JABIRU A HASSAN, Daga Kano
ZA a yi wa mutane miliyan 8 allurar rigakafin cutar sanƘarau a Jahar Kano wadda aka fara daga ranar 1 ga wannan wata na Disamba a faɗin jahar.
Jami\’in hulɗa da jama\’a na ma\’aikatar lafiya ta jahar, Malam Isma\’il Gwammaja ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Juma\’ar da ta gabata.
Sanarwar ta Ƙara da cewa, za a ci gaba da gudanar da wannan allura ta rigakafi a gidajen hakimai da dagatai da hedikwatocin Ƙananan hukumomi, kana su Ƙananan hukumomin za su ci gaba da bayar da dukkan tallafin da shirin ke buƘata a yankunansu.
Sannan ana yi wa yara waɗanda shekarunsu ya kama daga 1 zuwa 29, kana kwanaki 10 za a yi ana gudanar da wannan rigakafi domin tabbatar da ganin an cimma nasarar shirin.
Malam Isma\’il Gwammaja ya bayyana cewa, daraktan shirin allurar rigakafi a matakin farko na ma\’aikatar lafiya ta Jahar Kano, Dokta Nasir Mahmoud ya yi kira ga ɗaukacin al\’ummar Jahar ta Kano da su bai wa wannan shiri cikakken goyon baya wajen kai \’ya\’yansu allurar rigakafin domin cimma manufa.
Wakilin mu ya ziyarci wasu cibiyoyin da ake gudanar da rigakafin inda ya ruwaito cewa, mutane suna kai \’ya\’yansu wajen wannan rigakafin wataƘila hakan ya faru ne bisa yadda aka wayar da kan al\’umma ta hanyoyi masu gamsarwa.
A Ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, wakilin namu ya ziyarci garuruwan Dungurawa da Ƙwa inda ya ruwaito cewa, jami\’an gudanar da allurar rigakafin suna aiki cikin natsuwa da bin al\’amura a hankali ta yadda su kansu yaran suke fahimtar muhimmancin wannan allura.
Haka kuma wasu yaran ma su ne suke gabatar da kansu ba tare da wani ya kai su ba, wanda hakan ta sanya ake ganin cewa, za a iya cimma adadin alƘaluman da ake buƘata a jahar.