1.Bismillahi mai rahma,
Salatin ka ga mai girma,
Muhammadu Ɗaha ja rahama,
A duniya har Ƙiyama ma,
Mai son mu yi zamantare.
- Shimfiɗa ɗaya za mu zauna
Ni da kai zo nan mu zauna
In da ke zo nan mu zauna
In da ku ma zo mu zauna
Tabarmar ta mu ce tare.
- Ɗaki ɗaya ne fa namu
Ga gadaje nan fa namu
Shimfiɗu ne muka samu
Babu komi kar mu damu
Sai mu kwana abin mu tare.
- Kar ka hau mini kai in hauka
Ba ka Ƙi na ba ni Ƙinka
In gida na ɗaya da naka
Ga shiyya na ga shiyyarka
Sai mu gyara gidanmu tare.
- Mun haɗe kuma unguwarmu
Ga gida na ko gidanmu
Ga gidan wasu naku namu
Ga iyakokin gidanmu
Duk da naku muna fa tare.
- Rugga na ɗaya da naka
Ga bukka na da naka
Inda shanu na da naka
Ga iyali na da naka
Mu yi zama mai kyau fa tare.
- Ƙauye na ɗaya da naka
Karkara na ɗaya da naka
Ko gari na ɗaya da naka
Kai ka sanni ko na sanka
Sai mu so junanmu tare.
- Mazaɓa, Ƙaramar hukuma
Ko jaha ɗaya muka sama
Ko Ƙasa sai mu yi ta himma
Ci gabanmu da nata har ma
Masu son mu muna fa tare.
- In uwa ɗaya muka samu
In uba ɗaya muka samu
Mallami ɗaya muka samu
Shugaba ɗaya muka samu
Ba na biyu a gare su tare.
- Kowanensu mu girmama shi
Kar mu yarda a banzata shi
Yadda duk Allah Ya yi shi
Inda samu ko rashin shi
Inda shi ko ba a tare.
- In addini guda ne
Haka in yare guda ne
Ko jam’iyya guda ne
Yanki sana’a guda ne
Ko ba haka ga mu tare.
- Kasuwa ɗaya ce fa tamu
Ko wurin aikin ga namu
Asibiti gun maganinmu
Haka na rafin ga namu
Rijiya ce tamu tare.
- Kowane Allah ya ba mu
Za mu amfana dukkanmu
Shi ya ba mu Ya ko haɗa mu
Mu kula su da kyau dukkanmu
Namu ne an ba mu tare.
- Mata da miji kowa da nashi
‘Ya’ya kuma kowa da nashi
Sutura kowa da nashi
Samu kowa da nashi
Duniya kuma ga mu tare.
- Addini kowa da nashi
Yare kowa da nashi
Hali kowa da nashi
Ƙira kowa da nashi
Allah ya haɗa mu tare.
- Duk abin da Ya haɗa mu
Ya fi abin da zai raba mu
Haka nan kuma me gina mu
Ya fi me rusa gininmu
Wanda be son ga mu tare.
- Makaranta ce fa tamu
Sannan ga Mallamanmu
Komi ke ciki an fa ba mu
Babu bambanci ajinmu
HaƘuri za mu yi fa tare.
- Allah ɗaya ne Ya yi mu
Allah ɗaya ne Ya sanmu
Allah ɗaya ne Ya ba mu
Allah ɗaya ke haɗa mu
Koda mun so mu ware.
- Allah ɗaya ke rabawa
Shi ne kuma ke haɗau
Shi ne me komi da kowa
Shi ne me baiwa bawa
Addini da wuri da yare.
- Komi Allah Ya zaɓa
Shi ne bawa ya zaɓa
Hanya mai kyau ka zaɓa
In mummuna ka zaɓa
Sai Ya so ka gane ku tare.
- Duk abin da ya ba ku tare
Ku haɗe a cikinsa tare
Inda Annabi ga ku tare
Inda shaiɗan ga ku tare
Inda yatsu in kutare.
- In makahi in guragu
Masu ji bebe da shegu
Ko ka yarda ko ka tsargu
Ga na kirki ga miyagu
Ya haɗa ku, ku ci shi tare.
- Lafiya ita za ka nema
Da zama a cikinta nema
Kar ka yarda da masu ce ma
Ka ji tsoro don ka koma
Gun tsiya ko sare-sare.
- Kar ka je inda za a jima
In ka ɗauki fansa a ɗau ma
Kiyayi iyaye, ‘yan uwa ma
Da nashi da naka yana isar ma
Addu’a mai kyawu dai tsare.
- Allahu ke haɗawa a wuri ɗaya
Waɗansu ya haɗa su a duniya ɗaya
Waɗansu ya haɗa su cikin Ƙasa ɗaya
Waɗansu ya haɗa su a ɓangare ɗaya
Waɗansu ya haɗa su, su yi zamansu tare.
- Waɗansu ya haɗa su a tare ɗaya
Waɗansu ya haɗa su ba su gu ɗaya
Waɗansu ya haɗa su sana’a ɗaya
Waɗansu ya haɗa su da bauta ɗaya
Waɗansu ya haɗa su daban-daban a tare.
- Waɗansu ya haɗa su zamansu lafiya
Waɗansu an haɗa su suna ta yin tsiya
Waɗansu an raba su sun sami lafiya
Waɗansu an raba su suna hayaniya
Waɗanda ke da haƘuri suna zamansu tare.
- Ki ce da ni ban amince da ke ba
Ashe be fi in ce ke ɓarauniya ba
Ka ce ban amince da kayanka ba
Ashe be fi in ce ka cuce ni ba
Duka suna gudana a kan zamanmu tare.
- Cewa ban amince ma da ɗaki ba
Ashe be fi in ce kai ka ɗauka ba
Ka ce ban amince ma rumfarmu ba
Ashe be fi in ce kai ka ɗiba ba
Ba ka jin ana wannan sai zamana tare.
- Azzalumi yake sa mutum yin fushi
Ya taso masa in ya cutar da shi
Kana kwance ka bar tashi da shi
In tsaye ne zauna ko ka kwanta da shi
Sababbin haka ai sai zaman tare.
- Me ramuwa ya Ƙara azzalumi
Wanda ko ya rama daidai hakimi
Wanda ko ya yafe babban malami
Wanda duk ya ɓoye shaida azzalumi
In ana zaman tare a daina tsumbure.
Mu Kwana Nan