Yajin Aikin Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Ya Shafi Harkokin Kasuwanci — Alhaji Umar

0
8204

Isah Ahmed, Daga Jos

SHUGABAN ‘yan kasuwar Ƙaramar hukumar Jos ta Arewa da ke Jahar Filato, Alhaji Yakubu Abdullahi Umar ya bayyana cewa babu shakka yajin aikin da ma’aikatan Ƙananan hukumomin jahar ke yi a halin yanzu ya shafi harkokin kasuwanci.

Alhaji Yakubu Abdullahi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ci gaba da cewa, a yanzu harkokin kasuwanci sun tsaya cik a garin Jos da sauran Ƙananan hukumomin jahar sakamakon yajin aikin don haka ‘yan kasuwa suna cikin mawuyacin hali.

Ya ce da ma idan aka biya ma’aikata albashinsu sukan zo su sayi abinci da sauran kayayyakin buƘatu, amma  a yanzu  ‘yan kasuwa ba sa ganin ma’aikatan saboda wannan matsala.

Ya yi kira ga gwamnatin Jahar Filato ta tausaya ta biya wa ma’aikatan Ƙananan hukumomin Jahar Filato buƘatunsu, don a kawo Ƙarshen wannan matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here