An Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Kan Farfaɗo Da Jiragen Ƙasa — Alhaji Maikuɗi Tela

0
8022

BALARABE JUNAIDU NUHU, Daga Kaduna

BABBAN jami’i mai kula da ofishin yaƘin neman zaɓen shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan/Namadi Sambo a 2011, na shiyyar Arewa maso Yamma, Alhaji Muhammadu Maikuɗi Tela, ya yaba wa ƘoƘarin gwamnatin tarayya na farfaɗo da zirga-zirgar jiragen Ƙasa wanda tuni ya fara aiki ka’in da na’in, musamman daga Legas zuwa Kano inda talakawan Ƙasa ke cike da murna.

Alhaji Maikuɗi Tela ya bayyana wannan yabo ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna, a farkon wannan makon.

Haka ya yaba da aikin gina tashar jirgin Ƙasa ta Rigasa, da gina titin jirgin Ƙasa wanda ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja wanda za a yi amfani da jirgin Ƙasa mai sauri irin na zamani, wanda ofishin mataimakin shugaban Ƙasa, Alhaji Muhammadu Namadi Sambo ke kula da zirga-zirgar jiragen Ƙasa ɗin.

Ya ce a bisa ga ƘoƘarin mataimakin shugaban Ƙasar, aƘalla matasa sama da 10,000 ne za su sami aikin yi inda ya ce abin a yaba wa gwamnatin tarayya ne.

Haka ya ce gwamnatin tarayya ta sami nasarori wajen inganta samar da wutar lantarki inda ya ce kamar yadda shugaban Ƙasa ya sanar a saƘonsa na sabuwar shekara ta 2013 cewa, a yanzu sun samar da miga-watt 4,500 inda ya ce abin a yaba ne.

Haka an duƘufa ka’in da na’in wajen gyaran hanyoyin Ƙasar nan inda akasarin hanyoyin da suka lalace an ci Ƙarfinsu.

Alhaji Maikuɗi Tela ya Ƙara da cewa, sha’anin rashin tsaro kuwa, ya ce gwamnati tana samun gagarumin nasara a kai sosai, inda ya ce wannan nasara da ake samu akwai addu’o’i na al’ummar Ƙasa da suke yi a kullum da kuma ƘoƘarin rundunar tsaro ta Ƙasa, inda ya buƘaci al’ummar Ƙasar da kada su gajiya da yin addu’o’in.

Ya ce abubuwan da suka faru a shekarar 2012 kada Allah ya maimaita su, inda ya yi addu’a, shekarar 2013 ta zamo abin farin ciki ga ‘yan Najeriya.

Sannan sai ya buƘaci ‘yan Najeriya da su rungumi aƘidar zaman lafiya su manta da bambance-bambancen da ke tsakaninsu don a sami ci gaba a Ƙasa.

Haka kuma ya buƘaci al’ummar Jahar Kaduna da su mara wa Gwamna Mukhtar Ramalan Yero da mataimakinsa, Ambasada Nuhu Nyam Audu Bajoga baya tare da addu’ar Allah Ya ba su ikon yin adalci ga kowa da kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here