Wasu ’Yan Bindiga Sun Ƙona Caji Ofis Na Fiƙa

0
8460

MUHAMMAD SANI CHINADE, Daga Damaturu

WASU \’yan bindiga da har zuwa yanzu ba a kai ga sanin ko su wane ne ba sun kai harin a garin Fiƙa fadar ƙaramar hukumar Fiƙa cikin Jahar Yobe a daren ranar Asabar yadda suka shafe awanni suna harbe-harbe gami da jefa abubuwan fashewa da ake kyautata zaton bama-bamai, ne a kan wasu gine-ginen da suka haɗa da babban caji ofis ɗin \’yan sandan garin da cibiyar sadarwa ta kamfanin sadarwa mai zaman kansa na MTN da ke garin da kuma wata makarantar firamare wadda ya kai ga ƙonewarsu.

Wata majiya da ke garin na Fiƙa ta shaida wa wakilinmu kan cewar \’yan bindigar sun fara harbe-harben ne da kusan asubahi wadda suka ɗauki lokaci mai tsawo suna abu ɗaya.

Majiyar ta ƙara da cewar, mazauna garin na Fiƙa a daren wannan ranar sun ga taƙaici domin abu ne, da ba su tsammaci faruwarsa ba a garin sai ga shi kuma abin ya kasance.

Wani mazaunin garin na Fiƙa da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce a daren ya sulale ya karisa kwana a

daji saboda ƙidima da ya yi, ya faɗa ta wayar tafi da gidanka cewar, shi wannan abu ya yi matuƙar ba shi tsoro don abu ne tun ana yinsa a Damaturu, Potiskum, Damagum sai ga shi lamarin ya kariso Fiƙa, ai ka ga in har ba a yi da gaske ba zai kai ga haɗe Jahar ta Yobe baki ɗaya.

Don haka ne malamin ya kirayi gwamnatin Jahar ta Yobe da ta yi wa Allah da manzonSa ta nemi waɗannan \’yan bindiga ta zauna da su don nemo bakin zaren sasanta wannan irin lamari amma in muddin aka ce wuta da wuta ne, to, da ƙyar a magance irin wannan hautsini sai dai ma sake rikita lamarin ta yadda zai bazu kowane wuri na jahar.

Wata majiyar da ba ta da tabbas a garin na Fiƙa ta shaida wa wakilinmu cewar, mutane sama da 10 suka tagayyara a wannan farmaki na \’yan bindiga duk da cewar, kafin \’yan bindigar su kai ga kammala hare-haren na su jami\’an tsaron JTF sun isa garin yadda suka fuskanci \’yan bindigar.

Kakakin rundunar tsaron dawo da zaman lafiya a Jahar ta Yobe, Laftana Lazarus Eli ya tabbatar da wannan hari na \’yan bindiga sai dai kuma ya ce tunin jami\’ansu sun shawo kan lamarin yadda suka dakusar da yunƙurin na \’yan bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here