ƊAN majalisar dokokin Jahar Filato, mai wakiltar mazaɓar Jos ta Arewa ya bayyana gazawar da gwamnan jahar, Jonah David Jang, na ta kawo ƙarshen yajin aikin da ma’aikata ke yi a jahar lallai alama ce ta gazawa sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci.
Honorabul Ibrahim Hassan ya bayyana hakan lokacin da yake bayar da gudunmawa a game da maganar da shugaban kwamitin ƙwadago na majalisar, Honorabul Exo Nandom Pyennap, wanda ya shaida wa majalisar cewa, ma’aikatan ƙananan hukumomi sun amince su karɓi ƙarin kashi biyar a madadin kashi 50 cikin ɗarin da a da can suka kafe sai an ba su na ƙarin albashin dubu goma sha takwas a matsayin ƙarancin albashi.
Amma ma’aikatan sun ƙi janye yajin aikin sakamakon kafewar da gwamnan ya yi na cewa, duk wanda bai yi aiki ba, ba za a biya shi albashi ba”.
Kamar yadda Honorabul Hassan ya bayyana cewa, lallai abin baƙin ciki ne ƙwarai irin yadda aka kasa biyan albashin da ya dace a biya ma’aikatan na dubu sha takwas kamar yadda doka ta tanadar lamarin da ya haifar wa ma’aikatan shiga cikin wani hali har waɗansu 13 suka mutu a mazaɓarsa ta Jos ta Arewa,.
“Lallai ni a ganina wannan gazawa ce wadda gwamnatin ta kasa tsayar da yajin aikin da ya daɗe har tsawon watanni 6”, inji shi.
“Ba daɗi kuma wani abin baƙin ciki ne ga gwamna da ya ce idan ba aiki ba albashi”.
Ɗan majalisar ya bayyana yanayin cewa, ya yi jagorancin rufe dukkan makarantun firamare da duk cibiyoyin kula da lafiyar jama’a saboda yajin aikin, abin da ya bayyana da cewa, duk ya faru ne saboda halin ko-in-kular da gwamnati ta nuna.
“A yau ko da ana biyan ma’aikaci Naira dubu sha takwas, ba zai iya biyan buƙatunsa ba, ko da kansiloli suna aika yaransu makarantun kuɗi ne, ba wai batun shugabanninmu ake yi ba don haka babu wanda ya damu da rufe makarantun firamare”, ya bayyana.
Da yake tofa albarkacin bakinsa game da lamarin Honorabul John Clark, inda ya ce za a warware matsalar.
‘Yan majalisar sun cimma yarjejeniyar kiran wani taron masu ruwa da tsaki da suka haɗa da ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi, ƙungiyoyin ƙwadago, ma’aikatar ƙananan hukumomi da kuma kwamitin da tun farko aka kafa domin ya shiga tsakani domin warware matsalar.