa’ a wurare da yawa, ta nan za mu iya fahimtar ma’ana irin wadda mace kan samar ga mijinta, za mu fahimce shi ta hanyar faɗarSa Maɗaukaki:
“Akwai daga ayoyinSa Ya halitta muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya ƙauna da tausayi a tsakaninku..” Surar Rum 33:21. Da faɗarSa: “..Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami natsuwa da ita”. Surar A’arafi, 7:189.
Za mu fahimci kimar kalmar ‘Natsuwa’ a zaman tare ne yayin da muka san cewa Alƙur\’ani ya siffanta alaƙa tsakanin miji da mata da cewa alaƙa ce ta (Natsuwa, ƙauna da soyayya).Ke nan bari mu karanto kalmar ‘natsuwa’ a wurare da dama cikin Alƙur\’ani, don mu san ma’anarta a zamantakewa da iyali. Allah Maɗaukaki ya faɗi cewa:”(Allah) Ya sanya muku dare a natse” wato mutane na natsuwa a cikin shi natsuwa na hutawa. Haka nan Allah Ya faɗi cewa: “Ka yi salla gare su lallai sallarka natsuwa ce garesu”, wato suna natsuwa da addu’arka, kuma hankalinsu na kwanciya da ita. A wani wuri kuma Ya ce: “Shi ne wanda ya saukar da natsuwa a zukatan Muminai”
Ya samar da tabbas da kwanciyar hankali.Malaman harshen larabci sun yi wadataccen sharhi a kan kalmar, tare da bayar da misalai, inda duk suka fassara ‘Natsuwa’ da: Kwanciyar hankali, rashin jin kaɗaici da duk abin da ka sami tabbas tare da zama da shi kuma ka huta da rayuwa tare da shi.(2)
Da haka za mu iya fahimtar natsuwar da mace ke samarwa ga mijinta da iyalinta, wato shi ne: hutawa, aminci, ɗauke kaɗaici, tausayi, albarka da tabbaci, kamar yadda za mu iya fahimtar sirrin zaɓar wannan kalma mai ma’anoni da yawa, da Alƙur\’ani ya yi.
Haƙiƙa darussa na ilimi sun tabbatar da irin tasiri da yanayin rai da halin mutum ke da shi a kan ɗaukacin harkokin shi cikin rayuwa; saboda a tabbace yake a ilimance cewa ayyukan zamantakewa, alhakin aiki da neman abin duniya, na daga noma, sana’a, hada-hadar siyasa, zamantakewa da hidima ga al\’umma kamar ayyukan gudanarwa, aikin injiniya, karantarwa, aikin likita, kasuwanci, fannoni da sauran irinsu waɗanda kowane ɗaya daga namiji da mace ke yi; duk suna da tasiri kai tsaye daga yanayinsu na halayya. Namijin da ke raye a tsakiyar matsalolin iyali da damuwar zuci da ɓacin rai, samun shi ga abin duniya kaɗan ne, haka nan nishaɗinshi wajen aiki da tunanin ƙirƙirar wani abu cikin ayyukan shi su ma suna tasirantuwa, kuma matsalarsa na ƙaruwa wajen alaƙarsa tare da abokan aikinsa da waɗanda yake da alaƙa da su.
Mu Kwana Nan