Muhammad Sani Chinade, Daga Damaturu
GWAMNATIN Jahar Yobe na ƘoƘarin shawo kan manyan matsalolin da ke haddasa rikice-rikicen da ake samu a duk shekara a tsakanin manoma da makiyaya wanda ke haifar da rasa rayuka da dukiyoyin jama’a daga ɓangarorin biyu.
A kan haka ne gwamnatin Jahar ta Yobe ta shirya wani taron fahimtar juna a tsakanin manoma da makiyaya ‘yan asalin jahar da ma makiyayan da ke zuwa daga jahohin maƘwabta haɗe da makiyaya ‘yan Ƙasa da aka fi sani da suna sulluɓawa don ganin an kawo sa-toka-sa-katsin da ke tasowa a tsakaninsu a duk shekara.
A taron sasantawa da gwamnatin ta shirya wanda aka yi a garin Damaturu tsakanin ɓangarorin biyu don fahimtar juna, gwamnatin ta gayyato shugabannin Ƙungiyar makiyaya ta Ƙasa reshen Jahar Yobe da na shugabannin Ƙungiyar makiyaya ‘yan Ƙasa wato sulluɓawa da suka fito daga jahohin Zamfara, Sakkwato da Kebbi, inda suka gudanar da tattaunawarsu domin shawo kan rikicin da ake samu tsakaninsu da manoman jahar.
Da ya ke gabatar da jawabinsa wajen taron na sasantawa, Kwamishinan ma’aikatar bunƘasa kiwon dabbobi da kamun kifi na jahar, Alhaji Idris Machina ya bayyana maƘasudin shirya wannan taro da cewar, an shirya taron ne domin ƘoƘarin shawo kan yamutsin da a duk shekara ake samu tsakanin manoma da makiyaya wanda a mafi yawan lokaci kan haddasa mummunan yanayin da ke jawo rasa rayukan jama’a da asarar dukiyoyi daga dukkan ɓangarorin biyu, wani lokaci har ma da na jami’an tsaro wanda kuwa hakan babbar asara ne ga jahar da ma Ƙasa baki ɗaya.
Kwamishinan ya Ƙara da cewar, kan hakan ne gwamnati ta ga ya dace da ta shirya wannan taro don ganin an samo bakin zaren magance ire-iren wannan rikici da ya Ƙi ci ya Ƙi cinyewa da ke kawo tarnaƘi ga harkokin ci gaban noma da kiwo a jahar kasancewar mafi yawan al’ummarta da ma na arewacin Ƙasar manoma ne kuma makiyaya inda kuwa kowa ya san irin rawar da noma da kiwo kan taka wajen ciyar da tattalin arziƘin Ƙasa gaba.
Da wakilinmu ke tuntuɓar wani Ƙusa a Ƙungiyar ta makiyaya a Jahar Yobe, Malam Muhammad Khalil a kan ko mene ne fatarsu bisa ga wannan taro nasu? Sai ya amsa da cewar, su fatar su shi ne a sami maslaha tsakaninsu da ‘yan uwansu manoma kasancewar manoma da makiyaya tamkar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai don haka ya zama wajibi a samo bakin zaren sasanta wannan taƘaddama da ta daɗe tana kawo tsaiko tsakaninsu da manoma.
A Ƙarshen zaman dai dukkannin ɓangarorin sun amince da mutunta juna ta wajen kula da haƘƘoƘin juna’in inda ta ɓangaren manoma za su riƘa kauce wa noma a kan burtalolin da dabbobin makiyaya ke bi don zuwa kiwo, mashayar ruwa da kuma Ƙaura, tare da ɗebe amfanin gonarsu a kan lokaci, yadda za su sami damar gudanar da kiwonsu ba tare da sun yi masu ɓarna ba, inda su kuma makiyayan za su kauce wa ɓarnata amfanin gonar da manoman kan noma wato manoman rani ko na damina. Kasancewar hakan ne ke haddasa rikicin da ake samu a tsakaninsu.