Da sunan Allah mai Rahama mai Jinƙai.
Na ɗauki Alƙalamina da niyyar yin rubutu domin faɗakarwa da jawo hankalin gwamnatin Jahar Zamfara da kuma iyayenmu sarakunan jahar don yin nasiha zuwa garesu, ba don komai ba sai don a gyara domin mu sami zaman lafiya da ci gaba a jaharmu mai albarka, Allah ya taimake mu. Amin.
Na farko dai sanannen abu ne ɓarayi ‘yan fashi da makami sun addabi Jahar Zamfara, ta yadda suke wa bayin Allah kisan gilla a ƙauyuka da dama na Jahar Zamfara, wanda har an wayi gari abin yana nema ya gagari jami’an tsaro. Wanda masu yin wannan ɗanyen aiki ba wasu baƙi ba ne, illa matasa ne marasa aikin yi da suka yi wa jahar katutu. Abu ne a fili ƙarara cewa, lallai da za ka zagaya cikin garin Gusau da sauran ƙananan hukumomi, kai ka san irin yadda za ka ga matasa ‘yan zaman kashe wando, da ba su aikin fari ba su na baƙi suna yawo lungu-lungu, kwararo-kwararo, ba sa komai sai maula da fadanci, kai ma ka san lallai a rina, wai an saci zanen mahaukaciya.
To, ni nasihata a nan zuwa ga gwamna shi ne, lallai ya tashi tsaye domin ganin an yi maganin rashin aikin yi a tsakanin matasa, wanda shi kaɗai ne hanya mafi sauƙi da za a yi maganin wannan musiba da bala’i da suke addabar wannan jahar tamu mai albarka. Gwamna ya sani, gayyato Ali Ƙwara ba shi ne mafita ba, mafita shi ne, lallai a shagaltar da matasa ta hanyar samar masu aiki, domin su amfani kansu, kuma su kasance sun amfani jahar.
Sanya ‘yan ƙalilan daga wasu matasa ƙarƙashin su Bashari matutu da gundumi da sauran ‘yan bangar siyasar gwamna, su kwashe kwata da shara, a wata a ba su dubu goma-goma ba shi ne mafita ba, a’a, mafita sh ine ƙirƙiro da ingantattun ayyuka wanda ɗimbin dubban matasa da ba su da aikin yi za su amfana.
Sannan haƙƙin gwamnati ne ta ɗora matasa a kan hanya domin su san ciwon kansu tare da nuna musu muhimmancin neman na kai da muhimmancin dogaro da kai da kuma nuna masu illar matashi ya zama ɗan maula, mai zaman kashe wando, bafade.
Ga shi a halin yanzu saboda rashin aikin yi a tsakanin matasa a Jahar Zamfara, sace-sace da miyagun ayyuka kullum sai ƙaruwa suke yi, sai ga shi irin abin nan da ake cewa, ana kukan targaɗe sai ga karaya, shugaban daraktocin kamfanin alawa na Gusau da aka fi sani da suna “Gusau Sweet Factory”, Alhaji Yusuf Garba ya tabbatar cewa, lallai kamfanin zai rushe, (wato ya dakatar da aiki) sanadiyyar rashin isassun al’amuran tafiyar da kamfanin, a lokacin da yake zagaya kamfanin tare da kwamishinan kasuwanci na Jahar Zamfara, Alhaji Hassan Zurmi. Wanda tsayawar kamfanin zai yi sanadiyyar sallamar ɗaruruwan ma’aikata, wanda ba abin da hakan zai haifar illa ƙara dagulewar al’amurra da suka shafi tsaro. Shi dai Alhaji Yusuf Garba ya ce kamfanin yana neman gudunmawar gwamnatin jaha domin ya ci gaba da tafiyar da harkokinsa. Inda ya ce suna neman gwamnatin jaha ta taimaka masu da rancen Naira miliyan ɗari da hamsin, idan ba haka ba kuwa, lallai kamfanin zai rushe gaba-ɗaya.
Saboda haka, ina kira tare da nasiha zuwa ga gwamna da kar ya bari wannan abin kunya ya faru a kan Naira miliyan ɗari da hamsin kacal, wanda ba komai ne ba a wurin gwamnatin.
Gwamna ya sani fa, wannan kamfani na alawa ya taɓa zama kamfani na biyu mafi girma a Najeriya. An kafa shi shekara arba’in da suka wuce, sannan wannan kamfani shi ne mafi tsufan kamfanin alawa a yankin arewa maso yamma. An kafa shi a shekarar 1972 da nufin samar wa matasan yankin aikin yi. Mai kamfanin a wancan lokaci shi ne marigayi Abdallah Akari ɗan ƙasar Lebanon, wanda Sardauna ne ya ba shi takardar izinin zama ɗan ƙasa domin amfaninsa ga al’umma. Kuma kamfanin yana yin katan dubu arba’in na alawa a da, amma yanzu ko katan ɗaya ba ya yi, saboda haka ina kira ga kwamishina Hassan Zurmi da Gwamna Abdul’Aziz Yari da su tashi tsaye lallai kar su bari wannan masana’anta ta durƙushe.
Sannan na biyu, zan yi tsokaci ne da nasiha zuwa ga wasu daga cikin sarakunan Jahar Zamfara, a kan wani labari da kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cewa, wai sarakunan Zamfara za su ɗauki nauyin wani bil a majalisar dokokin jahar, da zai hana auren wuri (wato aurar da ‘yan mata da wuri) a Jahar Zamfara. Sun kafa dalili a kan cewa, auren wuri shi ke kawo ciwon yoyon fitsari, wanda a gaskiya ba haka ba ne; domin binciken masana aikin likitanci ya tabbatar da cewa, aurar da yarinya da wuri ba shi ke kawo ciwon yoyon fitsari ba. Abin da ke kawo shi ne, doguwar naƙuda da rashin kayan aiki ingantattu a asibitocinmu da kuma rashin ƙwararrun unguwarzomomi da za su kula da irin waɗannan matsaloli a asibitocinmu. Saboda haka ina kira ga sarakunan Jahar Zamfara da ke da hannu a ɗaukar nauyin wannan bil, da su ji tsoron Allah, su sani cewa, auren wuri shi ke kawo ciwon yoyon fitsari, suka ne ga addini saboda haka su janye wannan ƙuduri nasu.
Bukhaari, Muslim, Abu Dawuda, An-Nasa’i, Ibn Majah, Ad-Daarimiy, Baihaki, Ibn jaarud, At-tayalisi, Ahmad, Ibn Auwanah, Haythamiy, Al-haakim, Ibn Hibban, Ibn sa’ad, Al-Bazzar, sun ruwaito hadisin A’isha Allah ya ƙara mata yarda inda take cewa;
“Annabi (SAW) ya aure ni ina ‘yar shekaru shida sannan na tare a gidansa ina ‘yar shekaru tara, sannan ya rasu (SAW) a lokacin ina ‘yar shekaru sha takwas”.
Sannan Ibn Kathir ya faɗa a cikin shahararren littafinsa mai suna Al-bidayah Wan-nihaayah cewa;
“Babu saɓani a wurin malamai, duka sun yi ittifaƙi cewa;
“Annabi (SAW) ya auri A’isha (R.A) tana ‘yar shekaru shida, sannan ta tare tana da shekaru tara”.
Saboda haka na ke cewa, a bisa wannan dalili, bai kamata Musulmi ya soki auren wuri ba. Musamman a wannan zamani da fasiƙanci ya yawaita.
Saboda haka ya ku iyaye na sarakuna, lallai ina kiranku da cewa, ku janye wannan magana.
Sannan tsokacina na ƙarshe zan yi nasiha ne tare da jawo hankalin Gwamna Abdul’Aziz Yari da muƙarrabansa da su ji tsoron Allah, su daina kallon mai faɗa masu gaskiya a matsayin maƙiyinsu, domin duk wanda zai jawo hankalinka a kan wasu kura-kuranka don ka gyara, to, ba ƙaramin masoyinka ba ne.
Kafofin yaɗa labarai sun buga saƙon gargaɗi zuwa ga Mai Martaba Sarkin Zurmi, Alhaji Abubakar Atiku, saƙon da ya fito ta hannun mai bai wa gwamna shawara a kan harkokin sadarwa da kafafen yaɗa labarai, Alhaji Sani Abdullahi Tsafe, a kan shi Sarkin Zurmi ya nuna damuwarsa game da halin ko-in-kula da gwamnati ke nunawa a kan sha’anin tsaro a jahar, da ya addabi al’umma musamman kisan da ‘yan fashi suka yi wa ‘yan banga goma a yankinsa, shi ne sai ita gwamnatin Abdul’Aziz Yari ta nuna cewa, maganganun na Sarkin Zurmi, maganganu ne da za su harzuƙa jama’a, saboda haka gwamnati ba za ta taɓa yarda da irin wannan ba, kuma ba za ta lamunce ba.
To, ka ga a haƙiƙanin gaskiya wannan gwamnati ba ta son a faɗa mata gaskiya, in ba haka ba, mene ne laifin Sarkin Zurmi a wannan al’amari? Ana buƙatar ne ya ga gaskiya ya yi shiru ya ƙi magana? To, gwamnatin Zamfara dai da muƙarrabanta, sun san ko waye Sarkin Zurmi, Alhaji Abubakar Atiku, a iya sanina da shi, ban yi tsammanin barazana irin wannan ta hana shi fadar gaskiya ba, a kodayaushe, kuma ko a kan waye.
Wannan ba shi ne karo na farko ba da wannan gwamnati ta Zamfara ta fito fili ƙarara ta ƙalubalanci wani mai sarauta ba. Idan za mu iya tunawa, kwanakin baya ma Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Muhammadu Kabir Ɗanbaba, ya faɗi gaskiyar abin da ke faruwa a kan gubar dalma cewa, yara da mutanen wasu ƙauyuka suna cutuwa da gubar. Nan take gwamnatin ta ƙaryata shi, kuma ta ƙalubalance shi a kafafen yaɗa labarai ta hannun kwamishinan yaɗa labarai, Alhaji Ibrahim Birnin Magaji. Ka san wannan ya nuna ƙarara a fili cewa, wannan gwamnatin ta Yari (Ɗanmakau), ba ta son gaskiya, kuma ba ta son masu faɗa mata gaskiya. Saboda haka sai mu ce Allah ya kyauta, kuma idan masu shiryuwa ne, Allah ya shiryar da su, idan kuma ba masu shiryuwa ba ne, Allah ya kawo wa Zamfarawa gwamnatin jama’a ta al’umma, wadda suke so, kuma tana son su Amin. Kuma lallai ya kamata mu san cewa, yanzu kan mage ya waye, kuma Zamfarawa idonsu ya buɗe, ba wawaye ba ne, ba ƙidahumai ba ne. Duk gwamnatin da ta kyautata masu sun sani, kuma za su ci gaba da goyon bayanta, haka duk gwamnatin da ta munana masu, sun sani kuma za su juya mata baya, su kifar da ita idan zaɓe ya zo, kuma sun gaji da gafara sa ba su ga ƙaho ba.
Lallai gwamnatin Yari da muƙarrabanta su sani, dole ne su tashi tsaye su kawo ƙarshen wannan kisan gilla da ake yi wa bayin Allah. Domin daga cikin abubuwan da yake wajibi a wurin kowace nagartacciyar gwamnati, ta kare wa al’umma, akwai tsare rayuka da kuma dukiyoyi.
Sannan Sarkin Zurmi, Alhaji Abubakar Atiku, kar ka yi shakkar faɗar gaskiya ko a kan waye, insha-Allah ba zan gushe ba ina yi maka addu’a a kan Allah ya kare ka. Da ma an ce in za ka faɗi, faɗi gaskiya, komai taka ja maka ka biya”. Sannan Allah yana tare da mai gaskiya a duk inda yake.
Sannan daga ƙarshe, Gwamna Yari ya sani, bai kai darajar Abubakar da Umar (R.A) ba, ko kusa amma, to, mu kalli huɗubobinsu a lokacin da aka zaɓe su a matsayin Khalifofi. Kowanensu cewa ya yi, idan na bi Allah da manzonSa da kuma gaskiya, to, dole a yi mini ɗa’a, amma idan na kauce a dawo da ni kan hanya koda da kaifin takobi ne, kuma kar a bi ni a kan kaucewar. Wannan shi ne irin tarbiyyar da sahabbai suka samu daga manzon Allah (SAW), sai aka wayi gari, komai matsayin mutum a cikinsu idan ya kauce, to, za su gaya masa gaskiya komai ɗacinta. Ina roƙon Allah (SWT) ya gafarta mana zunuban mu, kuma ya ba mu ikon gyarawa kafin ta Allah ta kasance a garemu. Amin.
Ma’assalam.
IMAM MURTADA MUHAMMAD GUSAU, (Abu Mus’ab), Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi, Okene Jahar Kogi. 08038289761, 08056557477.