JABIRU A. HASSAN, Daga Kano
SarkiN tashar Malam Ƙato Sikwaya da kuma Sabon Gari da ke Kano, Alhaji Isyaku Hassan ya bayyana cewa, ƘirƘiro da hukumar karota da gwamnatin Jahar Kano ta yi ƘarƘashin jagorancin Gwamna, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya kawo wa jahar da al’ummarta martaba da ci gaba da kuma bunƘasa harkokin yau da kullum.
Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce za su ci gaba da bai wa wannan hukuma goyon baya domin tabbatar da doka da oda a matsayinsa na shugaba.
Haka kuma babu wata Ƙasa a duk faɗin duniya da za ta ci gaba idan har babu doka da oda, saboda haka ƘirƘiro wannan hukuma ya yi daidai da wannan zamani kuma ya yaba wa shugaban hukumar da mataimakinsa wajen jajircewa da tabbatar da aikin da aka sa su.
Hassan ya yi kira ga direbobi da sauran al’ummar jahar su bai wa wannan hukuma goyon baya domin ci gaban Jahar Kano da Ƙasa baki ɗaya.