GTK: Za mu so jin taƘaitaccen tarihinka?
TSIGA: Alhamdulillah, suna na Muhammad Sani Ibrahim Tsiga, Tsiga gari ne cikin Jihar Katsina. An haife ni ne a Ƙaramar hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna.
Na yi karatuna na firamare a unguwar Rigasa, na kuma yi karatun sakandare a Rigacikun kuma yanzu haka ina zaune ne a cikin garin Kaduna a unguwar Rigasa. Kamar yadda Allah Ya tsara ban sami kammala karatuna ba na tsunduma harkar fim.
GTK: Ko za ka iya tuna lokacin da ka fara wasan kwaikwayo?
TSIGA: Eh! To, na fara wasan kwaikwayo ne tun ina makarantar firamare. Abu ne da nake matuƘar so tun ina yaro, ina sha’awa da kuma jin daɗin yin wasa, za ma ka lura da hakan duk lokacin da nake kan daɓe ko kuma nake fim.
GTK: Ga shi dai kai cikakken Bahaushe ne amma abin mamaki sai kuma kake fitowa a matsayin ɗan Gwari, ko me ya sa?
TSIGE: Ka ga dai na lura ne na ga muna da Ɗan Yarbawa, wanda yake kwaikwayon Ƙabilar Yarbawa, haka kuma muna da Baban Chinedu, mai kwaikwayon Ƙabilar Ibo da dai sauransu. Amma sai na ga ga wata Ƙabila mai muhimmanci wacce ba wanda ya damu ya kwaikwayeta a indostirin Hausa wato Ƙabilar Gwari. Sai aka yi sa’a ni kuma na zauna a garin Tafa wanda mafi yawancinsu Gwarawa ne, ina zuwa kotu kallon shari’a wanda idan suna Hausa sai a yi ta masu dariya. Haka ya ja ra’ayina na fara wasa a matsayin ɗan Gwari ina kwaikwayon harshensu.
A yanzu maganar da muke yi da kai ina tabbatar maka na san kusan komai na Ƙabilar Gwari, har ina ma jin yaren kodayake ban Ƙware ba sosai domin har Ƙauyukansu nakan je don in gane wa idona irin al’adarsu.
GTK: To, kana fitowa a matsayin mashayi, kana zuwa mashayarsu ne don ganin yadda suke yi idan ka je Ƙauyukansu?
TSIGA: Eh! wani lokaci ina zuwa mashayarsu domin gane wa idona abubuwan da ke gudana a wurin. Kamar kusan kowace Ƙabila, su ma Ƙabilar Gwari akwai masu shan giya wanda kuma suna da yadda suke al’amuransu. Suna giyarsu ta gargajiya “Burkutu”. Ina zuwa mashayarsu ba wai don in sha ba, a’a, sai dai don in ga yadda suke yi.
GTK: Yaya za ka kwatanta Ƙabilar Gwari?
TSIGA: Mutane ne masu son zaman lafiya da son junansu, suna da haba-haba da mutane. Da wuya ka ga suna faɗa tsakaninsu ko da wasu mutane, suna kuma da yin aiki tuƘuru.
GTK: Na taɓa jin cewa, ka yi dirama a rediyo Nijeriya na Kaduna, a lokacin wane matsayin kake fitowa?
TSIGA: Eh! Na yi aiki da rediyo Nijeriya, a lokacin ban fara fitowa a matsayin ɗan Gwari ba, ina fitowa ne a matsayin yaro domin lokacin ina yaro ne Ƙarami.
GTK: Waɗanne irin nasarori ko alherai ka samu a fannin wasan kwaikwayo musamman a matsayinka na ɗan Gwari?
TSIGA: Hmm! Na sami abubuwa da dama. Abin da na fi so shi ne yadda wannan matsayi na ɗan Gwari ya sami ɗaukaka. A sakamakon wannan matsayi na ɗan Gwari, jama’a da dama yanzu sun san Ƙabilar Gwari da kuma irin al’adunsu. Ina farin ciki da hakan domin ba Ƙaramin ci gaba ba ne.
Haka kuma ta ɓangaren samun kuɗi ko abin duniya, na sami nasarori da dama. Akwai lokacin da wani mutum ya gayyace ni wajen biki, so kawai yake in halarci bikin. Bayan bikin ya ba ni maƘudan kuɗi wanda kuma na ji daɗin hakan.
Wannan ya nuna mini muhimmancin fim a tsakanin al’umma, ya kuma Ƙara mini Ƙwarin gwiwa.
GTK: Ko za ka iya tuna yawan fina-finan da ka yi?
TSIGA: Da farko dai na fara Ƙirga fina-finaina, ina kuma rubutawa, amma daga baya dole ta sa na bari saboda ayyuka sun min yawa, ba ni da lokacin yin hakan. A yanzu dai ba zan iya cewa, ga iyakacin ko yawan fina-finan da na yi ba.
GTK: Ko za ka iya faɗa mana fina-finanka waɗanda ka fi so?
TSIGA: Akwai fina-finan da zan iya cewa, sun Ƙara ɗaukaka ɗan Gwari, suka kuma Ƙara ɗaukaka ni kaina har na zama abin da nake a yau. Akwai fina-finai kamar su “Ibro Ɗan Ruwa” da “A Fafata” waɗannan fina-finai ne da nake ji da su.
Haka kuma akwai fim ɗin “Ibro ka Girmi Sana’a”, akwai abin da na yi a fim ɗin wanda daga baya an ba ni labarin cewa, Ƙabilar Gwari sun ji daɗin abin da na yi, kai ba ma su kaɗai ba, har ma da Hausawan.