Taron Arewa Zai Lalubo Hanyoyin Ci Gaban Yankin — Bugaje

0
1096

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI, Daga Kaduna

BABBAN burinmu a ‘yancin arewacin Najeriya shi ne samar da kyakkyawan yanayin da zai amfani kowa musamman ta fuskar albarkatun Ƙasar da Allah ya hore wa yankin.

Waɗannan kalamai ne ke fitowa daga cikin mafi yawan mahalarta taron lalubo hanyoyin da za a yi amfani da su domin ciyar da yankin gaba.

Alhaji Usman Bugaje ya ce duk da cewa, akwai ainihin Ƙungiyoyi daban-daban da ke aiki domin lalubo hanyoyin ci gaban arewa lallai yana da kyau a haɗa hannu waje ɗaya ta yadda kwalliya za ta biya kuɗin sabulu.

“Babbar manufar wannan taro shi ne a samu a haɗa hannu domin lalubo hanyar ci gaban yankin da Ƙasa baki ɗaya, saboda da akwai waɗansu sauran Ƙungiyoyin da ke aiki domin samun nasara, don haka za mu haɗa kai wuri ɗaya ta yadda za a sami ingantaccen canji mai ma’ana da zai haifar da canji mai ma’ana.

Ya ce kamar yadda kowa ya san matsalar shi ne ba wai wani al’amari ne da mutum ɗaya ko biyu za su iya warware ta ba, don haka ne wannan taron ya sha bamban da sauran tarurruka da suka gudana a yankin.

Saboda a wannan karon, za a samar da ainihin hanyar tsarin gudanar da aiki domin ci gaban arewa baki ɗaya. Kodayake da akwai irin buƘatu na Ƙungiyar ACF da Ƙugiyar gwamnonin arewacin Najeriya.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, ɗaya daga cikin mahalarta taron da ya fito daga ma’aikatar wayar da kan manoma da kuma gudanar da bincike (NAERLS) ta Zariya, ya ce yankin na arewa wani wuri ne mai ɗimbin arziƘin gaske musamman ta fuskar noma don haka yake buƘatar shugabanni domin aiwatar da lamarin.

“Koda batun tsaron da yankin ke fama da shi duk wani al’amari ne da ke buƘatar kowa ya bayar da gudunmawarsa”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here