Rikicin Mallakar Rijiyoyin Mai: Jonathan Ya Gana Da Peter Obi Da Idris Wada

0
1222

SHUGABA Goodluck Jonathan ya yi wata ganawar sirri da gwamnanonin Jahohin Anambara da Kogi, Peter Obi da Kyaftin Idris Wada da kuma mataimakin gwamnan Jahar Enugu a wani yunƙurin samo bakin zaren warware rikicin da ke tsakanin jahohin game da mallakar  rijiyoyin man fetur.

Iƙirarin mallakar rijiyoyin man fetur ɗin dai ta yi ƙamari ne bayan da Shugaba Jonathan ya bayyana  Jahar Anambara a cikin jerin jahohin da suka mallaki man fetur a wata ziyara da ya kai a Jahar a kwanakin baya.

A sakamakon hakan ne dai Jahar Kogi ta mayar da martani da kakkausan harshe inda ta bayyana cewa, rijiyoyin man na cikin yankin ƙaramar hukumar Abaji ne wadda ke cikin Jahar Kogi.

Idan ba a manta ba dai, har ila, akwai rikici a game da mallakar rijiyoyin mai tsakanin Jahohin Kuros Ribas da Akwa-Ibom da kuma Jahohin Ribas da Bayelsa wadda ke samun goyon bayan shugaban ƙasa.

Ko a ranar Litinin ɗin da ta gabata, ƙungiyar ‘yan ƙabilar Kalabari sun yi wata zanga-zanga a birnin Abuja cewa, ana shirin hannunta wa Jahar Bayelsa inda Shugaba Jonathan ya fito wasu rijiyoyin mai shida waɗanda mallakar Jahar Ribas ne.

Tuni dai fadar shugaban ƙasa ta yi amfani da wannan zargin da ake yi wa shugaba Jonathan inda ta bayyana hakan a matsayin labarin ƙanzon kurege kawai, inda ta ƙara da cewa, hukumomin da ke da alhakin warware rikicin iyakoki na nan na gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

A lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan ganawar su da shugaban ƙasa, Gwamna Obi ya bada tabbacin cewa, za a warware rikicin cikin lumana, kuma tuni shugaba Jonathan ya fara samun hakan.

Shi ma gwamnan Jahar Kogi, Idris Wada ya bayyana ƙwarin gwiwar sa cewa, tun da har shugaban ƙasa ya shiga tsakani, to, hukumar kula da iyakoki ta ƙasa za ta gudanar da ayyukanta a kan adalci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here