Da sunanKa Allah
1. Na kira Ka Allah
Da ikonKa Allah
Taimake ni Allah
In kira ga kowa.
- Ina yabon Rasulu
Muhammadu Halilu
Habibu ne Jalilu
A kan dukkan Rasulu
Ka fi bashi baiwa.
- Yadda gare ka Rabbu
Ga Ali har Sahabu
Sa Rahmar ka Rabbu
Ga Tabi’an Sahabu
Da Tabi’ut Tabi’awa.
- Ina kira Musulmi
Da wanda ba Musulmi
Kar mu yi sake da ilimi
Domin sai da ilimi
Ake batun Arewa.
- Nijeirya ga tamu
Idan fa babu ilimi
Sunanta ba ta samu
In mun sake da ilimi
Sunan yana ɓacewa.
- Ni na kira ka ɗanta
Nijeriya uwa ta
In har ka amsa ɗanta
Ko ke ki amsa ‘yarta
Ɗan Kudu ko Arewa.
- Duniya in ka duba
Ɗa kake ko uba
Adamu ne uba
Yarensa ka sa gaba
Da ilimomin Annabawa.
- Yare duka nashi ne
Addinai nashi ne
Yanku duka nashi ne
Maza, mata nashi ne
Uba ɗaya muke har uwa.
- Hauwa’u matarsa ne
‘Ya’ya duka nasu ne
Addini nasu ne
Duniya duka nasu ne
Sai mu rungumi ‘yan uwa.
- Saƙon Allah gare mu
Manzo zai zo gare mu
Allah in zai kira mu
ManzonSa zai kira mu
‘Yan Adamu da Hauwa.
- Bambanci na Jalla
Haka nan ma ƙabila
Domin mu san shi Jalla
Mu san juna jimilla
Sarakai da talakawa.
- Bai yi sai don a bi shi
Bai yi ba don a ƙi shi
Bauta a mayar gare shi
Ya so kuma wani ya ƙi shi
Falala adalci ga kowa.
- Bai wani don ka ƙi shi
Sai in shi ya ƙi shi
Bai wani don ka so shi
Sai in shi ya so shi
Shi kuma ke da kowa.
- Ɗa na bin uban shi
Uba na bi ga ɗan shi
Mata ga miji ta bi shi
Ya yi wata ba ta bin shi
Ya yi komi da kowa.
- Wa da ƙani musali
Mai ilimi da jahili
Ka ga abu ba dalili
Sai sababi da ƙanli
Ba yadda bai iyawa.
- Don haka kama kanka
Bari ta batun wanin ka
Idan ka kama kanka
To, zai kwaikwaye ka
Ya bi ka da taimakawa.
- Mai hidima ga kansa
Ya taimaki ɗan uwansa
Allah mai taimakonsa
Ya taimaki ɗan uwansa
Shi da yake taimakawa.
- Kyaun ɗa ƙarami uwarsa
Yana ɗakin uwarsa
Ya zo ɗakin ubansa
Ya gane shiyar ubansa
Kafin na ƙani da wa.
- Shiya na ƙanin uba
Ko shiya na wan uba
Haka nan na uban uba
Duka ba su kamar uba
Bale fa gidan uwa.
- Dage da biɗan sani
Zaman banza ba sani
Aikin banza ba sani
Kada ku zauna ba sani
Kuna kallon ‘yan uwa.
- Mata kai mata cefane
Gida kai masu cefane
Gari kai masu cefane
Ƙasa kai masu cefane
Yanzu ka zama ɗan uwa.
- Ka ce a yi maka
Can da an maka
Har yanzu ana maka
Sutura har abincinka
Har da ilimi ɗan uwa.
- Tambayi masu yi maka
Ko kake so ya yi maka
Ka ce wa ke maka
In ko ya amsa maka
Sai ka ƙara tunanuwa.
- Sayarwa ba ta kamar saye
Mai sayarwa ga mai saye
Kasuwar birni da ƙauye
In babu ilimi ga mai saye
Wa ke da riba mai sayarwa.
- Mai sayarwa bai da ilimi
Mai saye in yana da ilimi
Shi kan ci riba da ilimi
Komi za ka yi nemi ilimi
In saye ne in sayarwa.
- Ƙwadago ne za a ba ka
Ko a amsa nan gare ka
In ma sana’a gare ka
Koyo koyarwa da ɗanka
Sai da ilimi ɗan Arewa.
- Matuƙin jirgi da mota
Babu cutarwa da sata
Mai niƙan injin da Dokta
Maigini da rufi da fenta
Sai da ilimi ɗan Arewa.
- Kada ka ce ka sami hanya
Ci da sha sutura a duniya
Gida da abin tabiya a hanya
Safe maraice ka kama hanya
Biɗan ilimi maza ɗan Arewa.
- Biɗan ilimi na ƙara buɗi
Ya hana ka ya sa ka ka gane ruɗi
Ka wadatu da shi ko babu kuɗi
Da ilimi mai mulki kan yi harɗi
Ya miƙe ƙafarsa ya tsere kowa.
- Ilimi ke sa a yi karatu
Za ka ga me shi na rubutu.
Bai barin nemansa yana karatu
Ko da an taru gabansa ana karatu
Bai barin ɗaukar ilimi ga kowa.
- Me zai sa kai mai sana’a
Ko mai aiki don jama’a
Da me ƙaramin ilimi ƙana’a
Ka fasa biɗan ilimi da ɗa’a
Kana son ace maka ka fi kowa.
- Daga kullum kada ka fasa
Neman ilimi kada ka ƙosa
Don addini ko kuma ƙasa
Jahilci maƙiyi na nisa
Har kusa shi ne fiye da kowa.
- Ba maƙiyi da ya kai kamarsa
Ko shaiɗani ba ya kai sa
Bale maƙiyanka kusa da nesa
Shi ya sa shaɗan ya hana ka yinsa
Yi karatu Allah ke ta cewa.
- Mafifici Manzonmu Yasin
Ya ce biɗan ilimi ka je Sin
Kafirci nisa suna Sin
Ɗan Saudiyya ya je nema zuwa Sin
Don zaman duniya ga kowa.
Mu Kwana Nan