Wazirin Katsina Ya Cika Shekara 10 Da Naɗinsa

0
8536

Abdullahi Muhammed, Daga Katsina

A JUMA’AR nan ne Wazirin Katsina, Dokta Sani Abubakar Lugga ya cika shekara goma da naɗinsa a matsayin Wazirin Katsina wanda marigayi Sarkin Katsina, Alhaji Muhammadu Kabir Usman ya naɗa shi.

Sai dai a maimakon, shirya bikin hawan dawakai da kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, addu’o’i a kai ta gudanarwa a gidansa da ke cikin garin Katsina

Malaman da suka haɗa da na ƙungiyoyin Izala da Ɗariƙa suka gudanar da addu’o’in.

A jawabinsa bayan kammala gudanar da addu’o’in Wazirin Katsina, Alhaji Sani Abubakar Lugga ya ce wannan lokaci na halin da ƙasa ke ciki ba na shagulgula ba ne, shi ya sa, ya gayyato malamai domin su gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya. Ya yi addu’ar fatar Allah ya bada shugabanni nagari masu tsoron Allah.

Haka kuma ya yi roƙon ga Allah ya kawo zaman lafiya ga inda ake ta fitintinu  a faɗin duniya baki ɗaya.

Ya yi nuni da cewa, a shekarun da ya yi yana kan sarautarsa na Wazirin Katsina bai fuskanci wani ƙalubale ba.

Sai ya gode wa Allah da ya nuna masa wannan rana da fatar Allah ya zaunar da ƙasar nan lafiya.

Malaman da suka haɗa da liman Lawal Sani, Na’ibin Liman Abba, Malam Sani Ƙerau tare da sauran manyan malamai suka gudanar da addu’o’i daban-daban      domin taya Wazirin murnar shekara goma da naɗinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here