Gobara: Miji Ya Tsallake Rijiya Da Baya sanadiyyar Tukunyar Matarsa

0
2314

Wani matashi mai suna Ibrahim da akewa lakabi da (Kuru) dan kimanin shekaru 30  da ke zaune a sabon garin Rigasa cikin garin Kaduna, ya tsallake rigiya da baya a yayin da tafasasshen  Man gyadan da matarsa za tayi girki dashi ya kusa halaka shi.

Lamarin ya faru  ne a gidansa da marece sa\’ilin da matarsa  ta dora man a wuta don yin girkin dare,  wanda ya yi sanadin konewarsa a yayin da ya yi kokarin dauke tukunyar man da ta kama da wuta don gujewa gobarar  iskar tukunyar gas  da suke girkin dashi a gidan.

A binciken da wakilinmu  Usman Nasidi, ya gudanar ya gano cewa ba wutar gobara bace ta kona shi illa kokarin sauke tukunyar abincin da matarsa ta dora a wuta ne inda man ya fallatsar masa a hannu kuma da yaji zafi sai ya saki tukunyar baki daya wanda tafasasshen man ya kwaru masa a jiki kuma da yayi kokarin tsallakewa sai ya zame ya fada kan ragowar man da wanda ya zube.

Dukda yake Kurun ya kasa bayyana komai da kansa, wata majiya daga cikin aminansa sun bayyana cewa kamin aukuwar lamarin, yana kwance ne a gidan inda matar shi ta nemi ya taimaka mata da duba tukunyar sakamakon nonon da take ba \’yarsu data dame ta kuka bayan ta dora girkin, amma yana zuwa sai ya tarar da har wuta ta kama a cikin tukunyar shi ne yayi kokarin kawar da tukunyar daga inda take.

Ta kara da cewa bayan zuwan shi wajen, yayi kokarin kashe wutar abin dafa abincin na tukunyar iskar gas din kamin yayi kokarin fitar da tukunyar abincin da ake soya man don gujewa tashin gobara babba dakan iya kona gidan baki daya, amma sai dai hakan bata yu ba wanda har ya kaiga konewarsa.

Amma a halin yanzu dai, Ibrahim Kurun yana nan kwance cikin mummunar yanayi yana jinyar kunar zafin man domin duk jikin nasa tun daga kirji har zuwa kafa ta gaba ya salube baki daya sakamakon man daya kwaru masa a jiki da wanda ya fada akai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here