Kanbura’uba!!!

0
1818

wanibawanAllahne ke dakuɗi Naira ɗari biyar da ashirin a aljihunsa, sai ya ga wani almajiri yana bara, sai ya kira shi ya ciro kuɗin aljihunsa da niyyar zai ba shi sadakar Naira ashirin ɗin da ke cikin aljihunsa.

Bawan Allah nan da ya ciro kuɗin da zai ba almajirin sai bai duba ba, ashe ya yi kuskure ya ba shi wannan Naira ɗari biyar ɗin da ke aljihunsa, kawai sai ya fita batunsa har almajirin ya wuce.

Sai da aka zo yin salla a cikin sahu a masallaci, bayan an yi ruƘu’u, sai sauran kuɗin Naira ashirin da ke aljihunsa ya faɗo, ganin haka bai san lokacin da ya ce Kanbura’uba ba.

 

Mun samu wannan labari daga

 

Ibrahim Sabo Abdullahi

GSM: 08033418795

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here