RABO HALADU DAGA KADUNA.
AN shawarci kananan manoma da ke fadin Jihar Kaduna, dasu mike wajen shiga
kungiyoyin manoma domin samun kusancin da ya dace daga wajen gwamnati.
Kwamishinan ma\’aikatar ayyukan gona ta Jihar Kaduna, Mista Manzo Daniel
Maigari ya bada wannan shawara a yayin wani taron manema labarai da ya
gudana a sakatariyar \’yan jaridu ta kasa da ke jihar.
Mista Maigari ya ci gaba da cewar shiga kungiyoyin manoma wata hanya ce mai
sauki wacce za ta sadar da manoma da gwamnati har a kai ga samun biyan
bukata.
Kwamishinan ya ci gaba da cewar, a duk shekara kananan manoma a jihar suna
samar da dimbim masara da sauran dangin amfanin gona, wanda ake neman saye
ruwa a jallo a ciki da wajen jihar, amma rashin kasancewarsu a kungiyance
yana mayar da hannun agogo baya.