Umar Saye, Daga Bauci
OFISHIN hukumar yaƘi da cutar Sida da tarin fuka da kuturta da maleriya na Jahar Bauci (BACATMA), ya gudanar da feshin maganin sauro da kuma aikin haɗin gwiwar yashe magudanun ruwa don kawar da Ƙazantar da ke haifar da yawaitar sauro, a wani matakin kai tsaye na magance zazzaɓin maleriya daga tushe.
Shugaban hukumar ta BACATMA, Dokta Mohammed S. Liman cikin jawabinsa a gangamin aikin feshin sauro da tsaftace magudanun ruwa da aka aiwatar a filin Ƙwallon Kobi, ya ja hankalin mutane da cewa, su kasance masu gyara muhallinsu don guje wa yaɗuwar Ƙwayoyin cuta musamman zazzaɓin maleriya wanda ake kamuwa da shi a kowane lokaci kuma yake ɓarna wa mutane.
Don haka, ya ce an fara wannan aiki na feshin maganin sauro da jimawa a cikin garin Bauci da kuma wasu yankunan Ƙananan hukumomi don kare kai da kuma nuna wa mutane muhimmancin tsaftar muhalli don ya zamanto rigakafi wanda ya fi magani kuma gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba. Don haka ya ce buƘatar gwamnati shi ne ta ga mutane a kullum suna rayuwa cikin Ƙoshin lafiya, saboda haka aka fito da shirin raba gidajen sauro kyauta da kuma magunguna na zazzaɓin maleriya na miliyoyin Naira da bin zuwa kowane saƘo don ilimantar da mutane game da muhim-mancin tsaftar muhalli.
Shi ma Hakimin Bauci, Alhaji Nuru Adamu Jumba a nasa jawabin, ya yaba game da ƘoƘarin gwamnati kan lura da lafiya tare kuma da aikin da hukumar BACATMA ke gudanarwa wajen yaƘi da manyan cututtukan da suke damun mutane a wannan lokaci. Don haka ya shawarci jama’a kan su riƘa tsaftace muhallinsu don kare rayuwarsu da ta iyalansu daga kamuwa da cututtuka.
A wani labarin kuma, ofishin shugaban ma’aikatan Jahar Bauci, Mista Abdon Gin ya bayar da lambar yabo ta musamman ga shugaban hukumar ta BACATMA, Dokta Mohammed S. Liman da wasu hukumomi huɗu da suka taka rawar a zo a gani wajen inganta ayyukansu a Jahar Bauci. Tuni dai aka yi bikin karramawar da bayar da lambar yabon a otal na Zaranda da ke Bauci inda aka bayyana ayyukan BACATMA a matsayin abin koyi ga sauran hukumomin gwamnati a Jahar Bauci.