HUKUMAR tara haraji ta tarayyar Najeriya (FIRS) ta yi namijin ƙoƙarin tara harajji da ya kai zunzurutun kuɗi har Naira tiriliyon 3.81 da kimanin Naira biliyan 23.30 da suka miƙa su ga ma’aikatar babban birnin tarayya, Abuja (FCTA) na lokacin ƙarshen watan Satumbar shekarar 2012.
Waɗannan jimillar kuɗaɗe sun haɗa da kuɗaɗen shigar nan na ma’aikata da ake kira “Pay As You Earn (PAYE)’, wato biya kamar yadda ka ke karɓa, da kuma kuɗin shiga na kuɗin shiga na ƙashin kai (PIT) da ake karɓa daga masu gidajen babban birnin, wannan ya nuna ƙarin kuɗaɗen shigar da aka samu idan an kwatanta da Naira biliyan 21.94 da aka kai wa ma’aikatar a bara, wato shekarar 2011.
Darakta na ɓangaren sadarwa da tuntuɓa na hukumar tara harajin FIRS, Mista Emmanuel Obeta ne ya sanar da haka, inda ya ƙara da cewa, wannan yunƙuri na tara harajin haka, ya haɗa da karɓar haraji na gaba-ɗaya na zango na ɗaya da na biyu da kuma uku na shekarar ta 2012 wanda ya kai jimlar Naira tiriliyan 3.81.
Mista Obeta ya ce da wannan yawan kuɗaɗen na haraji FIRS ta zarce kuɗaɗen da aka yi kasafinsu a kasafin kuɗin ƙasar nan, wato Naira tiriliyan 3.6 a watanni tara a cikin shekarar, inda aka yanke cewa, ɓangaren ma’adinan mai za a sami haraji na Naira tiriliyan 2.399, sauran wurare kuma su harhaɗo Naira tiriliyan 1.406.
Daraktan ya ci gaba da cewa, yawan kuɗaɗen da hukumarsu ta tara ya nuna an sami ƙarin kuɗaɗen shiga na kimanin Naira biliyan 890 idan aka kwatanta da Naira biliyan 2.91 da aka samu a shekarar 2011. Ya ce a shekarar 2011 FIRS ta tara Naira biliyan 955.19 a zangon farko, Naira biliyan 985.30 a zango na biyu, sai kuma Naira biliyan 974.65 a zangon ƙarshe.
A cewar darakta Obeta, yawan kuɗaɗen da suka tara a shekarar 2012, sun karkasa su zuwa zango-zango har uku kamar yadda aka saba, a inda ya baje su a faifai tun daga abin da aka tara daga watan Janairu zuwa watan Satumba.