Matasan Arewa Da Na Kudu: ’Yan Ta’adda Ne Da ’Yan Gada

0
2197

Assalamu Alaikum, don Allah wannan saƙo ne nike son isar wa duniya cewa, mu ‘yan arewa mutane ne masu son zama lafiya, masu son ci gaba, saboda haka ba mu da ta’addanci da ’yan ta’adda  ko ‘fundamentalist’, ko extremists, kawai abin da ke faruwa game da tashe-tashen hankula shi ne, waɗannan mutane masu tada bama-bamai, mutane ne da suke ganin an zalunce su, ba a yi masu adalci ba. An karkashe su, an kore su, an hana su zama gidajensu, kuma suna cikin fushi matuƙa.

Saboda haka shugabannin arewa da shugabannin Najeriya ku sani; a yi ƙoƙarin yin adalci; a yi maganin yunwa, a yi maganin rashin aikin yi da talaucin da ke addabar Arewa, duk idan an yi wannan insha-Allah ina ganin za a samu zaman lafiya a Arewa. Sannan waɗannan mutane a bi su da lallashi da ban haƙuri, ba amfani da ƙarfi ba. Ina ganin idan jami’an tsaron Najeriya suka ci gaba da amfani da ƙarfi a wannan al’amari, to, sai dai su kashe dukkan matasan arewa, domin tsakani da Allah, matasan arewa suna cikin fushi matuƙa a kan yadda ake nuna masu rashin adalci.

Na farko, suna son yin karatu ba hali, domin karatu ya zama sai wane da wane.

Na biyu, waɗanda suka samu damar karatun babu aikin yi.

Na uku, yunwa da talauci ya addabe su, kullum kuma suna kallon yadda manyan arewa suke fantamawa, su da iyalansu. Kuma matasan arewa suna jin labarin yadda manyan kudu suke taimakon matasansu, ta hanyar ilimi, aikin yi da sauransu.

Na huɗu, ka duba yadda wannan Gwamnati ta Jonathan take tura ‘yan Neja-Delta matasa makaranta a ƙasashen waje, ga kuma albashi na musamman da ake masu da sunan ahuwa, sun yi kuɗi ba su da matsala, amma matasan arewa kullum kashe su ake yi da sunnan yaƙi da ta’addanci. Gwamnoninmu, malaman addini, sarakuna da dukkanin shugabanin arewa kowa ya yi shiru a kan wannan. A yau an wayi gari, Neja-Delta suna karɓar maƙudan kuɗaɗe da sunan ‘amnesty’, ga hukumar raya yankin Neja-Delta, wato NDDC ga kashi 13 da ake ware masu, ga ‘Allocation’, ga ministari Neja-Delta da ’Yar’Adua ya ƙirƙiro. Amma arewa fa? Ɗan kason ma da ake bata na ‘Allocation’ na jahohi, an wayi gari sai ka zama ɗan iska, ko ɗan maula ko bafade ko ɗan tumasanci ko ɗan bangar siyasa, sannan ka samu wani abu a wurin ‘yan siyasa. Yau matashin kudu ya zama ɗan gata, amma matashin Arewa ya zama ɗan ta’adda wai.

Tompolo, Boylof, Ateke Tom, Dokubo Asari, Gani Adams, shugaban MASSOB, Egbesu Boys, da sauran ire-irensu, sun zama hamshakai, suna fantamawa.

Saboda haka wallahi ina shaida maku cewa, babu maganar ta’addanci. A’a magana ce ta rashin adalci, babu yanda za a yi a zauna lafiya, a cikin yanayi irin wannan na rashin adalci. Manyan arewa, ina kiran ku ku canza tafiyarku, ku rungumi talakawanku, ku taimaka masu, ku lallashe su, ku ja su a jika, kada ku yar da su, kada ku riƙa ƙyamarsu, ba yadda za a yi ya kasance kun yi nesa da matasa ba ku sauraronsu, an sami tazara mai nisa tsakaninku, sannan ku ce kuna son zaman lafiya, ba zai yiwu ba. Kun san matasan nan fa su ne manyan gobe.

Bill Clinton, John Campbell, Johny Carson, da dukkan wani mai mutunci, duk sun faɗa cewa, rashin adalcin da ake yi wa arewa shi ya jawo waɗannan matsalolin, to, wallahi maganarsu gaskiya ce ku saurare ta da idon basira.

Daga ƙarshe, ina jinjina wa T. Y. Ɗanjuma, saboda ƙoƙarin da yake yi na taimakon talakawa, a T. Y. Ɗanjuma Foundation da kuma Furofesa Jibril Aminu, sSaboda shi ma ƙoƙarinsa da kuma fadar gaskiya da Sanata Bukar Abba Ibrahim saboda shi ma ya faɗi gaskiya cewa, rashin adalcin da ake yi shi ke jawo wannan tashin-tashina, to, wannan gaskiya ne, ba wani ta’addanci wallahi.

Sannan ina rufe wannan saƙo da maganar wani mutum, wanda wannan magana gaskiya ce ba ƙarya ba. Yake cewa, (wannan mutum shi ne; Fredrick Douglas Washington DC). “where Justice is denied, where poverty is enforced, where ignorance prevails and where anyone class is made to feel that society is in an organized conspiracy to oppress, Rob and degrade them, Neither persons nor property will be safe”.

Wannan Magana Gaskiya ce, kuma wannan shi ne yake faruwa a Arewa.

Kuma duk wani shugaban arewa idan shi Musulmi ne, to, ya yi koyi da mutane irinsu; Sardanna, Tafawa Ɓalewa, Ribaɗu, Aliyu Makaman Bida, Sa Abubakar na III, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da sauran su. Idan shi Kirista ne ya yi  koyi da mutane irin su: Ishaya Audu, Joseph Tarka, Achimugu, Ohikere, da Sunday Awoniyi, (wanda har ma ake kiransa Sunday Ɗan Sardauna) da sauransu. Waɗannan mutane ba su raba kan arewa ba, kuma sun yi al’amurransu tsakani da Allah.

Sannan ina kira ga shugabannin addini na arewa su ji tsoron Allah, Musulminsu da Kiristocinsu, domin suna bada gudunmuwa wajen raba kan al’ummar arewa. Sannan abin tambaya a nan shi ne: shin idan sun ci gaba da hura wutar fitina ta hanyar raba kan Musulmi da Kirista a arewa, cikinsu akwai wanda abin ba zai shafe shi ba? Kuma su je kudu, su gani shin da matasan kudu da na arewa, wane ne ya fi ci gaba? Ni ina shiga kudancin Najeriya domin wa’azi da da’awah, kuma na san cewa, akwai bambanci tsakanin matashin kudu da na arewa. Sannan mu yi wa kanmu adalci a duk abin da za mu yi ko za mu faɗa, in har bokon ‘yan arewa da ‘yan bokon arewa, sun kawo ci gaba ga arewa da ‘yan arewa, to, ba za a sami wani ya ce Boko Haramun ne ba.

To, an wayi gari ɗan bokon arewa yana ƙyamar ‘yan uwansa, yana ƙyamar addininsa, ya ware gefe daga shi sai ‘ya‘yansa sai matarsa. Ya fi son a yi mashi maula da fadanci, ya riƙa raba Naira ɗari, ɗari biyu, ko ya riƙa dafa abinci yana fitowa da shi ƙofar gida ana ci, amma ba zai iya yi maka hanyar da za ka sami abincin ba. Wanda ‘yan kudu ba haka suke yi ba.

Maganar da T. Y. Ɗanjuma ya taɓa yi cewa, Najeriya za ta iya zama Somaliya wannan fa gaskiya ne yake faɗa, domin rashin adalci da ake wa matasan arewa da kuma jefa su cikin talauci da yunwa, an wayi gari fashi da makami, kisan gilla zubar da jini, sun yi katutu a arewa. Da ma an ce: “hungry man is an angry man”.  “when poverty comes in the door, love goes out the window”.  “idle mind is the devil workshop”.  “poverty waits at the gates of idleness”.  kuma ance: “as you sow, so shall you reap”. “as you make your bed, you have to lie on it”.

Don Allah ina miƙa gaisuwa ta ga Dokta Bello Kirfi da sauran ‘yan uwa Musulmi, irin su Dokta Muhammad Sani Abdu da suka yi yunƙurin ganin cewa, an samu maslaha ta hanyar shirya taron dattawan yankin arewa maso gabas. To, amma su sani wannan matsala ce ta arewa gaba ɗaya. Allah ya saka masu da alkhairinSa amin. Ma’assalam.

 

Murtada Muhammad, Ya rubuto ne daga Gusau. (Abu Mus’ab) Chief Imam: Nagazi Jumu’at Mosque Okene, Kogi State. 08038289761; 08056557477.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here