Sarki na rayuwa kuma yana mutuwa

0
1389

Babu wani abin da Allah ke yi wa mai wata baiwa da baiwar ba a yi masa ba, domin Allah Ya nuna duka Shi ne ke yi masu. Sarki na rayuwa kuma yana mutuwa, haka talaka, haka malami da jahili, haka mai kuɗi da matalauci, suna Ƙoshi kuma suna jin yunwa, mai lafiya da mara lafiya in an wayi gari da mutum, wata rana lallai ba za a yi yammaci da shi ba. Haka in an yi yammaci da shi, wani dare ba za a wayi gari da shi ba, in ka yi dariya ko kuka ka yi, kuka ko dariya mai Ƙarewa ne a nan wanda ya yi maka dariya da wuya in da rai bai yi maka kuka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here