Ilmin Firamare A Jihar Zamfara: Ƙalubalen Da Ke Gaban Murtala Adamu Jangeɓe!!

0
11763

TUN lokacin da ya karɓi ragamar jagorancin Hukumar Kula da samar da ilimin firmare ta Jahar Zamfara wato, ‘Zamfara State Universal Basic Education (ZSUBE) ake ganin cewar ba shakka Alhaji Murtala Adamu Jangeɓe na da muhimmin ƙalubale a gabansa wajen tayar da komaɗar lalacewar darajar ilimin firamare da sake fito da ingantattun hanyoyin bunƙasa karatun yara ‘yan firamare a Jihar Zamfara.

A matsayinsa na tsohon ɗalibin ilimi kuma malamin makaranta, masani a kan lamuran yau da kullum waɗanda suka shafi al’umma, musamman ma tun a zamansa cikin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da kuma irin hoɓɓasan da ya yi wajen fito da tsare-tsare masu inganci ga ci gaban al’ummar jihar , Murtala Adamu Jangeɓe na da basirar maido da darajar ilimin firamare bisa inganttacciyar hanyar ci gaba da bunƙasa.

Ilimin firamare a ko’ina a duniya shi ne muhimmin ginshiƙin samar da da kyakkyawar makoma wadda ta dace ga ci gaban hazaƙa, tarbiyya da karatun yara har zuwa jami’a. Ainihin ilimin firamare shi ne tashar farko wajen samar da alƙiblar da ta dace ga cimma burin al’umma na karatun ‘ya’yansu.

Wannan matsalar da kuma yadda taɓarɓarewar ilimin firamare da tarbiyyar yara ya addabi al’umma ne aka fito da shirin gyara da tayar da komaɗar ilimin firamare ta hanyar ƙirƙiro da tsare-tsare masu muhimmanci waɗanda hukumomin gwamnati a matakin jihohi da na ƙasa suka ayyanar.

Sai dai wannan lamarin bai cimma burin da ake so ba sakamakon riƙon sakainar kashi da ko oho da ainihin jami’an da aka bai wa aikin suka yi. Hakan ya haddasa giɓi mai yawa ga lalacewar tarbiyyar karatun da hazaƙa tsakanin ɗalibai tun daga lokacin ƙirƙiro shirin bunƙasa ilimin firamare wanda Gwamnatin  Obasanjo ta yi.

Jahar Zamfara kamar sauran jihohin arewa da ma wasu jihohin Najeriya, sun fuskanci matsalar rashin kulawa da lalacewar bunƙasar karatu na wani lokaci sakamakon riƙon sakainar kashi da aka yi wa shirin duk da maƙudan kuɗaɗen da aka kashe.

Hakan ya yi illa ga hazaƙa, tarbiyya da ƙwarewa a wasu darussa masu muhimmanci ga kusan yara masu yawa, waɗanda ya kamata su sami ingantaccen ilimi tun a matakin firamare a Jahar ta Zamfara.

Haka ma jihar ta kasance cikin jihohin da suke a sahun na rashin wadataccen ilimin firamare a jerin jihohin da suka fi fuskantar wannan matsalar a ƙididdigar Hukumar Kula da Al’adu da kuma tallafin ilimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta UNESCO.

Tsarin bayar da ilimin firamare da aka tsara da maƙudan biliyoyin kuɗaɗen da aka kashe domin amfanin shirin, sun sha ruwa, domin kuwa hakan bai amfanar da komi ba illa asarar dukiya da lokacin da aka yi a Jihar Zamfara.

Tsarin tallafi da gyaran azuzuwa na karatu da samar da kayan aiki a makarantun firamare ma ya haɗu da cikas da ban takaici, sakamakon ko oho da aka yi wajen wannan shirin ga waɗanda ke da alhakin gyaran.

Ci gaba da yin kashe mu raba da rashin alƙibla ga wasu jami’an ƙananan hukumomi da ‘yan kwangila, haɗe da sakacin ƙananan hukumomin mulkin aihar goma sha huɗu wajen tsayawa su lura kuma su tabbatar da aikata ayyukan kirki, ya janyo asara mai ɗimbin yawa a kan makomar ilimin yara.

Dangane da sanin waɗannan matsaloli da kuma kasancewarsa tsohon malamin makaranta kuma ma’aikacin hukumar ilimi ta LEA a baya; ya sanya Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’Aziz Yari nazari da ɗaukar lokaci ga wanda zai iya hannunta makomar ilimin Firamaren ta Jihar Zamfara gare shi.

Tsayawa a kan manufarsa da aka san shi da ita, domin tabbatar da cimma burinsa na gyara da tayar da komaɗar matsalolin ilimin Firamaren ne ya sanya ya zaƙulo mutumin da ake ganin ya samu karɓuwa nan take ga kusan ilahirin al’ummar jihar wajen gaskiya da tsare aiki ga lamarin bunƙasa Jahar ta Zamfara.

Dangane da hakan ne ya sanya Gwamnan jahar, ya ga dacewar Murtala Adamu wajen miƙa masa amanar shugabancin Hukumar Kula da Ilimin Firamare domin fito da hanyar tayar da komaɗar ilimi, tarbiyya da kuma bunƙasa karatun yara. Ga dukkan alamu ya sanya hannu biyu ya karɓa sakamakon tsare-tsaren da ake ganin ya soma da su wajen cimma nasarar bunƙasa ilimin firamare na jahar.

Ba shakka ba ƙaramin lissafi da hangen nesa ake ganin Gwamna Yari ya yi wajen cimma burinsa na ɗauko wanda ya dace a ganin samun nasara da farfaɗo matsalar Ilmin firamare ba. A kan wannan al’ummar jihar, ke ganin shugaban hukumar yana da ƙalubale, mai yawa da ke gabansa ga cimma nasara.

Wasu daga cikin muhimman ƙalubalen sun ƙunshi tabbatar wa al’ummar Jahar Zamfara cewar zai iya kai gaci, ga bunƙasa da kuma farfaɗo da darajar wannan ilimin da ke da muhimmanci ga rayuwar al’ummar jahar baki ɗayansu.

A jahar Zamfara dai akwai kusan makarantun firamare birjik a kusan kowane ƙauye ko gunduma da yanki na ƙananan hukumomin mulkin jahar. To, sai dai wannan ba shi ne abin dubawa ba, muhimmin abin lura, su ne yadda za a bunƙasa darajar ilimin firamaren ga al’ummar jihar.

Mafi yawan makarantun firamaren da ke jahar duk suna cikin halin wahala da rashin kayan aiki. Sai kuma lallacewar azuzuwan karatu da gine-ginen makarantun yayin da wasu ma sun rufta sosai ba wurin karatu ga ɗaliban. Akwai kuma rashin kujeru da tebura na zama domin karatu, da rashin littattafan koyarwa da na karatu a kusan duk mafi rinjayen makarantun.

Haka ma akwai matsalar ƙwarewa da kuma na kayan aiki ga wasu mafi rinjayen malaman da aka ɗauka domin koyarwa a makarantun. Wasu ma daga cikinsu ba su da masaniya ko kaɗan a kan yadda za su iya kula da ɗaliban firamare.

Wasu daga cikin makarantun firamaren da ke da kusan yara hamsin zuwa ɗari, suna fama da rashin malami koda ɗaya ko kuma kayan aikin da za a yi amfani da su a makaranta, hakan ya jawo ba su aikata komi, illa guje-guje da wasanni.

Kusan kashi saba’in bisa ɗari na malaman da ake da su a jahar, kamar sauran jahohin arewa ba ƙwarraru ba ne, wasu daga cikinsu ma ba su zuwa makarantunsu sai a lokacin biyan albashi ko kuma wani taron wanda ya danganci ƙarin kuɗaɗe, inji wata majiya.

Haka ma ana zargin wasu makarantun firamare na Jahar Zamfara kamar sauran jahohi suna ɗauke da ma’aikatan bogi da ke karɓar albashi daga jami’an yankunan ƙananan hukumomin mulkin na LEA.

Wasu daga cikin jami’an ilimin yankunna ƙananan hukumomin mulki ana zarginsu da yin kashe mu raba da wasu malaman makarantun, abin da ya kawo dalilin taɓarɓarewar ilimin har ma gwamnatin jaha tana asarar miliyoyin nairori da ake ɓatarwa da sunan bunƙasa ilimin makarantun firamaren da kuma faɗaɗa karatun yara ƙanana.

Wannan matsalar ta janyo ɗaukar hankali na wasu muhimman hukumomin bayar da tallafi da kawo ɗauki ga Ilmin Firamare a wajen jihar abin da ya sanya suka buƙaci gyara da sake tabbatar da inganttaciyar alƙibla ga ilimi a Jihar ta Zamfara.

Baki ɗayan jihar dai tana da kusan yawan makarantun firamare har…. waɗanda suke da yawan ɗalibai har kusan…waɗannan makarantun suna da buƙatar kulawa domin faɗaɗa ilimin da kuma samar da ingantaccen ilimi ga yaran Jahar Zamfara.

Kamar yadda ake faɗi a lokuta da dama bayan karɓar jagorancinsa, Murtala Adamu zai fuskanci ƙalubalen ga wasu da ke neman bai kai ga nasara ba, sakamakon yadda yake nufin gyara da kuma tayar da komaɗar ilimin ba tare da damuwa da ƙafar da ya zungura ba.

Haka ma wasu na ganin zai fuskanci wasu ‘yan mun iya’ da suke ganin ala dole sai an yi tafiyar da su wajen cimma nasara ga gyara da kuma tabbatar da ci gaban ilimin na jahar. Wasu daga cikinsu na nuna adawar a fili ta hanyar yin zagon ƙasa, inda suke iyawa ko kuma neman ɓata suna ga shirin da duk zai ɓullo da shi a nan gaba.

A kodayaushe aka fito da gyara domin amfanin ci gaban al’umma ala dole a samu masu nuna rashin amincewarsu ga neman inganta samun nasarar waɗannan gyare-gyare.

Kasancewar Murtala Adamu ya shigo da niyya tagari wajen fito da hanyar magance matsalar da ilimin Firamare ya shiga a ciki, wannan adawar ba za ta yi masa illa ko kaɗan ba, illa ƙara masa ƙarfin gwiwa ga fuskantar matsalolin da ke gabansa, inji wani tsohon ma’aikacin LEA na Zamfara.

Ba shakka yana da masaniyar hakan, kasancewarsa ɗan siyasa kuma malamin makaranta, musamman ma  kan abin da ya shafi sanin halayyar al’umma. Don haka ake ganin ƙalubalen da zai fuskanta shi ne gaskiya da adalci ga shirin da ya ƙirƙiro.

A jawabin da ya yi wa manyan jami’an ilimi na ƙananan hukumomi mulki wato, ES, ya fito fili ya tabbatar masu da cewar ba zai yi wata- wata  wajen canza duk wanda ya nuna rashin kulawa da kuma kishi ga gyaran matsalar ilimi a yankinsa ba.

Ya yi masu gargaɗi ta hanyar nuna takaicinsa a kan halin da ilimin firamare yake ciki a jihar ta hanyar ‘ jirwaye mai kamar wanka ’ na cewar, ala dole su tsaya yankunansu wajen gyara da aiki tuƙuru domin ganin cewar sun kula da muhimman hanyoyi na bunƙasa ilimi da kuma karatu a makarantun.

Wannan zai ba su dama wajen fito da matsalolin da ke neman agaji daga hukumar kai tsaye wajen samar da kayan aiki da kuma bunƙasa karatun ɗalibansu. Ya ce zai taka birki  kan duk wani jami’in da ya kasa nemo hanyar magance matsalar.

Haka ma ya gargaɗe su wajen kauce wa fadanci ko ƙoƙarin nemo hanyar kashe mu raba  kan dukiyar jama’a; maimakon haka su mayar da hankali wajen taimaka wa hukumar ga samun nasarar abin da take nema na bunƙasa ilimin firamare a jahar Zamfara.

Ɗaya daga cikin muhimman gyare-gyaren waɗanda Gwamna Abdul’Aziz Yari ke hanƙoron samu ga sha’anin ilimi a jihar ne ya sanya amince wa Murtala Adamu Jangeɓe da fito da hanyoyin da suka dace ba tare da katsalanda ga samun nasara ta farfaɗo da ilimin Firamare a jihar ba.

Wannan damar wadda ba kasafai shugabannin hukumomin gwamnati ke samun irin ta ba; haƙiƙa za ta taimaka masa ga cimma nasarar da ake hanƙoron samu ga ayyukan raya ilimi a jihar, da ma Zamfarawa na yi masa kallon mutum mai gaskiya da riƙon amana a kan dukkan ayyukan da aka sanya shi gaba.

A jawabinsa ga sabon shugaban Hukumar Ilimin Firamare na jihar, Gwamna Yari ya fito fili ya tabbatar masa da cewar muhimmin abin lura ga naɗinsa a kan wannan muƙami, shi ne riƙon amana da tsare gaskiya da aiki tuƙuru, ga ciyar da Jihar Zamfara gaba da aka sanar masa.

Wannan na daga cikin dacewar da ta sanya aka hannunta masa amanar makomar ilimin firamare na jihar baki ɗaya ga hannunsa, domin ya fito da kuma tsara manufa ta cimma nasarar bunƙasa ilimin a jihar baki ɗaya.

Wasu daga cikinsu, sun ƙunshi gyaran tsaf ga makomar ɗaliban da ke karatun firamare da kuma inganta hanyoyin koyarwa wanda ya dace da yanayin da ake ciki a yanzu.

Muhimmin abin da Gwamna Yari ya fi buƙatar ganin an farfaɗo daga ilimin na firamare akwai sake tayar da komaɗar tarbiyyar karatun yara da kuma bunƙasa koyar da darussan kimiyya, lissafi, turanci da islamiyya da sauran darussan da za su kawo ci gaba ga jihar.

Waɗanan darussan na daga cikin manyan darussa waɗanda ake fuskanta ga karatun yara a firamare, kusan duk lokutan da suka gabata musamman a lokacin jarrabawar fita daga makarantun zuwa na gaba.

A wani taron gabatar da kansa wanda ya gudanar da manya da ƙananan jami’an hukumar ilimin Firamare ta jahar tun kafin ya fara aiki, Murtala Adamu Jangebe ya fito fili ya ƙalubalanci jami’an wajen mayar da hankali ga muhimmin aikin gyara da kuma farfaɗo da darajar ilimi a jahar.

Haka ma, ya nuna masu akwai jan aiki gaba na kishin ƙasa, riƙon amana da tsare gaskiya wajen ciyar da jahar gaba a kan abin da ya shafi ci gaban ilimin baki ɗaya.

Ya tabbatar masu cewar ilimin Firamare shi ne muhimmin tsaunin samun nasara na sauran karatun ɗaliban jihar, domin haka dole ne a yi haƙuri a sanya kishin ƙasa, tsoron Allah da kuma gaskiya wajen aiki ba dare ba rana wajen ganin an cimma wannan manufar.

Ya tunatar da su a kan amanar da  Gwamna ya ba su ta makomar al’ummar Jahar Zamfara ga samun inganataccen tafarki na bunƙasa tarbiyya da karatun yara, wannan ba wata ja da baya ko jin kunya wajen tabbatar da shi kuwa.

“Muhimmin aikin da ke gabanmu baki ɗayanmu (inji Murtala Adamu) shi ne maido da darajar ilimi da kuma bunƙasa ayyukan da suka shafi ci gaban ilimin firamare a wannan jahar. Wannan kuwa ya ƙunshi aiki tuƙuru, tsare gaskiya da kuma kiyaye ƙa’idar aiki garemu baki ɗaya”.

Haƙiƙa ya dace ilahirin jama’ar Jahar Zamfara sun bai wa Gwamnati da Hukumar Ilimin Firamare goyon baya ga cimma wannan ƙalubalen da ta sanya gaba saboda ceto makomar ɗaliban makarantun firamare.

Taimaka wa gwamnati da sanya yara makaranta da kuma kula da zuwansu na daga cikin ababen da suke na bai wa gwamnati goyon baya, wanda iyaye za su yi wajen ganin cewar ‘ya’yansu na samun ilimin da ya dace.

Shi kanshi Gwamna Yari ya yi alƙawarin bayar da duk abin da ya dace na goyon baya da kuma tallafi ga Hukumar domin ganin cewar ta cimma burinta na farfaɗo da bunƙasa ilimin firamare.

A lokuta da dama ya faɗi hakan, musamman a wani taron ƙasa na gwamnonin Arewa da aka gudanar a Kaduna, ya fito fili ya ce ba ja da baya ga shirin bunƙasa ilimin firamare da kuma ci gabansa a Jihar Zamfara.

Gwamnan wanda ke hira da manema labarai, ya bayyana cewar; wasu daga cikin muhimman ababen da yake son mayar da hankalin samun nasararsu a yanzu ga jiharsa, sun ƙunshi bunƙasa tarbiyya da kuma ilimin Firamare da na Sakandare, tattalin arziƙi da zaman lafiya a jahar baki ɗaya.

Haƙiƙa Gwamna Yari na da aminci da yarda mai yawa ga shugaban Hukumar Ilimin Firamare ta Jahar Zamfara, Honorabul. Murtala Adamu, domin haka ya dace ya samu goyon baya ga sauran malamai, iyayen yara, jami’an ilimi na hukumar da sauran illahirin al’ummar Zamfara, wajen sauke nauyin aikin da aka ɗora masa na gyara da kuma tabbatar da bunƙasar Ilimin Firamare a jihar.

Wannan zai taimaka matuƙa ga samun nasarar makomar yaran da ke a makarantu da waɗanda za su zo daga baya ga ciyar da jahar gaba a fannin bunƙasar tattalin arziƙi, ilimi, tarbiyya da kuma ayyukan yi baki ɗaya.

Ilimin firamare yana da muhimmanci mai yawa ga al’ummarmu wajen tabbatar da tarbiyya da kuma makomar karatun ɗaliban jahar. Domin wannan akwai ƙalubale mai yawa ga abokan aiki na hukumar a matakin jaha, jami’an yankunan ƙananan hukumomin mulki da kuma sauran jama’a ga fatar alheri da haɗa kai ga samun nasara.

 

Yusuf Abubakar Ɗan Jarida Ne Mai Zaman Kansa

Lamba 24 Unguwar Gwaza, Gusau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here