Gudunmawar Mace Wajen Gina Al’umma (7)

0
1587

Mummunan surar da wasu masu bincike game da zamantakewa ke cirowa daga yanayin zamantakewa daban-daban, kamar nazarin nan da aka gudanar a kan yanayin zamantakewar mace a Ƙauyen Masar ko IraƘi ko Maroko ko yankin saharar tsibirin Larabawa da waɗansu; duk suna fitar da matsalolin mace ta hanyar hangen Ƙauyanci da sahara waɗanda suka ci baya kuma suke zaluntar mace sannan sai waɗannan nazarce-nazarce suka shiga bayar da misali ga zamantakewar Musulunci da su saboda mutanen waɗannan wurare Musulmi ne sun gafala da cewa waɗannan tunane-tunane da ayyuka ba su da wata alaƘa da tunane-tunanen Musulunci da ayyukansa.

Kuma ba kawai suna karo da halayya da hukunce-hukuncen Musulunci ba ne, a’a har ma Musulunci ya keɓe wani sashe daga tunane-tunanensa da dokokinsa da halayyarsa don yaƘi da su da sauya su. 2-Jahiltar Musulunci: Daga cikin matsalolin da tunane-tunanen Musulunci ke fuskanta a wannan lokaci da muke ciki, akwai jahiltar Musulunci da wasu ke yi, musamman ma a Ƙasashen Turai, Amurka da sauran nahiyoyin da ba na Musulunci ba.

Waɗannan na jahiltar mafi Ƙaranci daga Ƙa’idojin Musulunci. Kai! suna ma yi mishi wata mummunar fahimta karkatacciya da ke siffanta Musulunci da siffofin: ta’addanci, zubar da jini, ci baya da tsattsuran ra’ayi. Waɗannan tunane-tunane na daga abubuwan da Ƙungiyoyin Mustashrikai (masanan Turawa da suke karantar halayyar Ƙasashen Musulmi da addinin Musulunci don manufofi daban-daban), Sahyoniyawa(Ƙungiyar Yahudawa masu tsaurin ra’ayi) da Ƙungiyoyin Coci-Coci da mishan-mishan na Majami’ar Kiristoci suka sana’anta.

Babu wata surar haƘiƘanin Musulunci a ƘwaƘwalwar mutumin yamma, maimakon haka, duk abin da ke cikin ƘwaƘwalwarsa da fahimtarsa ita ce mummunar sura, kuma da mutumin yammaci ya san haƘiƘanin Musulunci da ya yi maraba da shi. Kuma da ya buɗe hankalinsa don yin muhawara ta ilimi, haka da ya karɓe shi da `yanci da buɗaɗɗiyar ƘwaƘwalwa.

A taƘaice za mu iya karanta wannan babbar matsala cikin jawabin da shugaban Ƙasar Jamus, Roman Hutsog ya yi a ranar 10/1/1995 a lokacin bikin girmama baturiyar nan masaniyar Ƙasashe da al’adun Musulmi (MustashriƘa) a Ƙasar Jamus, Anamari Shamel, mai adalci cikin abubuwan da take rubutawa ta faɗa, a lokacin bikin ba ta kyautar zaman lafiya da Ƙungiyar marubutan Ƙasar Jamus ta ba ta.

Ya faɗi abin da ta faɗa ne na mai mayar da martani ga masu sukar kyautar zaman lafiya da aka ba Shamel saboda kawai tana kariya ga tunane-tunanen Musulunci, kuma tana mu’amala da shi bisa gaskiya da adalci.tana kuma kira zuwa fahimtarsa da sauya mummunar surar da kafafen watsa labaran Turawa ke yi ga Musulunci da Musulmi; sai ya ce:­ “Akwai wani al’amari da ke bayyane Ƙarara cikin alaƘa da mu’amalarmu da Musulunci a wannan lokaci da muke ciki.

Ba za mu yi Ƙarya ga ra’ayin da ya watsu a Jamus ba, idan muka ce: abin da ke zuwa cikin tunanin mafi yawanmu a duk lokacin da aka ambaci Musulunci shi ne: `Dokokin uƘuba na rashin tausayi’ ko `rashin sassaucin addini’ ko zaluntar mace ko tsaurin ra’ayi irin na adawa, sai dai wannan Ƙuntata yanayi ne da ya wajaba mu sauya shi; mu tuna da ambaliyar nan ta hasken Musulunci wadda tun kafin Ƙarnoni shida ko bakwai ta kiyaye wa Ƙasashen yammaci wani sashe babba na tsofaffin abubuwan tarihi, wadda kuma a wancan lokaci ta sami kanta a gaban wani irin nau’i na tunanin yammaci; babbu shakka (wannan ambaliya) ta ji cewa ashe (wannan nau’i na tunanin yammaci) mai tsaurin ra’ayi ne mara sassauci”.

A yankin Ƙarshe na maganarsa, shugaban na Jamus ya yi bayanin dalilin adawa da Musulunci da cewa shi ne jahiltar da Turawa suka yi wa Musulunci, kan haka za mu same shi yana cewa:­ “Ashe ba ta yiwuwa dalilin rashin fahimtarmu ga Musulunci ya zama shi ne ginuwarsa a kan asasai masu zurfi na al’umma mai riƘo da addini alhali mu masu riƘo ne ta fuska mai girma da wani tafarki da bai yarda da addini ba? Don haka ya tabbata ya ya za mu yi mu’amala da wannan nazari mai matsala?

Shin ya yi daidai mu siffanta Musulmi masu tsoron Allah da siffofin `masu tsattsauran ra’ayi, ‘yan ta’adda’ don kawai mu mun rasa ingantaccen riskar yadda izgili yake a zukatan mabiya wasu addinai, ko kuwa saboda mun zama ba za mu iya bayyana irin wannan ingantacciyar fahimta ba?”.

Daga nan sai shugaban na Jamus ya bayyana cewa shi bai san Musulunci yadda ya kamata ba sai bayan da ya karanta littattafan wannan Mustashrika mai adalci (wato Shamel), sai ya ce:­ “Tsinkayata ga irin wannan babban nau’i na fuskance-fuskance cikin tarihin Musulunci da haƘiƘaninsa a halin yanzu bai fara ba sai ta hanyar littattafan Anamari Shamel, akwai kyakkyawan zaton kuma cewa waɗansu ma sun fuskanci irin wannan gwaji. HaƘiƘa muna buƘatar musanya abin da ya ƘuƘe mana na fahimtar sashinmu ga sashi…”

Sannan sai shugaban na Jamus ya yi kira da a fahimci Musulunci don shata wani matsayi game da shi, koma bayan matsayin da ya ginu a kan jahiltar sa, sai ya ce:­ “Ina yin iƘirari da cewa a gabanmu babu wani zaɓi face Ƙara samun masaniya game da duniyar Musulmi matuƘar muna nufin yin aiki don kare haƘƘin ɗan Adam da dimokuraɗiyya”.

Sai kuma ya Ƙara da cewa:­ “HaƘiƘa babban dalilin son sanin Musulunci da fahimtar wadatacciyar wayewar nan ta shi ya samo asali ne daga kasancewarmu cikin wata wayewa da ba shi ba. HaƘiƘa kuwa uwargida Shamel ta faɗaka da wannan buƘata ta rai, ina fatar kuma wannan ya zama shi ne yadda waɗansu masu yawa ke ji..”. “HaƘiƘa Uwargida Anamari Shamel ta share mana fagen haɗuwa da Musulunci. (11)

HaƘiƘa wannan rikici na bayar da kyautar zaman lafiya a Ƙasar Jamus ga masaniyar Ƙasashe da al’adun Musulmi (Shamel) a shekara ta 1995, da dacewar `yan siyasa da wayayyu daga ma’abuta tunani, shehunnan malamai, Turawa masana Ƙasashen Musulmi da al’adun Musulunci, ma’abuta fanni da adabi a Ƙasar Jamus, wadda ake ɗauka daga cikin manyan daulolin duniya a tarihin wannan zamani namu, da nasarar ɓangaren Shamel, wato masu kira zuwa a fahimci Musulunci a bisa haƘiƘaninsa don shata matsaya, daga cikin waɗanda ke sahun gaba na waɗannan kuwa har da manazarta da ‘yan siyasa, a cikin su har da shugaban Ƙasar Jamus wanda muka karanta muhimman zantuttukansa; duk yana nuna mana wani abu ne mai girma daga abubuwan da ke wuyan Musulmi marubuci, manazarci kuma ma’abucin fanni da adabi. Kamar yadda yake wuyan cibiyoyi da malaman addini, wannan kuwa shi ne nauyin yin bayanin Musulunci a bisa haƘiƘaninsa mai haske. Wanda yake tafiya tare da hankali da zuciya cikin sauƘi.

Hanyar aiki da tafarkin nan na AlƘur’ani wajen kira zuwa ga Allah Maɗaukaki:­ “Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau, kuma ka yi muhawara da su kan abin da yake shi ya fi kyau.” Surar Nahali, 16:125. Wannan ka-ce-na-ce na wayewa da ya faru a Jamus da yadda ya kare da nasarar masu kira zuwa ga fahimtar Musulunci, yana tabbatar mana da girman Musulunci, da shirin da ɗan Adam ke da shi na fahimta da karɓar Musulunci, duk kuwa yadda ya kai da isa.

Wannan Ƙa’ida da AlƘur’ani ya tabbatar da ita da faɗarsa:­ “Ku tafi zuwa ga Fir’auna don kuwa HaƘiƘa ya yi tsaurin kai. Sannan ku gaya masa magana mai taushi, ko wataƘila zai karɓi gargaɗi ko kuma ya ji tsoron (azabar Allah)”. Surar Ɗaha, 20:43-44.

Mu Kwana Nan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here