masu hikima sun ce

0
1375

AKASIN malami almajiri, su ne masu tsoron Allah da yi masa biyayya, kuma akasin masani da jahili, ba dole ne a same su masu biyayya ga Allah ba, kamar yadda ba dole ne a sami malami ko almajiri da ilimi mai yawa ba.

Kamar yadda ka san da wuya mutum bai yi barci ba cikin awoyi ashirin da huɗu (24) haka da wuya Allah bai jarrabe shi da halin rayuwa na daɗi ko na wuya, na so ko na Ƙi, na farin ciki ko na baƘin ciki ba.

Inda za ka san mutane sun yi nisa a cikin son duniya ba lahira ba shi ne, hatta malamai masu ilimi da koyarwa, masu kira a bi Allah a ji tsoronSa a yi koyi da manzonSa, yau su ne ke ɗibar abin da suke so na hukunce-hukunce na daga falalar da Allah Ya yi ga wasu bayinSa da suka shuɗe waɗanda ko sanin sunansu bai yi ba, gado; domin su ilimantar, amma idan su na yanzu suka sami ikon ɗiba su wallafa, sai su katange wasu, wai ba su yarda wani ya kwafa ba sai da neman yardar su, amma su sun kwafa ba a hana su ba!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here