An Buƙaci ’Ya’yan Ƙungiyar Zaɓi Sonka Su Ci Gaba Da Goyon Bayan Ƙungiyar

0
8132

Muhammad Sani Chinade, Daga Azare

AN kirayi ‘ya’yan ƙungiyar zabi sonka da taimakon juna ta ƙasa reshen Jahar Bauci da su ci gaba da ba da goyon baya dangane da ci gaban ƙungiyar musamman ga sababbin shugabannin ƙungiyar don ciyar da ita gaba.

Wannan kira ya fito ne daga bakin sabon shugaban ƙungiyar na ƙasa reshen Jahar Bauci, Malam Nura Fatara a tattaunawar da suka yi da wakilinmu jim kaɗan da zaɓarsa a matsayin wanda zai jagorancin ƙungiyar a matakin jaha na tsawon shekaru huɗu kamar yadda tsarin mulkin ƙungiyar ya ayyana.

Malam Nura Fatara ya ci gaba da cewar, kasancewar wannan ƙungiya tasu ta jaha ta ɗan sami naƙasu a baya sakamakon rashin tarukka da ƙungiyar ta fuskanta a baya da kuwa babu wata ƙungiya da za ta ci gaba in ba tare da shugabanninta na gudanar da tarurruka ba da nufin samo bakin zaren magance matsalolin ta ɓalle wa ƙungiyar zaɓi sonka wadda dama can ta gaji gudanar da tarukka a kasancewarta ƙungiyar da ta kafu domin sada zumunci.

Don haka ne sabon shugaban ya kirayi dukkan ‘ya’yan ƙungiyar a Jahar Bauci da su ba shi goyon baya don ya sami gudanar da shugabancinsa cikin nasara, kana su yi ƙoƙarin halartar dukkan wani taron da ƙungiyar za ta kira da nufin ciyar da ita gaba tare da kawar da duk wani rashin fahimtar juna da ke tsakani don samo bakin zaren ɗinke duk wata ɓaraka da za ta iya tasowa.

Daga nan sai sabon shugaban ya bada tabbaci ga ‘ya‘yan ƙungiyar cewar, zai yi iya ƙoƙarinsa don ganin a lokacinsa ya yi hoɓɓasan haɗa kan ‘ya’yan ƙungiyar a dukkan sassan Jahar Bauci don ganin an gudu tare an kuma tsira tare kasancewar da ma babbar manufar ƙungiyar shi ne haɗa kai da taimakon juna.

Ya kuma yaba wa tsofaffin shugabannin ƙungiyar dangane da karamcin da suka nuna masa a yayin gudanar da zaɓen kasancewar bai fuskanci wata turjiya ba, daga nan ya neme su da su goya masa baya don kai ƙungiyar ga nasara.

Shugaba Nura Fatara ya kuma hori ‘ya‘yan ƙungiyar da su ci gaba da halayyar su na bin doka da oda musamman a wannan lokaci da mafi yawa yankunansu na arewacin ƙasar nan ke fuskantar barazanar taɓarɓarear tsaro tare da goya wa gwamnati baya don ta cimma burinta na ciyar da Jahar Bauci da ƙungiyoyi gaba duk da cewar, ƙungiyar ba ta da wata manufa dangane da sa kanta a harkokin siyasa, sai dai kuma akwai buƙatar da  a goya baya ga muradun gwamnati kasancewar mulki na dimokuraɗiyya ake yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here