Gwamna Geidam Ya Bada Tabbacin Ciyar Da Harkokin Shari’a Gaba

0
1484

Muhammad Sani Chinade, Daga Damaturu

GWAMNA Alhaji Ibrahim Geidam na Jahar Yobe ya bada tabbacin ci gaba da inganta harkokin shari’ar jahar tare da mutunta ta ganin irin muhimmancin da sashin ke da shi dangane da ci gaban ɗorewar Ƙasa.

Gwamnan ya tabbatar da hakan ne a yayin da yake jawabi wajen rantsar da sabon AlƘalin-AlƘalan jahar (Grand Kadi), Kadi Alhaji Shayibu Talba a babban ɗakin taro na WAWA da ke gidan gwamnatin jahar a garin Damaturu.

Ya Ƙara da cewar, ya zama wajibi gwamnatin ta inganta sashin na shari’a kasancewar na ɗaya daga cikin ginshiƘan da suka samar da kowace irin gwamnati ne musamman a wannan lokaci na mulki irin na dimokuraɗiyya.

Gwamna Geidam ya ci gaba da cewar, sashin na shari’a na da muhimmiyar rawar takawa dangane da ciyar da kowace irin Ƙasa gaba a matsayinsa na raba gardama kan duk wata taƘaddama da ke iya tasowa dangane da madafun iko ga mulki irin na dimokuraɗiyya, don haka akwai buƘatar da a haɓaka shi.

Ya kuma hori sabon AlƘalin-AlƘalan da ya ɗauki wannan matsayi da ya samu da cewar, an ba shi ne ba don komai ba sai domin cancanta kasancewar, yana da ladubba a kan harkokin shari’a da ya yi fice a kai. Don haka abin buƘata ne da ya ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansa kan sabon muƘamin da ya samu kansa a kai kuma babban Ƙalubale ne a gareshi.

A cewar, Gwamnan wannan muƘami na AlƘalin-AlƘalai (Grand Kadi) da aka naɗa Alhaji Shayibu Talba an naɗa shi ne bisa dokar Ƙasa mai lamba 276 (1) ɗaya cikin baka wadda majalisar dokokin jahar ta albarkanta.

Don haka ya bada tabbacin ci gaba da haɓaka harkokin shari’a ba tare da nuna gajiya, ba da hakan ne ma a kasafin kuɗin da ya gabatar ga majalisar dokokin jahar a makon da ya gabata aka ware kaso mai tsoka ga sashin shari’a don gudanar da abubuwa masu muhimmanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here