“Kowa zan bai da ilimi da shi da jaki mi ke raba su idan ba zancen rashin bindin nan ba”.
Wannan baitin waƘa ce ta wani mawaƘi mai suna Garba Maitandu Shinkafi, kuma cike take da basira, musamman a kan nuna muhimmancin ilimi ga rayuwar ɗan Adam. MawaƘin ya nuna cewa, duk mara ilimi ɗaya yake da jaki. Jaki kuwa dabba ne da mafi yawancin lokaci akan danganta shi da daƘiƘanci. Idan ko haka ne, ya zamanto wajibi ga duk ɗan Adam ya nemi ilimi ko don rayuwar kansa shi kaɗai, saboda duk mai ilimi ba ya taɓewa komai daɗewa.
Wannan bayani shimfiɗa ce a kan wani yanayi mara kyau da muka tsinci kanmu a wannan jiha ta Kaduna, ko kuma in ce a Ƙasar ma baki ɗaya, amma kuma ya fi shafar jihohin Arewacin Ƙasar nan. Wannan yanayi kuwa shi ne rashin kammala karatu idan an fara.
Mun wayi gari a wannan Ƙasa tamu, matasa da dama sun tsinci kansu a wani hali na ƘaƘa-nika yi a dalilin rashin samun damar kammala karatu, idan sun fara. Wannan al’amari kuwa ya shafi ɗalibai musamman na gaba da firamare da kuma waɗanda suke jami’a ko makarantun Kimiyya da Fasaha ko kuma na koyon malanta.
Wannan matsayi da matasanmu, maza da mata, suka tsinci kansu yana da illoli da dama. Na farko dai yana sa irin waɗannan rukunin matasa a wani hali na tsaka mai wuya na rashin samun aikin yi. Kuma kowace shekara ana yaye ɗalibai dubu mafi rinjaye daga cikinsu na rasa aikin yi duk da Ƙwazon da wasu daga cikinsu suka nuna kuma aka ga hakan a satifiket ɗinsu. Ashe ke nan wanda bai gama karatu ba sai ya fitar da tsammanin more rayuwa ta hanyar samun ilimin zamani.
Illa ta biyu kuwa ita ce wadda ta shafi matasa mata. Duk yadda ɗiya mace ta so da samun ilimi sai ya kasance wani dalili ya hana ta kammala karatun. To, a wannan ɓangare namu, wato Arewa, babu abin da iyayenta za su yi tunani illa su aurar da ita ko tana so ko ba ta so. Wasu su amince, idan kuma sun yi dacen miji ma’abucin ilimi, sai ya ɗauki nauyinta, har sai ta kammala ilimin a gidansa. Wata ko idan ta cije a kan ba za ta yi aure ba a wannan lokaci, sai ta sami saɓani da iyayenta har ya kai ta shiga wani mummunan hali na fasiƘanci, don kawai ta nema wa kanta kuɗin da za ta ci gaba da makaranta. A irin wannan hali ne ɗiya mace kan kamu da cututtukan zamani irin su Sida ko Ƙanjamau. Ka ga ke nan garin neman Ƙiba an samo rama.
Wata illar kuma da ta shafi rashin kammala karatu ga matasa ita ce faɗawa cikin mugun hali na shaye-shaye, ko fashi da makami da dai sauran mugun alkaba’irai da za su nesanta matashi cikin al’umma tagari.
Duk irin waɗannan jinsi na matasa da suka tsinci kansu a mummunan hali saboda rashin kammala makaranta suna nan birjik a Jihar Kaduna kamar sauran jihohi.
Yanzu kuma sai mu waiwayi dalilan da suke janyo rashin kammala makaranta ga ɗalibanmu. Bincike dai ya nuna irin waɗannan ɗalibai sun haɗa da taurin kan matashi da zuga irin ta abokai da kuma uwa uba talauci.
Bari in fara da talauci. Sanin kowa ne dai talauci mugun ciwo ne, kuma rashin ilimi ne ya sanya mutum cikin talauci, kuma talauci na iya sa wa mutum mutuwar zuci ko raunin imani har ya rungumi mugun halin da zai iya kai shi ga halaka. Matasa da dama waɗanda suka bar makaranta ba tare da sun kammala ba, akasari hakan na faruwa ne saboda rashin biyan kuɗin makaranta wanda ya fi Ƙarfin iyayensu. Hakan kuma kan faru ne a kowane mataki. Misali, sai ka ga yaro ko yarinya ta sami zuwa makarantar gaba da firamare amma kuɗin rajista ya gagari iyayenta.
Na sha yin magana da wasu iyaye da suke nuna takaicinsu na rashin iya biyan kuɗin rajista da za su sanya yaransu a makaranta. Malam Umar mai gyaran takalmi, wani mutum ne da yake sha’awar yaransa su yi karatu sai dai kuma ba shi da Ƙarfin da zai iya biya masu kuɗin makaranta don a yadda ya faɗa mini, ya ce “ina da yara tara, yanzu haka biyu sun gama sakandare, uku na kai, amma akwai guda biyu da ya kamata in sanya su a Ƙaramar sakandare tun da sun gama firamare, amma ba zan iya ba saboda kuɗin sun fi Ƙarfina, tun da aƘalla ina buƘatar Naira dubu 15, kuma ban da wannan dukanci babu wata sana’ar da nake yi, sai noma ɗan kaɗan idan damina ta sauka”.
Ga Malam Umar Baduku, babu yadda zai yi babu kuma inda za shi, ma’ana Ƙarshen makarantar yaran nan biyu, shi ne a firanmare tun da babu kuɗin rajista da za a biya masu don su ci gaba da zuwa makaranta. Allah kaɗai ya san ire-iren su, Malam Umar Baduku, a wannan jiha tamu. Ashe ke nan talauci ba Ƙaramin illa yake yi wa ci gaban ilimi ba.
Kamar yadda na ce a baya, ana iya samun irin wannan matsala a kowane fanni na karatu. Ma’ana ɗalibi na iya barin makaranta koda yana farkon karatu ne, ko tsakiya ko a daidai lokacin da zai yi jarrabawar barin makaranta, sai rashin kuɗin jarrabawa ya hana ɗalibi kammala karatu.
Wani dalili kuma da ke daƘile ci gaban karatun matasa shi ne “taurin kai”. Ma’ana a nan shi ne, akan sami yaran da iyayensu masu kuɗi ne, amma kuma sai taurin kai da kunnen Ƙashi ya hana su kammala makaranta. Irin waɗannan yara sun sami duk wani galihu na tafiyar da rayuwarsu a bisa kyakkyawan tafarki na yin makaranta, ko a Ƙasashen waje ne za a iya kai su, amma sai su gwammace kiɗa da karatu. Su ne za su shiga aikata miyagun ayyuka idan an tura su makaranta, kamar shaye-shayen miyagun Ƙwayoyi da neman mata, musamman ganin cewa, an ba su kuɗi masu yawa, sai su shiga sharholiya. Daga nan makarantar ta gagara ke nan daga baya su zama alaƘaƘai ga iyayensu har ma ga al’umma gaba ɗaya.
Har ila yau, akan sami matasa da ke sauraron ’yan uwansu matasa da suka Ƙi makaranta suka zaɓi hanyar lalacewa ko taɓarɓarewa ta fuskar rayuwa. Tun farko irin waɗannan matasa da ma sukan haɗu ne a makaranta ko kuma su haɗu da matasa ’yan uwansu da suka daɗe da guje wa karatu suka zaɓi harkar banza kamar yin sata da shan miyagun Ƙwayoyi.
A duk waɗannan dalilai da na zayyana kuma na yi bayani a kai, wanda ya fi addabar al’umma shi ne na talauci. Saboda gaskiyar al’amari shi ne matalauta sun fi yawa a Ƙasar nan, kuma ’ya’yan talakawa sun fi yawa, kuma su ne suka fi yawa a cikin yara matasa da kammala makaranta ke gagararsu. Kuma sakamakon haka yake Ƙara yawan matasa masu sana’ar banza a nan Kaduna da sauran jihohi.
Babban abin tambaya a nan ita ce, wace hanya ko matakai gwamnati ya kamata ta ɗauka don yunƘurin kawo Ƙarshen wannan mummunan lamari da ke barazana ga manyanmu na gobe?
Ya zamanto dole a yaba wa gwamnan Jihar Kaduna, Akitek Namadi Sambo, a kan wasu matakai da ya ɗauka don gyara harkar ilimi a wannan jiha ta Kaduna.
A karon farko tun da aka ƘirƘiro jihohi a Ƙasar nan, gwamnatin Namadi Sambo ce ta fara aiwatar da Ƙudurin nan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi na cewa, Ƙasashe su bayar da kashi 26 na cikin kasafin kuɗinsu don raya ko ci gaban ilimi. Babu mamaki a dalilin haka ne da hawansa karagar mulki ya Ƙara kashi 5 na albashin malamai. Wani ƘoƘari da gwamnan ya yi don taimakon yara da ma iyayensu shi ne, bayar da tufafin makaranta kyauta ga yaran firamare da ma hana biyan ko kwabo da sunan kuɗin makaranta a makarantun firamare.
Amma kuma duk da wannan ƘoƘari na Gwamna Namadi, akwai sauran rina a kaba, muddin ana son yaro ko yarinya ta fara karatu sai ta dire, to, dole ne gwamnati ta Ƙara himmatuwa na ɗaukar Ƙarin matakai. Misali, ya dace gwamnati ta isar da taimakonta wajen tallafa wa ’yan makarantar gaba da firamare musamman ta fuskar yi wa yaro rajista idan zai shiga sakandare, da kuma ɗauke wa ɗalibi biyan kuɗin jarrabawa, idan za a ɗauki jarrabawar fita sakandare.
Idan kuma an ga cewar hakan zai gagara, to, wajibi ne a ɗauki aƘalla kashi 80 cikin 100 na waɗannan kuɗaɗe a matsayin tallafi, haka idan an yi, zai taimaka wa yara masu hazaƘa da iyaye da kuma al’umma a sami kwanciyar hankali, ita kuma gwamnati ta sami yabo da sam-barka a wajen al’ummar da suka zaɓe ta, don su ma sun lasa romon dimokuraɗiyya.