Kai harin tarwatsa cibiyar kasuwanci ta Duniya wato ‘World Trade Organisation’ (WTO) wanda aka fi sani da harin Satumba 11. Kamar dai yadda duk wani mai ƙwaƙƙwaran bincike kan sharrin ƙasashen yammacin duniya irin su Amurka, Ingila da kuma Isra’ila kan Musulmin duniya, to, zai fahimci yadda sharrin waɗannan mutane yake. Sannan zai riƙa fahimtar wasu shirye-shiryen su na cutar da al’ummar da ba su ji ba, kuma ba su gani ba. Sannan ko da yaushe sukan shirya wasu ƙulle-ƙulle na cutarwa kan al’ummar Musulmi, domin sukan bi ta wani salo ne na wawantar da mutane, sannan kuma su kawar da hankulan mutane game da abubuwan da suke aikatawa da sunan wasu, don kada a gane su ne ke cutar da mutane kai tsaye.
Jama’a duk wannan shimfiɗar da nake ta yi, ina yi ne domin al’ummar Musulmi su fahimci sharrin maƙiyan mu irin su Amurka da ƙawayenta, ina fatar ladan wannan aiki Allah ya kai shi ga kakanni na waɗanda suka riga mu zuwa gidan gaskiya. Sannan kuma ina yin wannan shimfiɗa ce, domin al’ummar Musulmi mu ƙara fahimtar haƙiƙanin abin da ya faru a harin bam na Satumba 11.
Idan ka kalli wannan hoto da kyau kana iya ganin wannan dogon ginin yana ci da wuta, amma waɗannan jiragen guda biyu basu ma kai ga jikin ginin ba ma tukuna, ballantana su fashe a ciki har su sa ya kama da wuta. Sannan idan ka kalli waɗannan jiragen guda biyu kallo irin na ƙurulla musamman ga wace ta ɗan fi girman, to, za ka ga alamun harbi sun yi kuri a jikin jirgin har wuri uku, abin da muke gani a ‘Action film’ idan za a harbo jirgin sama ko kuma idan za a harbi mutum wato ‘target’ a turance, wato alamun harbi da bindiga wanda hakan ke nufin cewa, ana nufin wargaza waɗannan jiragen sama ne daga waje. Sannan kuma labari ya zo daga baya cewa, “an kama mutanen da suka ɗauki wannan hoton” domin hakan bai yi wa gwamnatin ta Amurka daɗi ba.
Sannan wani abin lura kuma, shi ne, a ranar da wannan harin zai auku duk wani bature mai ɗan muƙami a wannan ofis, to, bai zo aiki ba, tambaya? Sun san abin da zai faru ne? Sannan kuma mai ya sa suka kama mutanen da suka ɗauki wannan hoton? Ba sa so a ga ginin ya fara ci da wuta ne kafin jiragen su kai gare shi a fahimci shiri ne ko yaya? Mai karatu ka bai wa kanka amsa!.
Amma su abin da suke cewa, shi ne Ƙungiyar Alƙa’ida ce, ta ce ta ɗauki alhakin wannan harin na tarwatsa WTO, sannan kuma abin da yake da matuƙar muhimmanci mutane mu su sani shi ne, ba fa wasu ba ne Alƙa’ida illa Amurka da ƙawayenta. Saboda haka mu kwana da sanin cewa, Amurka ce da kanta ta kai wa cibiyar kasuwanci ta duniya (WTO) hari da kanta, domin kawai ta ɓata sunan Musulmi da Musulunci a duniya.
Inda kuma Allah ya tona masu asiri shi ne, a wannan hoton, shi ya sa ma aka kama waɗanda suka ɗauki wannan hoton, amma Amurka cewa, take yi wai “jiragen sama ne suka zo suka doki ginin, sannan suka shiga kuma suka fashe a ciki, wanda wai hakan ne ya yi sanadiyyar rugujewar wannan ginin” inji Amurka, wanda duk wanda ya kalli wannan hoton zai fahimci irin ƙaryar da Amurka ta sharara.
Yanzu dai mai karatu kana iya ganin bam ya shiga cikin ginin kuma yana ci da wuta kafin waɗannan jiragen ma su kai gare shi, kuma ko waɗannan jiragen Amurkar ce ta turo su da kanta domin kawai ta ɓata sunan mu, mu Musulmi da addinin mu na Musulunci ta haka ne suke ganin za a ƙyamace mu kuma a daina shigowa addinin, to, Amurka da sauran ƙawayenki da duk wasu masu tunani irin taku sai mu ce maku ƙaryar ku, Allah ya fi ku, ku yi shirri insha Allahu sai ya zame mana alhairi. Idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira.
Nura Ibrahim Khalil, ya ruwaito daga Zariya.