Sarkin Hausawan Ehor Ya Yi Kira A Duƙufa Da Addu’ar Neman Zaman Lafiya

0
8495
  1. A masgala, Daga Benin

SARKIN Hausawan Ehor, Alhaji Yusufu Alhasan ya yi kira ga ɗaukacin al’ummar ƙasar nan da su kasance masu ƙaunar juna kuma su haɗa kai tare da duƙufa da yin addu’o’in fatar alheri da zaman lafiya ga ƙasar nan.

Ya bayyana buƙatar hakan ne, a ƙarshen makon jiya a garin Benin fadar mulkin Gwamnatin Jahar Edo.

Sakin Hausawan garin Ehor, hedikwatar ƙaramar hukumar Uhonmwode, Jahar Edo ya yi wannan kiran ne tare da bayyana cewa irin matsalolin da ake gani yake ci gaba da ɗorewa a ƙasar nan kuma aka kasa shawo kansu a hukumance, to, lallai babu shakka maganinsa sai mu koma ga Allah mahalicci mu ci gaba da yawaita addu’o’i da sanya tsoron Allah cikin zukatanmu wajen gudanar da ayyukan ibada da mu’amila, inji shi.

AlhajiYusufu ya ce a haƙiƙanin gaskiya duk mai hankali ya san al’ummar ƙasar nan suna fama da mawuyacin hali na tsadar rayuwa ga kuma ainihin rashin tsaro, ko’ina ana zaman zullumi wanda ba a taɓa samun irin hakan ba tun daga lokacin da ƙasar nan ta samu ‘yancin kai a shekara ta 1960 a hannun turawan mulkin mallaka na Ingilan.

Dangane da batun ambaliyar ruwa na wannan shekara da ta faru a kwanakin baya ta yi wa manoma da sauran jama’a ɓarna kuwa, Sarkin Hausawan ya ce “a matsayina shugaban jama’a kuma mai iyali ina mai tausaya masu kuma sai ya ci gaba da cewa, saboda haka ina kira ga gwamnatin ƙasar nan da sauran ƙungiyoyi masu hannu da shuni da su tausayawa al’ummomin da wannan bala’in ya shafa su agaza masu.

Daga nan kuma sai Sarkin Hausawan ya yi wa waɗanda wannan bala’in ya shafa nasiha da cewa, su ɗauke shi tamkar ƙaddara ce daga Allah su yi tawakkali.

Daga bisani sai Sarkin Hausawan ya nuna matuƙar damuwa a kan abin da ya ce tauye haƙin ‘yan Najeriya ne na rashin ci gaba da yasar kogin Neja kuma sai ya tattara ya ɗora laifin ga gwamnatin tarayya.

Sarkin Hausawan ya ce dakatar da wannan aikin na yasar kogin yana daga abin da ya taimaka wajen malalowar ambaliya ruwa cikin wurare da aka manta ko shekaru nawa ne, ba a gani ruwa ya kwanta a wuraren ba sai kuma ya ce gine-gine na wasu wurare da jama’a suke ci ga da yi a bakin kowani gaba ya taimaka wajen toshe magudanun ruwa inda kogunan za su nunfasa.

Sarkin Hausawan, Alhaji Yusufu ya karasa da yi wa al’ummar ƙasar nan nasiha da su ɗauki wannan rayuwar da sauki su daina faɗin rai musamman a wannan lokaci da rayuwa take da tsada kawai abin da ya dace ga kowani mutum ya tsaya a matsayin da Allah ya tsayar da shi tare da ya yi amfani da abin da Allah ya hore masa ya tsare mutuncinsa da shi, inji Sarkin Hausawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here