An Ja Hankalin Mahajjata A Ƙaramar Hukumar Garko

0
8926

SANI AHMED SAGAGI, Daga

Jami’in riƙo na ƙaramar hukumar Garko, Alhaji Usman Muhammad Ƙofar Nassarawa ya ja hankalin mahajjata na ƙaramar hukumar Garko su ɗari da arba’in kan lallai su zamo jakadu nagari a yayin da suke aiwatar da ayyukan hajjin bana a ƙasa mai tsarki musamman ta fuskar kare dukkanin dokakin ilasar ta Saudiyya.

Usman Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattauna wa da manema labarai a birnin Kano don yi masu murnar barka da salla a inda ya ce tuni alhazan ƙaramar hukumar sun sauka a ƙasar ta Saudiyya kuma suna cikin koshin lafiya sa’annan ya kuma bayyana cewa, ƙaramar hukuma ta bai wa kowane Alhaji Riyal ɗari don tallafi gare su, a saboda haka ya neme su kan su yawaita addu’ar zaman lafiya ga ƙaramar hukumar Garko da Kano sai kuma Najeriya ta yadda hankalin al’umma zai kwanta a halin da ake ciki.

A wani labarin kuma Alhaji Muhammad Ƙofar Nassarawa ya bayyana cewa, sun tallafa wa ɗaliban da Gwamna Jahar Kano, Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya ɗauki nauyinsu zuwa ƙasashen waje karatu don yin digiri na biyu su ɗari biyar da ɗaya a inda ƙaramar hukumar take da mutane shida sun kuma bai wa kowa a mai kwalkwalwa maire da abin shan ruwa don rage zafi, amma kuma ya name su kan lallai su ma su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

Da ya koma ta kan batun alluran riga-kafin shan-inna kuma jami’in riƙon ya tabbatar da cewa, sun samu nasara samu kaso fiye da yadda suka tsare ana yawan cutar yaran da za a yi wa a faɗin ƙaramar hukumar.

Usman Muhammad ya ƙara da cewa, tuni suka mike don ganin sun fatattaki cutar daga ƙaramar hukumar baki ɗaya ta hanyar haɗa kai da masu unguwanni da dagatai sai kuma hakimin a inda suke fadakar da al’umma muhimmancin alluran rigakafin ta hanyar limamai da malaman makarantun allo da Islamiyya.

Sai dai ya ce babu mai ɗauke da cutar a duk faɗin ƙaramar hukumar baki ɗaya, don kuwa sun sayo sabulai da alawa waɗanda suke bai wa yaran da aka yi wa alluran.

A ƙarshe ya buƙaci dukkannin al’ummar yankin su ci gaba da bayar da ‘ya’yansu don tabbatuwar nasarar shirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here