Harkar WaƘa Da Fim Harka Ce Ta Hanyar Faɗakarwa -Birniwa (2)

0
9295

GTK: Shin waƘoƘin da ka ke rerawa, kana waƘoƘi ne irin na zamani ko kana kwaikwayon waƘoƘin mutanen da ne?

El-Mu’az: Ah, waƘoƘin da nake yi irin waƘoƘin zamani ne, amma kalaman da nake amfani da su suna da bambanci domin za ka ji sun girmi zamanin saboda irin baiwa da basirar da Allah Yake yi wa kowa, don zan iya zuwa da abin da kai kanka idan ka ji ma, ba za ka ɗauka ko tunanina ne ba.

To, ka ga irin haka na faruwa domin idan na yi misali da aminaina guda biyu wato Aminu ALAN WaƘa da Adamu Zango, da mafi yawancin masu sauraren waƘoƘin ALA suna tunanin ko za su ga wani tsoho ne saboda kalaman da yake faɗa sun girmi shekarun shi, sai dai an yi amfani da kayan kiɗa na zamani don Ƙawata waƘar.

GTK: A matsayinka na mawaƘi kuma furodusa, waɗanne irin nasarori ne ka samu ta fannin wannan harkar da ka tsinci kanka a ciki a halin yanzu?

El-Mu’az: Eh! Akwai nasarori da dama da na samu domin idan aka cire ɗaukaka ta sanin mutane, wata harka ce wacce za ta sa a sanka wanda a wani wajen za ta ja maka farin jini, a wani wajen kuma ta ja maka baƘin jini, saboda wannan harkar tana da Ƙalubale iri-iri, domin wani idan ya ga ka yi wani abu a cikin shirin fim, sai ya tsane ka har abada.

Hakazalika, wani kuma ko a waƘa ya ji ka faɗi wani abin da ya yi kama da halinsa, sai ya kira ka ya zage ka ko ya kira ka ya yaba maka don sun gamsar da shi, saboda akwai wata waƘa da muka yi da Adam Zango wato Gumbar Dutse da wasu suka ga kamar da su muke, don sun auna waƘar ya yi daidai da halinsu da har suka zo suka faɗi waɗansu maganganu bayan ba su san lokacin da muka rubuta waƘar ba, ba mu yi tunaninsu a rai ba, illa mun yi amfani da tunaninmu ne kawai.

To, haka harkar take don haka nasarorin da na samu bayan sanin jama’a na samu abubuwa da dama ta hanyar yi min kyaututtuka da dama a kan na waƘe wani ko wasu ko wata don cancanta, saboda haka akwai nasarori da Ƙalubale a tattare da yin harkar wanda inda an biye wa Ƙalubalen, da yanzu babu kowa a cikin harkar.

GTK: Shin a yanzu kana da wani sutudiyo naka na kanka da ka buɗe ko kuwa kana aiki tare da wasu ne?

El-Mu’az: Eh, to! A halin yanzu, ba ni da wani sutudiyo nawa na kaina, ina aiki ne tare da wasu domin na fi yin aiki a Hannun Dama sutudiyo da wani Kajat sutudiyo da ke Kakuri, amma sai dai ni yanzu da nake da niyyar buɗe nawa sutudiyon na kaina, nan bada daɗewa ba.

Kuma ina nan ina ta tanadin kayan na’urori na zamani da zan riƘa amfani da shi a madadin in riƘa zuwa wajen wasu ina yin aiki na, wanda yake sai dai wasu su riƘa zuwa waje na don yin aikin rekodin nasu, domin zan inganta sutudiyon matuƘa.

GTK: Wace shawara ko kira ka ke da shi ga sauran ‘yan uwanka mawaƘa da ‘yan wasan Hausa masu yin shirin fim ɗin Hausa?

El-Mu’az: Shawarar da zan ba ‘yan uwana mawaƘa bai wuce in ce su lura daɗin waƘa ko basirar waƘa ba ta gushewa matuƘar Allah Ya riga ya yi maka baiwa, amma bayan kwana biyu sai ka ji an riga an daina sauraren waƘar, to, wannan ya biyo baya ne a sakamakon duk an raja’a wajen waƘe abu ɗaya.

MawaƘanmu duk sun raja’a a kan waƘe-waƘen soyayya kawai, kuma kowane lokaci soyayya idan ana ɗaukar al’amura na rayuwa ana yin waƘa a kai kamar an yi yaƘi ka waƘe mutanen, irin halin rayuwa da ake ciki a yanzu na zalunci da shugabanni ke yi, domin waƘa hanya ce ta isar da saƘwanni wanda Ƙila sai bayan ba ran mawaƘin za a tuna da shi idan aka ji waƘar.

Misali, kwanan nan Aminu ALA ya yi wata waƘa da yake kira ga gwamnoni da su daina naɗin ciyamomi, wanda har wani gwamna da ya ji waƘar ya aika gidan rediyon Libati a kan su ci gaba da saka wannan waƘar, domin duk gwamnonin da ba su ji ba, su ji.

Don haka ina ba mawaƘanmu shawara da su riƘa amfani da abubuwan da ke faruwa da rayuwar jama’a a zamanin nan don yin waƘarsu, ba wai a ce kullum ba su da wani aiki sai waƘar soyayya, saboda waƘoƘin faɗaƘarwa sun fi amfani ga rayuwar jama’a ko al’umma.

Hakazalika ‘yan fim ɗin Hausa, ina mai ba su shawarar duk abin da suke so su yi, su yi shi don Allah domin babu wanda zai tsaya masu sai Allah a nan duniya da can lahira, saboda a harkar fim babu wata matsala irin maganganu da tsegumi marasa amfani da suke yi, wanda idan za su Ƙaurace masu, aka zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, aka haɗa kai, to, babu shakka nasarar da duk suke tunani a rayuwa za a samu, to, sai ana wuce nan idan kansu a haɗe yake.

Domin duk ranar da gwamnati ta farka ta shiga cikin harkar fim ɗin Hausa, to babu shakka harkar za ta faɗaɗa fiye da yadda ba sa zato, inda duk wanda bai shiga cikin harkar ba ya zo yana ƘoƘarin shiga cikin harkar amma shigar ya zo ya zama mai aiki, kana duk waɗanda suke ciki kuma su zo su samu ɗaukakar da basa tsammani a rayuwa fiye da zatonsu.

GTK: Daga Ƙarshe, wanesaƘo ka ke da shi ga masoyan ka na gida masu kallon ku da sauraren ka a kodayaushe?

El-Mu’az: SaƘon da nake da shi ga masoya da ‘yan uwa bai wuce fatar alheri ba, musamman ga iyalai domin mutumin da aka ce ya shiga wannan harka ta sana’ar waƘa ko harkar yin fim ɗin Hausa musamman, to, babu wani babban mutumin da zai haƘuri da shi irin iyalansa.

Saboda Ƙarancin lokacin da mutuma zai ba iyalansa domin wani lokacin ma cikin dare za a zo a kira shi, ya tashi ya tafi sutudiyo domin yin wani aikin. Kana da rana ma babu wani Ƙa’idadden lokacin da mutum ke da shi saboda harkar rekodin ko zuwa yin aikin shirin fim ɗin.

To, duk ire-iren waɗannan hali da mutum ke shiga ko yake ciki, iyalansa ne ake bari cikin tararrabi ko in ce tashin hankalin auna rayuwar sa da ake yi a kodayaushe, don za ka ji an ce yau mutum yana wannan gari wajen shirin fim, gobe ka ji an ce yana wancan garin, an jima Ƙila ka iya jin an ce yana wani wajen na daban wajen yin aikin shirin fim ɗin.

Saboda haka, ina miƘa godiya ta ga magoya baya na da masoya na da ke cikin wannan harkar da iyalanmu da ‘yan uwanmu, kana ina kuma Ƙara roƘon alfarmar Ƙara haƘuri da mu a duk irin halin da suka same mu ko suka tsince mu a ciki, kana ina roƘon jama’a da su riƘa yi mana fatar alheri da kyakkyawan zato ko zargi na alheri a kodayaushe, na gode.

GTK: To, Malam El-Mu’az mun gode da ba mu lokacin ka da ka yi.

El-Mu’az: Ni ma na gode, kuma na ji daɗi Ƙwarai da gaske.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here