Akwai Alheri Karantar Da Musulmi — Hajiya Dandalin Turawa

0
2468

GTK: Masu karatu za su buƘaci sanin ko wace ce ke ?

Hajiya Zainab: Auzubillahi minashshaɗanir rajim Bismillahir Rahmanirrahim. Suna na Hajiya Zainab Garba Dandalin Turawa Kano, an haife ni a unguwar Dandalin Turawa cikin birnin Kano aƘalla na sami shekara 40 ke nan da haihuwa.

GTK: Ta ɓangaren neman ilimi tun yaushe ne aka fara gwagwarmayar neman sani.

Hajiya Zainab: A gidanmu ni na fara neman ilimin boko da na Arabiya. Tun da muka tashi a gidan mu da ma mun iske akwai makarantar Islamiyya ana karatu har da na boko ake karantarwa duk a gidan namu, sai na bada ƘoƘari wajen neman ilimin guda biyu, Alhamdulillahi idan an fara sai in riƘa ɗaukar birona da littafi ina koya saboda ni na tashi da kwaɗayin in koyi karatun boko saboda haka sai na bada ƘoƘari na ci gaba da shiga aji ina koyon karatun bokon da na Arabiya da kyau-da kyau.

GTK: Idan mun fahimce ki ilimin zamanin ke ma ba a baro ki a baya ba kin nema?

Hajiya Zainab: Eh! Ina da ilimin boko bakin hali kuma Alhamdulillahi.

GTK: Hala, Hajiya ta ɗan matsa Ƙila har zuwa gaba da firamare?

Hajiya Zainab: Eh! Ina shirin zuwa makarantar gaba da firamare sai aka yi mini aure, ko da aka yi mini aure tun da ba a gida Kano muke zaune ba kudancin Nijeriya muka dawo da zama, Kurmin Yarbawa muka zauna, akwai makaranta a wajen kuma akwai yara mata, sa’o’i na da muke tafiya makaranta tare da su a Ƙofar gidanmu makarantar take ina shiga ɗaukar darasi da su.

GTK: Kun shafe lokaci mai tsawo zaman da kuka yi a Kurmin Yarbawa?

Hajiya Zainab: Eh! A Ƙauyen Ile-ife muka zauna kafin daga baya muka koma Ondo da zama.

GTK: Ga shi yanzu kuna garin Kalaba da zama?

Hajiya Zainab: Yadda aka yi muka dawo nan garin Kalaba da zama akwai wata yarinya da take hannun mijina an sa mata rana za a yi mata biki aka ce mu biyo ta nan mu faɗa masa, mu sanar da shi za a yi mata aure bayan ya koma gida Kano an yi biki an gama sai ya ce tun da zaman sa na Kalaba ya fi yawa da can Ondo sai ya ce mu dawo nan mu zauna shi ya sa muka dawo nan Kalaba muka zauna.

GTK: Tun da Allah ya yi zaman ku nan Kalaba ga shi har kin buɗe makarantar Islamiyya me ya jawo hankalinki har ki ka buɗe makaranta mai suna Nurul Huda Islamiyya ta matan aure aƘalla shekara nawa ke nan da kafa wannan makaranta?

Hajiya Zainab: Tun lokacin da na zo garin nan (Kalaba) na kan ce da matan aure su riƘa zuwa muna yin karatu, nakan ce masu na Arabiyya da na boko haka muka fara da mutanen unguwar nan ina cikin gaya masu wasu sukan zo wasu kuma su Ƙi zuwa, haka dai muka fara karatun daga baya aka yanke shawarar a buɗe makaranta tun da muna samun yawan waɗanda suke zuwa matan.

GTK: Me ya jawo hankalinki kan karantarwa har ki ke son bayar da taki gudunmawar?

Hajiya Zainab: Dalilin da ya sa har nake son in karantar saboda tana da muhimmanci, mai amfani da alheri ina son in sami alherin da ke  cikin karantar da ɗan uwanka Musulmi abin da bai sani ba ya sani, ilimi baya Ƙarewa domin ba yadda za a yi a ce ka fi kowa sani.

GTK: Ana samun nasara a kan abin da aka sanya gaba?

Hajiya Zainab: Allah ya taimaka waɗanda ba su san wani abu ba yanzu sun sani sosai.

GTK: Shekarar makarantar nawa da kafawa?

Hajiya Zainab: Shekara huɗu ke nan.

GTK: Idan mace tana son taimakon addini ko al’um-ma sai ta zama wata gawur-tacciyar mai kuɗi tukuna?

Hajiya Zainab: A’a, ko alama ba dole sai ka zama mai kuɗi ba domin za ka taimaki addini ko al’umma a haka ai ka ga mu ba kuɗin garemu ba, ba kuma masu kuɗin ba ne zuciyar yi ce kurum, Allah ya huwace, ka ga ba kuɗi muke karɓa ba, ba kuma wani ke ba mu ba, mu ne dai muke yin karo-karo a junan mu na kuɗin wata muke fita haƘƘin malamai ga shi kuɗin wata ma wasu ɗaliban ba bayarwa suke yi ba komai mu muke yi da kan mu.

GTK: Ana iya cewa, kishin addini da son yaɗuwarsa ce ta sanya ki ka buɗe makaranta?

Hajiya Zainab: Yau wa da son taimakawa Ƙwarai kuwa.

GTK: Ƙila akwai Ƙalubale da kike fuskanta game da gudanar da wannan makaranta za mu so ki gutsura mana kaɗan?

Hajiya Zainab: Ƙalubalen da muke fuskanta shi ne rashin zuwan ɗalibai makaranta kan lokaci wasu lokutan ma sai an fara karatu in ɗauki hijabi na ina bin su gida-gida ina kirawo su ku zo an fara karatu da ma kuma ka san wanda duk ya ce zai tara jama’a dole sai ya yi haƘuri da halayensu don haka haƘuri nake yi ina bin su gida-gida ina lallashinsu.

GTK: Yaya za ki kwatanta Ƙimar Ƙaruwar ɗalibai  shekarun baya da kuma ɗan tsakanin nan?

Hajiya Zainab: Alhamdulillahi bayan matan aure ma har da yara ’yan mata yanzu suna zuwa makarantar duk ana karatu da su.

GTK: Makarantar Nurul Huda na ɗaya daga cikin manyan makarantun Islamiyya masu yaɗa ilimin manya a Kalaba, kina samun wani tallafi ne daga gwamnatin jiharku ta Kano ko ta nan Kuros Riba?

Hajiya Zainab: Gaskiya gwamnati ba ta ba mu wani taimako, ba ta taɓa ba mu ko kwabo ba mu ne dai muke ɗaukar ɗawainiyar komai namu babu wani mai taimaka mana sai Allah, amma gwamnan Kuros Riba ya turo mana malamai biyu da ke karantar da mu ilimin boko, suna zuwa suna karantar da mu ilimin boko.

GTK: Kasancewarki ’yar asalin Jihar Kano Ƙin taɓa neman taimako daga wurin gwamnatin jihar don ki bunƘasa makarantarki?

Hajiya Zainab: Wallahi ba mu taɓa neman taimako ba daga hannun gwamnatin Kano ba domin gudanar da ɗawainiyar wannan makaranta ba.

GTK: Ko nan gaba akwai niyyar yin haka?

Hajiya Zainab: Eh! Akwai niyya musamman ka ga gidan nan da muke ciki mai shi ba Musulmi ba ne ya amince mana ya ba mu aro saboda muna zaune girma da arziƘi da shi ya sa bai hana mu ba ya ba mu ya amince mana mu yi makaranta, nan gaba za mu nemi taimako domin mu gina tamu makarantar saboda nan gaba idan ya nemi mu ba shi gidansa ka ga dole mu ba shi mu kuma mu nemi wani wurin don haka nan gaba za mu buƘaci taimakon.

GTK: Ƙaddara mai girma Malam Ibrahim Shekarau ya karanta hirar nan ya gayyace ki ya kuma tambaye ki irin taimakon da ki ke so za ki buƘaci na kuɗi ne ko yaya?

Hajiya Zainab: Gaskiya in dai har zai taimaka mana, to, ya gina mana makaranta ba kuɗi zan so ya ba ni ba gara a gina mana makaranta ya fi, idan aka gina mana makaranta, to, zan fi son wannan sannan kuma a ba mu malamai.

GTK: Ko kina da wani Ƙarin bayani ko saƘo ga ɗalibanki?

Hajiya Zainab: Kira zan yi ga matan aure don Allah su yi haƘuri da mazajensu musamman a wannan wata na azumi idan mai gida ya yi maki kayan salla ki amsa ki gode idan bai yi maki ba ki yi haƘuri kada ki ce kin yi masa bauta ta aikin sahur da buɗa baki bautar Allah kika yi a yi la’akari da marrar da muke ciki saƘona ke nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here