HIMMA DAI MATA

0
3444

SAU da yawa mukan sami ra’ayoyin makarantanmu daban-daban game da wannan shafi na Himma Dai Mata, ya’alla ko don bada shawarwari ko kuma nuna jinjina ko yabo game da wata muƘala da muka yi a shafin.

Wani abin mamaki ko kuma abin sha’awa shi ne, a iya nazarin da na yi da kuma irin saƘonnin da wayoyin da muka samu daga makarantanmu, na fahimci cewa wannan shafi ba na mata ba ne kaɗai, domin kuwa maza ma na da sha’awar karanta shafin duk da cewa yawancin abubuwan da shafin ke Ƙunsa sun ta’allaƘa ne a kan rayuwar mata da al’amurran yara.

A cikin saƘonnin da muka riƘa samu, mutane da dama sun ba mu shawarwarin mu riƘa rubutu a kan zamantakewar mata da miji da kuma abokiyar zama, wacce aka fi sani da kishiya, domin bada shawarwarin da za su kawo zaman lafiya mai ɗorewa a cikin gida da ma al’umma baki ɗaya.

Ganin haka ne ya sa na yi tunanin rubuta muƘala game da kishi na mata, wato waɗanda ke auren miji ɗaya.  Wai shin mene ne kishi? Me ya sa ake kishi? Kuma mene ne amfaninsa ko ribarsa ga ma’aura?

A ra’ayin wasu, kishi na nufin nuna damuwa ko Ƙyashi a kan wani abu ɗaya da mutane fiye da biyu ke amfani da shi, ko suke hanƘoron kishi.

Wasu kuma sun bayyana kishi a matsayin wani yanayi da mutum kan tsinci kanshi na son mallakar wani abu ko zuciyar wani, shi kaɗai ba tare da wani ya samu wannan abin ko kulawar wannan mutumin, ko kuma hankalin mutumin ya fi karkata ga mai nuna kishin a kansa ba.

Idan ka shiga wasu gidajen, za ka ga babu kwanciyar hankali ko haɗin kai tsakanin matan, wani lokaci ma har da ’ya’yansu.  Kowace tana ganin ita ta fi cancanta miji ya kula ko ya fi son ta ko ’ya’yanta.

Mata ina son mu Ƙara fahimtar wani abu, Hausawa kan ce abin da arziƘi bai ba ka ba, to tsiya ma ba za ta baka ba. Saboda haka mai zai hana mu kwantar da hankalinmu, mu yi kishi irin na zamani, wanda ba zai kai mu ga halaka ba?

Abu na farko, da ya kamata kowace mace ta nema don samun kyakkyawar rayuwa shi ne ilimi.  Duk mace mai ilimi za ta kasance abin sha’awa kuma abin koyi ga kowa.  Idan an ce ilimi ba wai ana nufin ilimin zamani kawai ba, a’a bayan ilimin boko, ya kamata mace ta kasance mai ilimin addini, wanda shi ne gaba a kan komai.  Sannan kuma ta kasance mai ilimin zamantakewa da jama’a wato ta san yadda za ta riƘa mu’amala da jama’a don kauce wa kowace irin fitina.

Hausawa kan ce idan kasan halin mutum, to, sai ka ci maganin zama da shi.  Komai zafin kishi da abokiyar zamanki ke da shi, za ki iya amfani da iliminki wajen ganin kin kauce wa fitinarta.  Idan kina da ilimin boko zai iya kasancewa ke ma’aikaciya ce saboda haka ba ki da lokacin zama ki biye wa kishiya kuna fitina a cikin gida.

Hakazalika mai ilimin addini ta san irin sharuɗɗan da addini ya gindaya mata game da zamantakewar aure da kuma waɗanda take tare da su. Saboda haka komai zafin kishinta tana iya dannewa don gudun kar ta saɓa wa Ubangijinta wanda Shi ne Ya ba maza damar aurar mace fiye da ɗaya, idan har Ya jaddada cewa su yi adalci a tsakanin matansu don samun lada da kuma kwanciyar hankali.

Sannan kuma kowane irin zama kuke yi da kishiya, kada ki yarda ta haɗa ki faɗa da mijinki.  Za ki ga wani gidan kamar ana zaman lafiya, amma sai kishiya ta riƘa shirya maƘarƘashiya don ta ga ta haddasa fitina tsakanin abokiyar zamanta da mijinta.  Ko a inda ba a zaman lafiyar ma, kullum ƘoƘarinta shi ne ta haddasa wani abu da zai sa ki ga baƘin mijinki.

Ina kira gare ku mata, duk abin da kishiya za ta faɗa miki na ɓatunci game da mijinki, koda kuwa kina ganin kin amince mata, to, kada ki yarda ta ga ɓacin ranki, koda abin ya yi miki zafi a rai, ki daure kada ki bari ta gane, kuma kada ki yi masa maganar a gabanta.

Sannan idan za ki yi masa maganar ki kasance cikin natsuwa yadda ke da shi za ku yi magana cikin fahimtar juna.  Kin ga idan kika yi haka koda abin da ta faɗa da gaske ne yana iya ba ki haƘuri saboda shi ma zai ji nauyin yadda kika ɓullo masa.

Ina kuma son ki kiyaye, duk abin da ya faru tsakaninki da miji, to, ku yi ku binne a ɗaki ba tare da kishiyarki ko wani ya fahimci cewa wani saɓani ya shiga tsakaninku ba.  Ko fushi yake yi da ke idan kuna cikin jama’a ki saki ranki ki kuma lallaɓa shi cikin wasa da dariya.  Yin hakan zai sa shi ma ya sauko daga fushin da yake yi.

Wani babban kuskure da mu mata kan yi shi ne nuna Ƙiyayya ga ’ya’yansu mijinsu.  Bai kamata don kuna samun saɓani tsakaninki da abokiyar zamanki sai kuma ki tsangwami ’ya’yanta ba.  Ki sani laifin wani ba ya shafar wani. Kuma waɗannan yara ’ya’yan mijinki ne, idan kuma kina son zaman lafiya, to, dole ki so abin da mijinki ke so.

Ki kuma sani, masu iya magana na cewa ɗa na kowa ne.  Ki tattali yaro a duk inda kika haɗu da shi.  Ba ki sani ba, ta iya yiwuwa nan gaba ki mori waɗannan ’ya’ya na mijinki fiye da yadda za ki mori naki na cikinki.

Saboda haka ki kasance mai tattalin ’ya’yan mijinki a kodayaushe, ki riƘa jansu a jiki, ki kuma riƘa yi masu kyauta da basu shawarwari masu kyau a duk lokacin da buƘatar hakan ta taso. Sannan ki kasance a gaba wajen ganin mijinki na biya wa ’ya’yansa buƘatunsu.  Hakan zai Ƙara miki kwarjini da daraja a wurin mijinki da kuma ’ya’yansa.

A wasu lokuta da dama, za ki ga mace tana tada jijiyar wuya don mijinta ya hana ta fita amma kuma ya bar kishiyarta ta fita.  Tana iya yiwuwa abokiyar zaman taki da ta fita ba da izinin mijinta ta fita ba, ta dai gagare shi ne kawai ya bar ta ta fita ba don zuciyarsa na so ba.  Ki sani maza kanso mace mai kame kanta a cikin gida ba tare da yawan zuwa unguwa ba sai dai idan da wata ƘwaƘƘwarar hujja.  Ki kuma sani wani lokaci idan mijinki na hana ki fita, yana nuni ne da cewa yana matuƘar son ki, saboda haka yana kishin ki riƘa fita wasu mazan na ganin ki a waje.

Hakazalika kishin zamani na mana nuni da cewa yanzu mata ba sa yaji, wato ba su barin gidan mijinsu wai don sun sami saɓani da shi.  A maimakon haka mace kan yi kishin cikin gida, wanda ko waɗanda take tare da su a gidan ba za su fahimci wani abu ba. Sai dai a tsakaninki da shi za ki ɗan janye jikinki, ki riƘa ɗari-ɗari da shi har ya fahimci inda kika sa gaba sannan ya nemi ku sasanta.  Amma fa ki sani, a nan ina nufin in dai laifin mijin ne shi ne za ki iya yin haka.  Ba wai a ce ke ce mai laifi ba kuma ki riƘa fushi.

Sai dai ki sani yin hakan ba shi ne mafi a’ala a gareku ba.  Idan mijinki ya saɓa miki, mafi sauƘi shi ne ki zaunar da shi ku tattauna, ku kuma yafe wa juna.  Kamar yadda masu iya magana kan ce, zo mu zauna zo mu saɓa, saboda haka abu mafi cancanta shi ne a riƘa haƘuri da miji da kuma abokiyar zama.  Hakan shi zai kai mu ga cin ribar aure duniya da lahira, kamar yadda akan ce mahaƘurci, mawadaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here