Rabo Haladu Daga kaduna
Danmajalisar dattawa mai wakiltar mazabar shiyya ta daya a jihar kaduna sanata Sule Usman Hunkuyi,ya baiwa dalibai mata goma gurbin karo karatun aikin likita a jami\’ar musulunci da ke kasar Yuganda.
Sanata Hunkuyi, ya bayyana cewa zai ci gaba da baiwa dalibai tallafin gurbin karo karatu domin samun isasun likitoci a jihar masamman likitoci mata.
Domin tunkarar hakan zai zama kalubale ga rashin isasun likitoci mata da jihar take fama dashi.\”zakaga cewa mace bata da lafiya a maimakon mace likita ta duba mara lafiyar sai kaga likita namiji ne zai tsaya a kan mara lafiyar sabo da rashin isassun likitoci mata\’.
Sanata ya kuma kai wadannan dalibai mata su 10 gidan gwamnatin Jahar Kaduna domin gwamna ya gansu ya kuma sa masu albarka.
A nasa jawabin malam Nasiru Elrufai, ya ce shima zai yi koyi da sanata hunkuyi zai bawa dalibai 30 gurbin karo karatu a kasashan waje.
Akarshe ya yi kira ga daliban da su mayar da hankali a kan abin da ya kaisu kasar Uganda.