Obasanjo Ya Ruɗe Kuma Ga Saurin Tunzura — Jonathan

0
8290

SHUGABAN Ƙasa,
Dokta Goodluck Jonathan, ya ragargaji tsohon shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo. Ya kira shi ruɗaɗɗen mutum game da ra’ayoyinsa waɗanda suka shafi yadda gwamnati take tafiyar da yaƘin sunƘurun ‘yan Boko Haram da ya Ƙi ci ya Ƙi cinyewa kuma ga saurin tunzura.

Dokta Goodluck Jonathan ya faɗi haka ta bakin mai taimaka masa a kan kafafen yaɗa labarai da yayatawa, Dokta Reuben Abati. Shugaban yana mayar da martani ne a kan kalamin da Obasanjo ya yi a tashar talabijin ta CNN a yayin hira da shi.

Obasanjo ya ce Shugaba Goodluck yana amfani da Ƙarfi ainun a yayin yaƘar ‘yan Boko Haram kuma ba ya bin hanyar tattaunawa a wajen magance matsalarsu.

An bayar da rahoton Obasanjo yana cewa, ya kamata in Jonathan ya ciza, to, ya hura.

Dokta Reuben Abati ya nuna rashin amincewa tare da yin suka game da kalamin Obasanjo a shafin yanar gizo ta Twitter. Ya kira Obasanjo ruɗaɗɗen mutum wanda gwamnati ba ta damu da shawara ko ra’ayinsa ba.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa ɗin ya ce tsohon shugaban Ƙasa Obasanjo a watan Nuwamban 2011 a garin Warri ya zargi gwamnatin tarayya da yin sassaucin a kan ‘ya’yan Boko Haram. Ya bayar da shawarar a ɗauki mataki shigen na Odi wato kisan kiyashi.

Abati ya ce a Janairun 2013 sai Obasanjo ya kawo shawarar gwamnati ta ɗauki matakin in ta ciza, to, ta hura a kan ‘ya’yan Ƙungiyar Boko Haram. Ya ce a ina ne Obasanjo ya tsaya.

Ya ce matsayin Obasanjo a kan Boko Haram shi ne saɓani da ruɗu. Ya Ƙara da cewa, wani rahoto ya ambaci Obasanjo yana cewa, a bi matakai wajen shawo kan ‘ya’yan Boko Haram. Kuma gwamnati ba ta buƘatar lacca a kan wannan, inji Abati.

Dokta Abati ya ce gwamnatin Jonathan ta nuna basira da yin abin da ya kamata a wajen tunkarar Ƙalubalen Boko Haram. Ya ce wannan ne ma ya kawo ci gaban da ake gani ana samu a yanzu.

Mista Obasanjo ya fara fusata Mista Jonathan ne ta cewa, ga alamu, shugaban Ƙasa yana da rauni a yadda yake tafiyar da Ƙalubalen tsaron da Ƙasa ke fuskanta.

A cikin sharhinsa, Obasanjo ya tunatar da jama’ar Ƙasa yadda ya umarci jami’an tsaro da su mamaye garin Odi a cikin Jahar Ribas don zaƘulo tsagerun da suka kashe jami’an tsaro a yayin mulkinsa.

Shi kuma Mista Jonathan a tattaunawa da wakilan kafafen yaɗa labarai ta Ƙarshe. Ya ce cika bakin da Obasanjo ke yi na an farmaki Odi bai magance matsala ba sai ma aka Ƙare da kashe waɗanda ba su ji kuma ba su gani ba.

Masu biyayya ga Jonathan da Obasanjo a cikin jam’iyyar PDP sun yi ta jefa wa juna kalamai tun daga lokacin. Kuma shugabannin jam’iyyar na Ƙasa suna kai gwauro suna kai mari a ƘoƘarin sasanta su biyun.

Obasanjo ya faɗa wa tawagar sulhu da Bamanga Tukur ya jagoranta a lokacin da suka ziyarce shi a gonarsa ta Ota a ranar 15 ga Disamban bara cewa, zai ci gaba da yin sharhi a kan batutuwa na Ƙasa idan yin haka ya wajaba ba tare da la’akari da ya sosa wa wani rai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here