Umar Saye, Daga Bauci
Mutane dubu 11 ke karɓar magani a cibiyoyin dubawa da bayar da magunguna 64 da ake da su a Jahar Bauci.
Shugaban hukumar yaƘi da zazzaɓin maleriya da tarin fuka da kuturta da cutar sida ta Jahar Bauci (BACATMA), Dokta Mohammed Sambo Liman, ne ya bayyana haka a lokacin bikin ranar cutar Sida ta majalisar ɗinkin duniya wanda ya gudana ranar ɗaya ga watan Nuwamba a Bauci.
Ya ce majalisar ɗinkin duniya ta ware wannan rana a matsayin ranar tunawa da masu ɗauke da wannan cuta ta sida (HIV/AIDS) a duniya saboda aƘalla sama da mutane dubu 215 suke mutuwa duk shekara kuma yara miliyan biyu kan zama marayu sakamakon cutar. Don haka gwamnatin Jahar Bauci da taimakon Ƙungiyoyin Ƙasa da Ƙasa sun samar da manyan cibiyoyi 12 da kuma wasu Ƙananan guda 64 da suke samar da magunguna kyauta ga masu ɗauke da cutar. Kuma bikin na bana takensa shi ne yaƘi na nuna Ƙyama da Ƙuntatawa ko wariya tare da wayar da kan jama’a game da wannan cutar.
Dokta Sambo Liman ya ce mutane miliyan uku suka kamu da cutar sida wacce aka fi sani da sida kuma tuni sama da mutane dubu 200 sun riga mu gidan gaskiya a Najeriya cikin wannan shekarar 2011 kurum. Ya ce kashi 80 cikin ɗari na wannan cuta ana kamuwa da shi ne ta hanyar jima’i, kuma sakamakon wayar da kan jama’a da ake yi cutar ta ragu daga kashi 6.8 zuwa 2.0 a shekarar 2012.
Daga Ƙarshe, ya yaba da irin gudunmawar da gwamnatin tarayya da Ƙungiyoyi masu zaman kansu na Ƙasa da Ƙasa da ‘yan jaridu da sauran waɗanda suke taimakawa wajen yaƘar wannan cuta suke bayarwa. Don haka ya shawarci mutane su riƘa gwaɗi kafin aure kuma su riƘa tsayawa ga iyalansu tare da yin taka tsan-tsan game da hanyoyin da ake kamuwa da cutar.