- A. MASAGALA, Daga Benin
ƁARAYI sun yi wa wani ɗan acaɓa mai suna Ali Alhasan Garko dukan tsiya tare da sassara shi da adda suka karɓe masa mashin ɗinsa mai lamba BEN 769 QB suka tafi suka bar shi kwance cikin jini da munanan raunuka.
Hakan ya faru ne a ƙarshen makon da ya gabata a wata Unguwar Urora da ke kan iyakar ƙaramar hukumar Ikpoba Okha da Uhonmwode a Jaihar Edo.
Shi dai wannan matashi Ali Alhasan ɗan asalin ƙaramar hukumar Garko can Jahar Kano mai yin haya da babur a garin Benin, Jahar Edo ya fito tafiyar aiki da safiya kamar yadda ya saba a kullum yana ɗaukan mutane (fasinjoji) ya kai wurin aiki su biya shi amma sai a ƙarshen makon jiya ya faɗa hannun ɓarayi dab da goshin magariba ya gamu da wasu ɓarayi su biyu suka tsayar da shi, ya tsaya sai suka yi jinga da shi suka shirya sun gaya masa inda zai kai ya sauke su.
Ɗan acaɓan Ali Alhasan ya ce “na haɗu da wasu gayun su biyu ban sani ba ashe su ɓarayi ne, ɗayan yana riƙe da jakar ruwa, ɗayan kuma yana riƙe da biredi sai suka tsayar da ni na tsaya suka ce da ni, in ɗauke su da babur zuwa cikin Unguwa Urora za su biyani kuɗi Naira100 sai na ɗauke su muna cikin tafiya har muka yi nisa sai suka nuna mini wata hanya da za ta shiga wani lungu a cikin Unguwar kawai da suka tabbatar muka yi nisa muka fara shiga jeji sai suka ce da ni in tsaya a nan za su sauka kafin a ce wani abu kawai babu abin da nake ji sai sara da adda a kaina tun ina tsaye har na faɗi ƙasa ban san lokacin da suka ja mashin ɗina har suka tafi ba suka bar ni ina kwance na yi wanka da jini. Sai wasu mutane ne suka same ni cikin wannan yanayi sai suka ɗauke ni suka kai ni asibiti aka yi mini wannan ɗinki da ka ke gani a kaina duk sun bi sun sassara ni”.
Babban jami’in ‘yan sandan mai kula da shiyyar ta Eyaen, Mista Samson ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce suna ci gaba da bincike na neman waɗanda suka aikata wannan har da sauran miyagun.