Mutane 9 Sun Mutu A Taho-Mu-Gama Tsakanin Jami’an Tsaro Da ’Yan Bindiga A Azare

0
1388

Umar Saye, Daga Bauci

Mutane 9 da suka haɗa da soja biyu da ɗan sanda ɗaya da wasu mutune biyu da kuma wasu ‘yan bindiga guda huɗu suka rasa rayukansu sakamakon taho mu gama da aka yi da juna ranar Lahadin da ta gabata a garin Azare da ke Jahar Bauci.

Al’amarin ya auku ne a yayin da ake cin kasuwar riɗi da ke garin na Azare, inda da rana tsaka wasu ‘yan bindiga huɗu suka shiga cikin kasuwar suka kama harbe-harbe suka karɓe kuɗaɗe masu tarin yawa suka ara cikin na kare. Amma ba tare da ɓata lokaci ba dubban mutanen da ke kasuwar sai suka rufa a bayansu da babura da motoci wasu kuma da Ƙafa inda aka musu Ƙofar rago suka rasa matsera har zuwa lokacin da jami’an tsaro suka kawo ɗauki aka kashe mutane uku daga cikin maharan.

Mahari na huɗu ya shiga cikin wani gida ne inda ya yi garkuwa da mutanen gidan ya hau kan bishiya yana harba bindiga a lokacin da jami’an tsaro ke ƘoƘarin fasa garun gidan domin su cim masa, har ta kai ga ya samu nasarar harbin sojoji biyu da ɗan sanda ɗaya da farin kaya guda biyu inda aka samu jimilar mutuwar mutane 9 nan take da kuma raunata wasu kafin aka cim masa aka harbe shi a hannu aka kama shi da rai, amma nan take jami’an tsaron suka kwantar da shi suka kashe.

Kafin aukuwar wannan lamari da kwanaki biyu, saida aka kai wani hari a garin na azare inda aka kashe wani basarake mai suna Alhaji Ibrahim Arab, Majidaɗin Katagum bayan ya dawo daga masallaci da magariba. Kuma kafin wannan an kai irin wannan hari an kashe Jarman Katagum, Alhaji Ibrahim Mohammed da kuma wani hari da aka kai gidan tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Alhaji  Aminu Saleh da ba a same shi ba aka kashe ‘yan sanda biyu a gidansa. Ba a jima ba aka sake kai irin wannan hari aka kashe wasu sojoji biyu a wani gidan mai, yayin da suke kalacin dare.

Irin kisan gillar da ake yi a garin na Azare ya sa mutane yin shahadar Ƙunar baƘin wake kan waɗannan ‘yan ta’adda lamarin da ya kai ga samun nasara kan su musamman ganin yadda wannan ta’addanci ya fara mayar da garin na Azare baya saboda yadda ake yawan kashe mutane a duk lokacin da ‘yan ta’addar suka kai hari.

Bayan aukuwar lamarin wakilinmu ya nemi jin ta bakin kwamishinan ‘yan sanda na Jahar Bauci, Mohammed Ladan amma ya Ƙi cewa komai kan lamarin sai ko ya tabbatar da aukuwar kai wannan hari tare da bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike kan abin da ya faru sai nan gaba za su yi bayani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here