Kasawar Majalisar Ɗinkin Duniya (2)

    1
    73572

    Wata kasawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya ita ce, bayar da matsayin kujerar-na-ƙi ga waɗansu ƙasashen da suka naɗa kansu a matsayin mambobin dindindin na kwamitin tsaro. Sashe na 24 ya ce, “Domin a tabbatar da cewa, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗauki matakin da ya dace”, tilas ne mambobin majalisar su gabatar da duk al’amuran da suka jiɓanci zaman lafiyar duniya da tsaro ga Majalisar Tsaro wadda “za ta ɗauki mataki a madadinsu.” Wannan dai ya nuna cewa, majalisar tana da naƙasu, domin kuwa ta bai wa waɗansu ƙasashe ‘yan ƙalilan ƙarfin bayar da shawara da ɗaukar mataki ga manyan al’amura, waɗanda suka haɗa da shigarwa, sallama da kuma ladabtarwa ga kowace daga cikin mambobin majalisar. Wannan ya saɓa wa maganar daidaito da ‘yancin da aka ce wai sauran tarkacen ƙawayen ƙasashen da ke cikin majalisar suke da shi. Raina hankali ne cewa, wai wata ƙasa ko ma ita kanta majalisar ba ta isa ta la’anci duk wani matakin hawa kujerar na-ƙi da wata mamba ta dindindin ta ɗauka ba. Ƙre da ƙarau, babu wani mataki da Majalisar ta Ɗinkin Duniya za ta iya ɗauka face sai kwamitin tsaro ya aminta da shi.

    Wata kasawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ita ce rashin haɗa kan ƙasashen duniya. Wannan kuwa ya biyo bayan Yaƙin Cacar Baki. Yaƙin Cacar Baki dai wani faɗan saɓanin ra’ayi ne, na fatar baki, a tsakanin ƙasashen Amurka da Tarayyar Sobiyet, wanda kuma ya yi wa duniya barazana.

    Bayan da waɗannan abokan gaba suka yi zazzafar mahawara kan waɗanda suka cancanci halartar taron Birnin San-Francisko na 1945 da kuma waɗanda basu cancanci halartarsa ba, dangantakar Rasha da Amurka ta yi tsamari sosai, a tsakanin shekarar 1946 zuwa ta 1991. Ƙasashen Turai da Amurka sun tsunduma wajen sarrafa makaman nukiliya da kuma faɗaɗa tsaronsu. Misali, a shekarar 1949, Amurka da ‘yan amshin shatarta sun kafa ƙungiyar tsaro ta NATO (wadda a halin yanzu ake fakewa da ita wajen kai farmaki a ƙasashe masu barazana ga Turai da Amurka), a yayin da Rasha da ƙawayenta suka rattaɓa hannun yarjejeniyar (Birnin) Waso a shekarar 1955. Da yake yanzu Yaƙin Cacar Baki ya wuce, ba abin da manyan ƙasashen duniya kamar Yahudawan Isra’ila ke yi face sarrafa da kuma mallakar makaman ƙare dangi. Amma kuma  ƙasashe kamar Libiya, Iraƙi, Koriya ta Arewa da Iran an ɗauke su a matsayin ƙasashen da ba su cancanci su mallaki irin waɗannan makaman ba. Wannan wace irin shari’ar gatari ce?

    Hakazalika, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙasa, ta la’akari da yadda take nuna isar-kadagi da son kai wajen yanke wa waɗansu ɗaiɗaikun jama’a da kuma ƙasashe marasa ƙarfi hukunci ta hanyar amfani da Kotun Ƙasa da Ƙasa. Mun sani cewa, a shekarar 1987, Kotun ta Duniya ta caji shugaban ƙasar Yugoslabiya, Solobodan Milosobich, wanda ya mutu a hannunta.

    A halin yanzu, tana cajin shugaba mai ci, Omar Al-Bashir na Sudan, da Mu’ammar Gaddafi na Libiya kafin mutuwarsa. Dukkaninsu, an caje su ne da laifuffukan da suka saɓa wa bil’adama. Amma kuma duk da haka, wannan kotu, ta ƙi ta ɗauki wani mataki a kan ɗan-jidali, Joj Bush na Amurka, Ariyel Sharon ko Benjamin Netanyahu na Isra’ila. Duk da yake wannan kotun, ta ɗauki mataki a kan waɗanda suka yi kisan-kiyashin ƙasar Ruwanda kuma a halin yanzu, tsohon shugaban ƙasar Laberiya, Charles Tela da tsohon Kwamandan Sojojin Sabiya, Bikto Miladich na hannun ta, ba mu san dalilin da ya sa ta bar tsohon shugaban ƙasar Iraƙi, Saddam Hussain Al-majid Al-Tikriti ya mutu a hannun Amurkawa ba.

    Wani babban dalili da ke nuna kasawar Majalisar Ɗinkin Duniya, shi ne katsalandan da ƙasar Amurka ke yi ma ta. Tun a ƙarshen ƙarni na 19, lokacin da Amurka ta ƙago ‘Manifest Destiny’ (wanda ke iƙirarin cewa, wai Amurkawa sun fi kowa a duniya, kuma wai Allah ya ɗora masu nauyin wayar da kan sauran ‘ƙauyawan’ duniya), ya zuwa bayar da gudunmawa da ta yi a yaƙin duniya na ɗaya da na biyu, wanda ya sa ta sami zama matsayin ƙasa mai faɗa a ji a duniya (wato Super Power). Amurka ta fito fili ta nuna sare-sarin mamayar duniya. Ta yi mugun maguɗi wajen kafuwar ƙungiyar ‘League of Nations’; ta kuma ƙi shiga ƙungiyar. A yayin da ta jagoranci kafuwar Majalisar ta Ɗinkin Duniya, ta yi tsaye wajen tabbatar da ganin ta mamaye ta. Ana iya gane hakan ne idan aka kalli sashe na 110 na dokokin majalisar. Wannan sashen ya ce; “ƙasar Amurka ce za ta raba” kwafen “Yarjejeniyar da aka rattaɓa wa hannu,” ta kafuwar Majalisar Ɗinkin Duniya “ga duk ƙasashen da suka rattaɓa hannunsu.” A taƙaice ma, jami’an Hukumar Leƙen Asirin Amurka na ‘Federal Bureau of Investigation’ (FBI) ne suka tantance ma’aikatan majalisar a lokacin da aka kafata. A nawa ra’ayi, a nan, ma iya cewa, wannan ƙarara ya nuna mana cewa, majalisar ba kome ba ce face wani ɓangare na Ofishin Kula da Harkokin Wajen Amurka (wato State Department).

    Tasirin Amurka kan Majalisar ta Dinkin Duniya ya ƙunshi maƙudan kuɗin da take kashe mata, domin kusan kacokan ita ce ke ɗauke da ita. Wannan shi ne dalilin da ya sa a kodayaushe take ganin cewa, tana da damar nuna isa ga al’amuran majalisar, ta hanyar hawa kujerar-na-ƙi, take kuma saɓa wa ƙudurorinta. Ire-iren waɗannan take-take da wuce makaɗi da rawa su ne suka ba ta dama ta kai wa maƙiyanta kamar Afganistan da Iraƙi hare-hare, haka dai ƙaddam, take kuma goyon bayan tare da ɗaukar nauyin ta’addancin ƙasar Yahudun Isra’ila – wadda (Isra’ilar) a kodayaushe take kau-da-kai ga ƙudurorin majalisar, tamkar dai yadda (ƙasar ta Amurka da gangar), ta rungume hannu, ta yi mui, a tsawon lokacin da gwamnatin wariya da nuna bambancin launin fata ta Afirka ta Kudu ta ɗauka tana uzzura wa baƙar fatar ƙasar masu rinjaye.

    A kammalawa, ina son in yi tuni ga mai karatu cewa, ƙasashe mafi ƙarfi na duniya ne suka kafa Majalisar Ɗinkin Duniya domin su sami damar tagayyarar da sauran ƙasashe ta fuskar tattalin arziƙi, siyasa da tsarin rayuwa. Duk da yake, majalisar tana aiki tuƙuru, ta hanyar hukumominta daban-daban, da nasarar kawo ƙarshen mulkin mallaka da ta yi a ƙasashe da dama, a nawa ra’ayi wannan majalisa, wani dandali ne kawai na ƙara tatse arziƙin, da kuma mallake ƙasashe marasa ƙarfi da aka (ce wai an) bai wa ‘yancin kai, ta hanyar salon sabon mulkin mallaka (wato neo-colonialism). Kasawar da majalisar ta yi na kawo ƙarshen rikice-rikice a duniya, tasiri da abin da ya biyo bayan Yaƙin Cacar Baki (wato Cold War), amfani da kotun ƙasa da ƙasa (wato Kotun Duniya) don cin zarafi da uzzurawa ga ƙasashe da waɗansu zaɓaɓɓun mutane da babakeren da Amurka ke yi, sun isa su nuna mana cewa wannan ƙungiya ta ƙasa da ƙasa ta kasa cimma burin da aka ce (wai) an kafa ta don shi. Kamar wai yadda Bahaushe ke cewa, “Duk inda mai aro zai je, da sanin mai riga,” wannan marubuci na kallon Majalisar Ɗinkin Duniya a matsayin wata kafa ta mulkin duniya bisa ga zalunci da bautarwa irin ta zamani. Ba ta haifar da kome ba face ɗaukaka rayuwa da matsayin manyan ƙasashe da kuma dakusar da ƙasashe marasa ƙarfi na duniya, waɗanda akasarin jama’arsu suke cikin tsumma, tagayyara, talauci da halin ha’ula’i.

    AƘilu M. Shehu Yabo,

    Wani mai sharhi ne,

    Mai zaman kansa da ke Yabo,

    Jihar Sakkwato. Ana iya samun sa a 07088213989, 08035293788 ko a

    i-mel: akilunyabo@yahoo.com.

    1 COMMENT

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here