Tarihin Rayuwar Tsohon Ministan Wasanni Furofesa Adedoja

0
1443

NASARORIN Furofesa Touheed Adedoja a matsayin fitaccen malami masani kuma ɗan siyasa ba ɓoyayye ba ne. Ya kafa tarihi a zamansa na matsayin shugaban tsangayar ilimi kuma shugaban sashin ilimin wasannin motsa jiki a Jami’ar Bayero da ke Kano da kasancewarsa babban malami a Jami’ar Maiduguri.

Furofesa Adedoja tsohon ɗalibin Jami’ar Ile Ife da Jami’ar Eastern Illinois da kuma Jami’ar Jahar Oklahoma dukkansu a Ƙasar Amurka ya zama Furofesa ne yana da shekara 44 a duniya.

Kasancewarsa masani kuma Furofesan ilimin wasannin motsa jiki kuma shugaban harkokin wasanni, Furofesa Adedoja ya riƘe manyan muƘamai a sashin ilimi da tattalin wasanni.

Lokacin da yake riƘe da muƘamin shugaban kwalejin ilimi (Na Musamman) ta tarayya da ke Jahar Oyo, kwalejin ta sami gagarumar bunƘasa a fannin ci gaban ilimi da har yanzu mutanen Jihar Oyo suke alfahari da shi.

Mutanen Jihar Oyo suna alfahari da rawar da Furofesa Adedoja ya taka a fagen buƘasa ilimi a jahar, lamarin da ya sanya jahar ta sami gagarumar nasara a fagen bunkasa ilimi kamar yadda jadawalin hukumar bayar da ilimin bai-ɗaya na shekarar 2005 zuwa 2006 ya nuna. Furofesa Adedoja ne a matsayinsa na kwamishinan ilimi na Jahar Oyo daga shekarar 2009 zuwa 2010 ya tsara dabarun da ma’aikatar ilimi ta Jahar Oyo ta yi amfani da su don taitayar ɗalibai da ake kira (OYO-MESI), lamarin da ya kawo karuwar masu Ƙwazo a tsakanin ɗaliban jahar a jarrabawar kammala makaranta ta shekarar 2010, kuma hakan yana ɗaya daga cikin nasarorin da Gwamnatin Adebayo Akala ta samu.

Lokacin da majalisar dattawa ta tantance Furofesa Adedoja a watan Oktoban bara don naɗa shi a matsayin minista tarayyar Najeriya, kowa ya ɗauka za a naɗa shi minsitan ilimi ne fagen da duniya ta san shi.

Sai dai tura shi ma’aikata ayyuka na musamman bai zo wa mutane da mamaki ba, saboda an san zai iya farfaɗo da al’amura a duk inda aka tura shi kamar yadda aka sani.

Sai dai Ƙara masa da muƘamin ministan wasanni a baya-bayan nan ya nuna yunƘurin Shugaba Goodluck Jonathan na samun gagarumar nasara ta hanyar ɗora mutumin da ya dace domin ya kula da bunƘasa harkokin wasanni a Ƙasar nan.

’Yan Najeriya sun zuba ido suka yadda Adedoja zai farfaɗo da harkokin wasanni a Ƙasa nan kamar yadda ya yi a ɓangaren ilimi.

Furofesa Adedoja Ƙwararren masanin harkokin wasanni ne da ba kawai a aji ya tsaya ba, a aikace yana da Ƙwarewa sosai a sassa da dama da suka haɗa da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da Ƙwallon kwando da Ƙwallon raga da Ƙwallon kirket da kuma wasannin naƘasassu. Yana daga cikin waɗanda suka kafa sashin ilimin wasannin motsa jiki da ilimin kiwon lafiya a Jami’ar Bayero ta Kano, kuma yana cikin ’yan wasan Ƙungiyar Ƙwallon raga ta Jahar Kano a wasan Ƙwallon raga na Najeriya na farko da aka gudanar a Ibadan a 1971.

A lokacin da Furofesa Adedoja yake Kano, daga 1989 zuwa 1995 ya shugabanci Ƙungiyar wasannin motsa jiki na ’yan Dagaji (Kano State Amateur Athletics Association), a hukumar wasanni ta Jahar Kano da shugaban Ƙungiyar wasannin motsa jiki ta naƘasassu ta Jihar Kano, sannan mai bayar da shawarar Ƙwarewa kuma shugaban kwamitin Ƙwararru kan wasannin motsa jiki na manyan kwalejojin horar da malamai da kuma kwalejojin ilimi na Ƙasa (NATCEGA) da aka gudanar a Gumel ta Jihar Jigawa a 1990.

Har wa yau Furofesa Adedoja ya taɓa riƘe muƘamin shugaban Ƙungiyar wasan Ƙwallon kirrket ta Jahar Borno daga 1985 zuwa 1988. Kuma ya taɓa zama mamba a kwamitin al’adu a wurin taron Ƙasa kan harkokin Ƙasashen waje na ma’aikatar harkokin Ƙasasshen waje a 1986 lokacin da marigayi Janar Joe Garba yana ministan harkokin Ƙasashen waje. Kuma takardar da Furofesa Adedoja ya gabatar a taron Kuru na 1986 ya kawo a ka sanya harkokin wasanni a cikin tsare-tsaren harkokin Ƙasashen waje na Najeriya.

A shekarar 2001 aka zaɓi Furofesa Adedoja a matsayin mataimakin shugaba na ɗaya na Ƙungiyar wasannin maƘasassu na Ƙasa, kuma mamba a kwamitin zartarwa na hukumar wasanni ta naƘasassu ta Afirka ta Yamma (African Sport Confederation for the Disabled -ASCOD), kuma shugaban Ƙungiyar wasanni ta naƘasassu ta duniya shiyyar Afirka ta Yamma daga shekarar 2001 zuwa 2005.

A shekarar 2004, Furofesa Adedoja ya jagoranci naƘasassun Najeriya zuwa ziyara samun horo na kwanaki 30 a Ƙasar Kyuba a shirye-shiryen halartar wasannin motsa jiki na Afirka.

Furofesa Adedoja mamba ne a kwamitin bincike na Najeriya da ya gudanar da nazari kan wasannin motsa jiki a wasan motsa jiki na Ƙasashen Afirka da aka gudanar a Harare ta Ƙasar Zimbabuwe 1995. Sannan wakili ne a hukumar gudanarwar cibiyar nazarin harkokin wasanni ta Ƙasa (NIS) da ke Legas daga shekarar 2001 zuwa 2003, sannan wakili a Ƙungiyar masana kimiyyar wasanni ta duniya, (International Society of Sports Psychology-ISSP).

Ya taɓa riƘe muƘamin mataimakin shugaban Ƙungiyar masana kimiyyar wasanni ta Najeriya, (Sports Psychology Association of Nigeria -SPAN), kuma wakili ne a Ƙungiyar kimiyyar wasanni da kiwon lafiya ta Najeriya (Fellow of the Nigerian Association of Sports Science and Medicine-FNASSM), kuma mamba a kwalejin ilimi ta Nijeriya.

Daga 1989 zuwa 1992, Furofesa Adedoja ya riƘe muƘamin babban sakataren Ƙungiyar wasanni motsa jiki da kula da lafiya da walwala (Nigerian Association for Physical, Health and Recreation-NAPHER)lokacin da marigayi Furofesa AbdulFatai Folawiyo yake shugabancinta na Ƙasa.

Shi cikakken wakili ne kuma abokin haɗakar kafawa kuma babban sakataren farko na Ƙungiyar kula da lafiya, wasannin motsa jiki da wuraren walwalar jama’a da harkokin wasanni ta Afirka mai hedikwata a Gaborone ta Ƙasar Botwana tsakanin 1972 zuwa 1975. Sannan lokacin da Janar Samuel Ogbemudia yake Gwamnan Jahar Bendel ta da, kuma ƘoƘarin inganta wasanni daga karkara ya zamo abin da ya sa a gaba, Furofesa  Adedoja ya koyar da Ƙwallon kwando na lokaci-lokaci, kuma ɗan wasan Ƙungiyar Ƙwallon kwando ta Jihar Bendel daga 1973 zuwa 1975.

Furofesa Adedoja ya shiga an dama da shi a matsayin jami’i a wasannin motsa jiki na jami’o’in Najeriya (NUGA) da suka gudana a Ibadan da Fatakwal da Kalaba da Benin da kuma Ilori, kuma jami’i na wasannin motsa jiki na Ƙasa da suka gudana a sassan Ƙasar nan.

Bisa waɗannan ɗimbin nasarori da gogewa da Ƙwarewa a fagen ilimi da gudanar da harkokin wasanni a iya cewa, Furofesa Touheed Adedoja ne Ƙwararren mai gudanar da harkokin wasanni na farko da ya zama ministan wasanni na Najeriya. Ba za a ɗauki naɗa shi a ministan wasanni a matsayin naɗi na siyasa ba, sai dai naɗi na Ƙwarewa bisa burin sake dabarun kawo juyi da sake fasalin harkokin wasanni a Najeriya.

Lokacin da yake ministan wasanni  ya taka rawar gani, inda aka sami sauye-saute da dama a harkokin wasanni a zamaninsa. Muna yi masa fatar alheri da gama mai alheri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here