Akwai Illa Kan Ƙin Aiwatar Da Rahotannin Kwamitocin Bincike — Barista Paki

0
8176

Isah Ahmed, Daga Jos

WANI lauya mai zaman kansa da ke zaune a garin Jos babban birnin Jahar Filato, Barista Aminu Idris Paki, ya bayyana cewa, babu shakka akwai babbar illa kan Ƙin aiwatar da rahotannin binciken da ake kafawa a Ƙasar nan.

Barista Aminu Idris Paki ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ci gaba da cewa, babbar illar da ke tattare da Ƙin aiwatar da rahotannin kwamitocin binciken da ake kafawa shi ne za a ci gaba da aikata laifuffuka a Ƙasar nan. Domin mutane suna ganin ba a yi wa duk wanda ya aikata laifi hukunci.

Ya ce an sha  kafa kwamitocin bincike a Ƙasar nan, amma babu wanda aka taɓa aiwatar da rahotonsa.

Ya ce misali an kafa kwamitocin bincike kan badaƘalar kwangilolin da aka bayar a kamfanin hukumar wutar lantarki ta Ƙasa, da yadda aka yi da kuɗaɗen tallafin  man fetur da sayar da kamfanonin gwamnatin tarayya da dai sauransu amma  har ya zuwa wannan lokaci an shiru da maganar.

Barista Aminu Paki ya yi bayanin cewa, ya  kamata duk wanda ya aikata laifi a Ƙasar nan a hukunta shi. Ya ce idan aka yi haka, abubuwa za su tafi daidai a Ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here