Bai Wa Soja Cin Kashin Kai A Tsarin Mulki Zai Magance Matsalar Tsaro — Alhaji Ɓatagarawa

0
9695

AHMAD ABDUL, Daga Kalaba

AN  bayar da shawara da matakan da za a ɗauka yadda idan an bi su za a shawo kan matsalar tsaro da ta addabi Ƙasar nan musamman Arewacinta.

Malam I. B. Ɓatagarawa wani wanda kan yi sharhi kan al’amuran tsaro kuma ɗan kasuwa mazaunin garin Fatakwal, har wa yau sakataren Ƙungiyar ‘yan asalin Jahar Katsina mazauna yankin kudu maso kudu a hira da wakilinmu na kudanci.

Ya ce “matuƘar ana son shawo kan matsalar tsaro a Ƙasar nan, dole fa sai an tsame harkokin tsaro daga hannun shugabanni sannan kuma a ba shi gurbi mai zaman kansa a cikin tsarin mulkin Ƙasar nan.” Ya ci gaba da cewa, matuƘar za a bari shugaban Ƙasa ne ke da iko kan naɗa manyan jami’an tsaro da kuma sauke su, to, lamari ya ci gaba da zama cikin halin ni ’yasu.

Alhaji Ɓatagarawa ya ci gaba da cewa, “misali ka ga maganar gyara a kundin tsarin mulkin Ƙasa kamata ya yi a tsame hannun shugaban Ƙasa daga naɗa babban jami’in sojoji da kuma ikon cirewa, kamata ya yi a ce an bai wa ɓangaren tsaro ikon cin gashin kansa na naɗawa da sauke manyan jami’ansa, ba fadar shugaban Ƙasa ba, ko shi kamata ya yi a ce an barsu su kare martabar tsarin mulki ko da akwai wani wanda ya taka doka za su hukunta shi amma ba a mayar da su tamkar wasu “’yan amshin shata ba”, inji Ɓatagarawa.

Ya ci gaba da bayyana cewa, “Ƙyale sojoji su zama masu kare dokar Ƙasa a bambantasu da yanayi na dimokuraɗiyya shi ya fi, idan aka Ƙyalesu su riƘa hukunta duk wani ko wata da ya keta hurumin tsarin mulki shi zai kawo maganin taɓarɓarewar tsaro da ake zargi ya faru a Ƙasar nan.

Ya yi addu’a, Allah ya kawo zaman lafiya a Ƙasar nan, Ya magance mana halin da ake ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here