ƘUNGIYAR Jama’atu Nasril Islam (JNI) a ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban JNI, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta yi Allah-wadai da harin bam da aka kai a mujami’ar St. Rita da ke Kaduna a kwanakin baya.
Wannan Allah-wadai yana ƙunshe a cikin sanarwar da sakataren JNI, Dokta Khalid Abubakar Aliyu, ya sanya mata hannu kuma aka raba wa manema labarai ita.
Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara sanya ido tare da duƙufa a kan matakan shawo kan sanya bam na rashin tunani.
Game da waɗanda lamarin ya rutsa da su, ya yi addu’ar Allah Ya ba iyalan da suka rasa nasu juriyar wannan babban rashi. Haka kuma ya yi addu’ar Allah ya kiyaye faruwar haka a nan gaba.
Sarkin Musulmi ya ce kada Allah Ya sanya masu aikata wannan ta’asa su kai ga nasarar kawo hargitsi a Kaduna.
A ƙarshe, shugaban JNI ɗin ya nemi ɗaukacin al’ummar Musulmi da su yi addu’a ga Allah maɗaukakin sarki da Ya kawo ƙarshen wannan hali da ake ciki tare da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan.