Isah Ahmed, Daga Jos
MATASAN garin Unguwar Bawa, Saminaka da ke ƙaramar hukumar Lere a Jahar Kaduna sun fara gudanar aikin gina wa makarantar Islamiyyarsu ta Madinatul Ahbab mazauninta na dindindin a garin na Unguwar Bawa.
Su dai matasan waɗanda sun kai 130 kuma tsofaffin ɗaliban makarantar sun lashi takwabin gina makarantar ne, ganin an yi shekara da shekaru ana ta neman gudunmawar gina makarantar daga ‘yan siyasar da suke riƙe da muƙamai da sauran masu hali na yankin amma abin ya gagara.
Da suke zantawa da wakilinmu, kan wannan aiki da matasan suka fara, shugaban makarantar, Malam Usman Salisu da shugaban ƙungiyar iyayen ɗaliban makarantar Malam Sunusi Jibrin Maharba da sakataren makarantar Malam Tijjani A. Yusuf, sun bayyana cewa, ganin an yi shekaru da dama ana koyar da ɗaliban wannan makaranta a Zauruka ba tare da samun azuzuwa ba.
Duk da cewa, an yi ta neman taimakon ganin an gina wannan makaranta ya sanya waɗannan matasa, suka taru suka haɗa kansu don ganin sun gina makarantar. Bayan da shugaban makarantun Madarasatul Ahbab na ƙasa, marigayi Sheikh Haruna Rasheed ya bayar da shawara a lokacin da yake raye.
A cewarsu, matasan sun ƙiyasta za su kashe kuɗi sama da Naira miliyan 2.5 wajen gudanar da wannan aiki, don haka suka yanka wa junansu haraji da ya kama daga Naira dubu 2 da Naira dubu 3 da Naira dubu 10 da Naira dubu 15 da kuma Naira dubu 20.
Suka ce ya zuwa yanzu matasan sun kashe kuɗi sama da Naira dubu 300, a wajen wannan aiki da suka sanya a gaba wanda suke sa ran kammalawa nan ba da daɗewa ba.
Suka ce a gaskiya waɗannan matasa sun yi abin koyi kan wannan aiki da suka sanya a gaba. Don haka sun yi kira ga matasa da sauran al’ummar Musulmi su yi koyi da waɗannan matasa wajen gudanar da irin wannan aiki.