Majalisar dokokin Nigeria ta gindaya sharuɗɗan da za ta bi wajen tantance mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya aika domin nada su a matsayin ministoci.
Daya daga cikin sharuɗɗan shi ne cewar duk wanda za a tantance sai ya nuna takardar bayanin dukiyar da ya mallaka.
Mai magana da yawun majalisar dattijan, Sanata Dino Melaye wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, ya kara da cewar dole ne sai sanatoci biyu daga jihar mutum na asali sun amince da shi, kafin majalisar ta amince a nada mutum a matsayin minista.
A ranar Talata, 13 ga watan Oktoba ne, majalisar ta ce za ta soma tantance mutanen.

A makon da ya wuce ne shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dattijai sunayen mutane 21 domin a tantance su kafin, ya nada su a matsayin ministoci.